18/05/2022
Mashallah
Ina so in ja hankalin musulmai a duk inda suke, musamman wayanda suke Mu'amala da jama'a daban-daban a zahiri (school, ma'aikata, kasuwa) da kuma social media.
Ka kiyaye mutuncin aqidar ka da addinin ka, ba a ko ina zaka tura abubuwan musulunci ba, ko kayi magana akan aqidar ka.
Misali, a whatsapp, ba a kowani group za kayi magana akan addini ko aqida ba, sai in domin haka a ka bude group din, ko kuma kai da masu irin ra'ayi/fahimtar ka ne a cikin group din.
Magana ko bayyana aqidar ka a ko ina, ba shi bane cikar addini ko aqida, kiyaye martabar addini ko aqidar ka daga zagi ko munanan martani, shine kasancewar ka cikakken mabiyi addini/aqidar ka.
Wani lokaci sai kaga ana turawa wasu abubuwa ana cewa duk wanda ya turawa mutane 10 ko group goma zai ga alheri, wanda ya qi kuwa kaza da kaza zai same shi, inji wa?
Haka zalika lamarin Debora, wanda ya tura abin addini a group din nan, yayi kuskure domin group ne na dalibai wanda aka bude domin harkar karatun su, da bai tura ba, da bata halaka ba!
Ka kiyaye aikata abinda sanadiyar ka za a halaka!
Abu na biyu, ka kiyaye zama ko shiga inda ba a san mutuncin aqidar ka ko addinin ka ba, domin wani lokaci, ko ba kaine ka fara Bayyana aqidar ka ba, sai anyi maka habaici ko tsokana.
Ina sake jaddada nasiha ta ga yan'uwa masu son musu da jayayya, wannan ba hanyar shiryar da zuciya bane, kokarin kwatanta kyawawan mu'amalar magabata shine hanyar shiryar da zuciya.
Ku fita daga group din da ba aqidar ku daya ba.
Ku kawar da kanku daga hirar da ya sabawa fahimtar ku.
Kuyi unfriending wanda ke tsokanar ku ta hanyar zagin abin son ku ko yi muku comments na izgili.
Wannan zamani ne da babu wanda yasan darajar abinda kake so sai kai kanka, don haka kare martabar abin son ka yana hannun ka ne. ka boye shi, kar ka bayyana shi ga kowa sai mai irin ra'ayin ka.
Allah ka bamu lafiya da zaman lafiya, ka qasqantar da masu son qasqantar da addinin ka, alfarmar Annabi SAW.