Zawiyan Arufu Wukari LGA

Zawiyan Arufu Wukari LGA This page was created to spread knowledge and educate our brothers who are followers of Sheikh Tijja

25/08/2026

🌙✨ EID MAULUD NABYY ﷺ ✨🌙

Eid Maulud Nabiyy Sallallahu Alayhi Wasallam ﷺ to all our amazing and valued customers. ❤️

Today, we celebrate the blessed birth and noble life of our beloved Prophet Muhammad ﷺ.

May Allah SWT fill our hearts with his love, guide us to follow his Sunnah, forgive our shortcomings, increase our Imaan, and bless us with peace, prosperity and endless Barakah. 🤲❤️

May Allah bless you, your families, and your businesses, and grant us all success in this world and everlasting happiness in the Hereafter.

Eid Maulud Mubarak! 🌙🕌✨

Zawiyar ARUFU

24/08/2026

A wace zawiya zaka raya wannan daren mai Albarka daren haihuwar Annabi S A W

TA’AZIYYA! TA’AZIYYA!! TA’AZIYYA!!!Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.Cikin matuƙar jimami da raunin zuciya, mu...
23/08/2026

TA’AZIYYA! TA’AZIYYA!! TA’AZIYYA!!!

Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Cikin matuƙar jimami da raunin zuciya, muna miƙa saƙon ta’aziyyarmu ga ɗaukacin al’ummar garin Arufu baki ɗaya bisa wannan babban rashi da ya same mu a daren jiya, Asabar, na rasuwar Malam Musa Bala, wanda aka fi sani da Oga Musa.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙansa da rahamarsa, Ya gafarta masa dukkan kurakuransa da zunubansa, Ya sa Aljannatul Firdausi ce makomarsa.

Haka kuma, muna roƙon Allah Ya ba iyalansa, ’ya’yansa, ’yan uwansa, abokansa da ɗaukacin al’ummar Arufu haƙurin jure wannan babban rashi. Allah Ya mayar da shi mafi alheri, Ya kuma kare mu daga sake fuskantar irin wannan babban rashi.

Allah Ya jiƙan marigayin, Ya gafarta masa, Ya sa Aljanna ce makomarsa. Ameen Ya Rabbal Alameen.

MUBARAQ IBRAHIM AHMAD

11/08/2026


Gobe Larabar Karshen Watan Safar

Ga Abinda Za'a karanta

( Masu Dabi'ar Ma'i Surdanu Aqrabu Hutu Ku Karanta
WALLAHU YA'ASIMUKA MINANNAS Kafa Dubu 1 Sai Akaranta Ayatul Kursiyyu Kafa 66 Insha Allahu Zaku Samu Dafa'i Da Káriya Daga Dukkan Sharr! )

( Masu Dabi'ar Nari Himlu Asadu Qausu Ku Karanta TABBAT YADA Zuwa Karshe 313 Saiku Karanta Ayatul Kursiyyu 66 Insha Allahu Zaku Samu Kariya Daga Dukkan Sharr! )

( Masu Dabi'ar Hawa'i Jauza'u Miyzanu Dalwu Ku Karanta Li'ilafi Kafa 111 Ayatul kusiyyu 66 Insha Allahu Zaku Samu Kariya Daga Dukkan Sharr! )

( Masu Dabi'ar Turabi Sauru Sunbula jadyu Ku Karanta Alamtara Kaifa Kafa 100 Sai Ayatul kusiyyu 66 Insha Allahu Zaku Samu Kariya Daga Dukkan Sharr! )
_____
Wannan Anaso Ne Daga Daren Yau Har Zuwa Wayewar Garin Gobe In allah Yakaimu Har Wunin Yakare Kasamu Kayi Wannan Koda Ba'a Lokaci Daya Bane
_______
Wanda Baisan Dabi'arsa Ba Ya Karanta Hasbunallahu Wani'imal Wakilu Kafa Dubu Daya
Allah Ubangiji Ya'amsa mana
WALLAHU A'ALAMU

25/07/2026

CONDOLENCE MESSAGE

From the Arufu Community

The entire Arufu Community extends its deepest and most heartfelt condolences to Barr. Muhammad Danji, Esq. and his entire family on the painful loss of your beloved son.

