22/08/2026
-Wata rana Imam Aliy (A.S) yana tafiya sai ya hadu da wani Bayahuden Khaibar s**aci gaba da tafiya tare,
bayan sunyi nisa a tafiyarsu sai s**a iso wata hanya da ruwa ya cika wajen babu yadda za'ayi su tsallake ruwan,
daga ganin haka sai bayahuden nan ya fito da wani zare ko yadi ya nannade jikin sa dashi yabita
kan ruwan nan ya k**a tafiya, bayan ya danyi nisa sai ya juyo ya cewa Imam Aliy (A.S), inhar kasan abinda nayi to kaima ka biyo takan ruwannan,
Sai Imam yace kadan jirani, Sannan yayi Ishara ga ruwan nan da hannunsa masu albarka take ruwan ya dare ya koma dutse, Imam yabi takai ya wuce, da Bayahuden nan yaga haka sai ya tsuguna gaban Imam yace dashi:
"Yakai wannan saurayi me ka karanta da har yasa ruwa ya koma Dutse?"
Sai Imam yace masa: "Kai me kayi kabi takan ruwa?"
Sai Bayahuden yace: "Ana da'autullaha bi Ismihil a'azam"
Sai Imam yace:
" Menene Ismullahil a'azam?"
Sai Bayahuden ya ce: "Sunan Khalifan Manzo Muhammad (AS)"
Sai Imam yace masa: ai nine Khalifan Manzo (AS) Take Bayahuden yace:
" ASH HADU AN LA'ILAHA ILLALLAH WA ASH HADU ANNA MUHAMMADAR RASULULLAH"
-Ya Ali.
voice of shi'a