Malam Tukur Buba Gombi

Malam Tukur Buba Gombi Wannan shafi ne dake kawo karatuttukan Sheikh Tukur Gombi.

23/07/2024
22/07/2024

Gara kaskancin Neman ilimi da kaskancin jahilci.
Daga cikin maganganun hikima na Asma'iyyu ya ce: duk wanda bai jure kaskancin Neman ilimi na awa daya ba. Zai yi fama da kaskancin jahilci na har abada.

15/07/2024

A kyautatawa iyalai ranar Ashura
Manzon Allah (s.a.w.) ya ce : duk wanda ya yalwatawa kansa da iyalansa a ranar Ashura Allah zai yalwata masa a sauran kwanakin shekarar.
Sahabbai sun jarraba hakan sun ga ya na yi sosai.
Jabir (r.a.) ya ce : mun jarraba hakan shekara arba'in Kuma mun ga ya na yi.
Ibnu uyaina ya ce: Muma mun jarraba tsawon shekara sittin Kuma mun ga alheri sosai.

14/07/2024
09/07/2024

A she wannan ma ya na daga cikin wawanci?
Wani mutum ya zo wajen Ibnu Abbas (r.a.)ya ce: ya saki matarsa saki uku.(kuma ya na son ta dawo) Mujahid ya ce: sai Ibnu Abbas ya yi shiru sai da na yi zaton zai mayar masa ita, sannan ya ce: mutum sai ya je ya tabka wawanci sannan ya zo ya na cewa ya Ibna Abbas ya Ibna Abbas. To Allah yace :
" duk Wanda ya ji tsoronsa zai sanya masa mafita"
to Kai ba ka ji tsoronsa ba, bai sanya maka mafita ba. Ka tafi matarka ta maka nisa.

08/07/2024

Hukuncin sana'ar bara:
Sana'ar bara haramun ce. Imam Ghazali ya ce: roko a asali haramun ne, Ana iya halatta shi ne kadai don lalura ga wanda ba shi da makawa. (Saboda) Annabi (s.a.w) ya ce: duk wanda ya ke roko domin ya tara, ya na rokawa kansa garwashin wuta ne in ya ga dama ya yi kadan ko ya yi mai yawa.
Muslim ne ya ruwaito shi.

05/07/2024

Ko ka yarda da wannan?
Ya zo a cikin maganganun hikima na larabawa cewa:
Larabawa su na cewa: masu kudi da su ke tsammanin talakawa su na cikin jin dadi, wawancinsu bai kai na talakawan da suke tsammanin masu kudi su na cikin jin dadi ba.

Address

Buba Basullube
Yola

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Malam Tukur Buba Gombi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Malam Tukur Buba Gombi:

Share