We are deeply saddened by this heartbreaking news and share in your grief during this difficult time. We pray that Almighty Allah (SWT) forgives the shortcomings of the deceased, grants him Al-Jannatul Firdaus, and gives you, your family, and all loved ones the strength, patience, and fortitude to bear this irreplaceable loss.

May Allah comfort your hearts, reward your patience abundantly, and protect your family from every form of sorrow.

"Indeed, to Allah we belong, and indeed, to Him we shall return." (Qur'an 2:156)

Inna Lillahi wa Inna Ilayhi Raji'un.

Signed:
Arufu Community

🌙 AL'UMAR GARIN ARUFU 🌙Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.Al'Umar Garin Arufu na taya daukacin 'Yan Tijjaniy...
17/07/2026

🌙 AL'UMAR GARIN ARUFU 🌙

Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi wa Barakatuhu.

Al'Umar Garin Arufu na taya daukacin 'Yan Tijjaniyya a faɗin duniya murnar shigowar watan Safar, watan da aka haifi Maulanmu, Sheikh Ahmad Tijjani (R.A.).

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanya wannan wata ya kasance wata na alheri, rahama, albarka da ƙaruwa cikin soyayyar Manzon Allah (ﷺ) da kuma bin tafarkin magabata na gari.

Allah Ya ba mu albarkacin Maulanmu Sheikh Ahmad Tijjani (R.A.), Ya ƙarfafa mana imani, Ya karɓi ibadunmu, Ya haɗa kan al'ummar Musulmi. Āmīn Yā Rabbal-'Ālamīn.

Barka da Shigowar Watan Safar!

MURIDI YA KAMATA YA KASANCE YANA DA SHAYKHI ƊAYA KAWAIƊaya daga cikin manyan sharuɗɗan Tafarkin Tijaniyya shi ne girmama...
08/07/2026

MURIDI YA KAMATA YA KASANCE YANA DA SHAYKHI ƊAYA KAWAI

Ɗaya daga cikin manyan sharuɗɗan Tafarkin Tijaniyya shi ne girmama dukkan Awliyai ba tare da ware kowa ba, yin imani da falalarsu, da kuma gaskata karamominsu. Wannan shi ne akidar Ahlus-Sunnah.

Hana da Shaykhi yake yi wa Muridi zuwa wurin wasu Awliyai ba yana nufin raina su ko nuna ƙyama gare su ba. A'a, manufarsa ita ce kiyaye maslahar Muridi wanda yake cikin tarbiyyar ruhi, kamar yadda Allah Ya tsara masa.

Masu ilimin ma'arifa (ʿArifūn) sun yi ittifaki cewa Muridi mai neman tarbiyya (Murīd al-Tarbiyyah) ya kamata ya kasance yana da Shaykhi guda ɗaya kawai. Muridi ba zai samu cikakkiyar fa'idar tarbiyya ba idan yana ta kai-komo tsakanin Shaykhi biyu, saboda bambancin siffofin ruhaniya, hasken ilahi, da ƙarfi na musamman da Allah Ya bai wa kowanne daga cikinsu.

Irin wannan canzawa tsakanin Shaykhi biyu na iya jawo ruɗani a zuciya da tunanin Muridi, har ya kasa samun cikakkiyar ikhlasi da sadaukarwa ga ɗayansu. Wannan kuwa yana hana shi samun asirai da hasken ruhaniya yadda ya kamata. Saboda haka, kasancewa tare da Shaykhi guda ɗaya shi ne mafi alheri kuma mafi dacewa ga Muridi.

Amma ziyartar Awliyai da niyyar neman kusanci ga Allah, ko ziyartar kaburburansu domin yin tunani, tuna Allah, da yi musu addu'a, abu ne da malamai s**a yi ittifaki a kan halaccinsa. Wannan aiki ya tabbata daga Sunnah ta Annabi ﷺ, kuma babu wanda yake da ikon hana shi. Tafarkin Tijaniyya ba ya hana wannan, kuma ba ya ƙyamar sa. A hakikanin gaskiya, babu wani sharadi a cikin Tijaniyya da ya saɓa wa Al-Qur'ani ko Sunnah ta Manzon Allah ﷺ.

Shaykh (Allah Ya yarda da shi) ya ce:

"Idan kun ji wani abu daga gare ni, ku auna shi da ma'aunin Shari'a. Duk abin da ya yi daidai da ita ku karɓa, duk abin da ya saɓa mata kuwa ku bar shi."

Wannan ƙa'ida da Shaykhin ya kafa tana daga cikin tubalan Tafarkin Tijaniyya kuma tana da matuƙar muhimmanci. Saboda haka, duk wata magana ko da'awa da ta saɓa da wannan ƙa'ida, wajibi ne a yi watsi da ita.

TA'AZIYYAMuna miƙa saƙon ta'aziyyarmu ga iyalan gidan Alhaji Musa Usman Kakat-Tumbi bisa rasuwar ɗansu, Engineer Yusuf (...
24/06/2026

TA'AZIYYA

Muna miƙa saƙon ta'aziyyarmu ga iyalan gidan Alhaji Musa Usman Kakat-Tumbi bisa rasuwar ɗansu, Engineer Yusuf (Nyako) Usman.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya jiƙansa da rahama, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Allah Ya ba iyalansa da dukkan waɗanda rasuwarsa ta shafa haƙurin jure wannan babban rashi.

Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un.

Daga: Al'ummar Musulmai na Arufu.

SAƘON TAYA MURNAAl'ummar Musulmai na Garin Arufu suna miƙa saƙon taya murna ga ɗan'uwanmu, MM DANJI ESQ, bisa ga nasarar...
21/06/2026

SAƘON TAYA MURNA

Al'ummar Musulmai na Garin Arufu suna miƙa saƙon taya murna ga ɗan'uwanmu, MM DANJI ESQ, bisa ga nasarar da Allah Ya ba shi ta samun kujerar Mataimakin Shugaban Hukumar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), Reshen Jalingo (Vice Chairman, NBA Jalingo Branch).

Wannan nasara alama ce ta jajircewa, ƙwarewa, nagarta da kuma amincewar da abokan aiki s**a nuna gare ka.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba ka hikima, lafiya da ikon gudanar da wannan muƙami cikin adalci da nasara. Allah Ya sanya wannan shugabanci ya zama alkhairi ga reshen NBA na Jalingo da kuma al'umma baki ɗaya.

Muna yi maka fatan alkhairi da ƙarin nasarori a rayuwa.

Muna taya ka murna sosai!

Daga: Al'ummar Musulmai na Garin Arufu.Allah Ya ƙara ɗaukaka da albarka. Amin. 🤲🏾

Eid Mubarak 🌙✨ I extend my warmest wishes to you all on this blessed occasion of Sallah. May this sacred celebration bri...
21/03/2026

Eid Mubarak 🌙✨

I extend my warmest wishes to you all on this blessed occasion of Sallah. May this sacred celebration bring peace, joy, and abundant blessings to your homes and families.

May your prayers be accepted, your sacrifices rewarded, and your hearts filled with gratitude and love. Let us continue to uphold unity, compassion, and kindness in our community.

Mallam IBRAHIM.K. AHMAD (Chief IMAN ARUFU)

Address

Arufu Wukari LGA
Ukari

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zawiyan Arufu Wukari LGA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share