Qafilatul Mahabbah Islamic Foundation Uba Branch

Qafilatul Mahabbah Islamic Foundation Uba Branch Kungiyar Musulunci mai Burin Hadin kai jin-ƙai, wa’azi da ci gaban Al'umman Garin Uba.

MaSha Allah Muma munanan Zuwa Insha Allah
20/04/2026

MaSha Allah Muma munanan Zuwa Insha Allah

*GODIYA*GODIYA**GODIYA*
Qafilatul mahabba reshen jihar yobe potiskum local government tana Mika sakon godiya ga daukacin malamai da daliban ilimi wadanda s**a bada gudumawarsu wajan ganin wannan DAURAR tayuwu

MUNA MUKU BARKA tareda bangajiya Allah yasaka muku da mafifichin Alkairy
Allah yakara hadamu cikin wata munasaba irin wannan

Mungode mungode mungode

GOBE MAI KYAU NA MATASAN GARIN UBA, JIHAR ADAMAWACikin ikon Allah da yardarsa, ya bai wa wasu matasa—waɗanda ba ma’aikat...
19/04/2026

GOBE MAI KYAU NA MATASAN GARIN UBA, JIHAR ADAMAWA

Cikin ikon Allah da yardarsa, ya bai wa wasu matasa—waɗanda ba ma’aikatan gwamnati ba ne, kuma ba manyan ‘yan kasuwa ba ne—sai dai ƙananan almajirai masu neman na kansu daga wajen Allah, damar taimakawa al’ummar Anguwan Dumde Central.

Sun yi babban aiki na gyaran borehole wanda ya lalace tsawon wata guda. A wannan lokaci, al’ummar unguwar sun sha wahala wajen samun ruwa, har suna zuwa daga Dumde zuwa wajen masallacin Juma’a domin samo ruwan ibada da na yau da kullum.

Waɗannan matasa sun nuna tarbiyya da sadaukarwa, inda s**a bayar da abin da suke da shi domin sauƙaƙa rayuwar al’umma. Duk da cewa su ma suna buƙatar kuɗin, sun fifita buƙatar jama’a a kan tasu, s**a aiwatar da wannan aiki na alkhairi.

Ba wannan kaɗai ba ne, kuma su malamai ne da ke karantar da yara a garin, suna ƙoƙarin gina matasa nagari masu tarbiyya.

Hakika, irin waɗannan matasa sun cancanci yabo, addu’a da jinjina daga al’umma. Irinsu ne muke fata Allah Ya ba su damar jagorantar al’umma domin su ci gaba da ayyukan alkhairi.

Suna da ƙungiya ta musamman mai kula da taimakon marayu, marasa ƙarfi, da mabukata gwargwadon iko, ƙarƙashin jagorancin Imam Aliyu Ndotti, wato Qafilatul Mahabbah Islamic Foundation.

Muna roƙon Allah Ya taimaka musu, Ya azurta su da dukiya mai albarka, Ya ƙara musu kishin gari da al’umma.
Ameen summa Ameen.

Sayyadina Abu Huraira yace: Ban taɓa ganin Abu me kyau kamar Annabi ﷺ ba, kamar rana ce take tafiya a fusakar sa ﷺ.Sayya...
13/01/2026

Sayyadina Abu Huraira yace: Ban taɓa ganin Abu me kyau kamar Annabi ﷺ ba, kamar rana ce take tafiya a fusakar sa ﷺ.

Sayyadina Ka'abu bun malik yace: Annabi ﷺ ya kasance in yayi farin ciki fusakar sa na haske, kai kace yankin wata ne.

Shehun mu Shehu Ibrahim Inyass RTA yace: "Annabi ﷺ Rana ne sai dai shi hasken sa ya game " a kwaishi a ko yaushe a kuma ko ina, saɓanin Rana da in Dare yayi babu haskenta.

   Batijjane Ɗan Faira Abdurrahaman Annahwy ya kammala PhD a Jami'ar Azhar da First class, ya kammala ya nada Shekara 25...
13/01/2026



Batijjane Ɗan Faira Abdurrahaman Annahwy ya kammala PhD a Jami'ar Azhar da First class, ya kammala ya nada Shekara 25, wanda shine mafi ƙanƙantar shekaru da ya kammala PhD A jami'ar.

Ministan Harkokin Addini na Misra Dr. Usama da manyan malaman jami'ar na cikin Mahalarta Munaƙashar, wanda hakan ya tuna min baitin Shehu:

ومرة أخرى ترون عجبا ** من فيض ذا الختم إمام النجبا

Wannan abun farin ciki ne ga dukkan yan faira musamman masu kishin ta, kuma wannan na nuna wa masu ƙoƙarin rushe Faidha se sun jira, Alhamdulillah!

Yau cikin yardar Allah, mun samu damar fara ziyarar da muka yi alkawarin za mu gabatar a lokacin da muka ƙaddamar da wan...
19/12/2025

Yau cikin yardar Allah, mun samu damar fara ziyarar da muka yi alkawarin za mu gabatar a lokacin da muka ƙaddamar da wannan ƙungiya.

A wannan ziyara, mun samu ziyartar Babban Malaminmu kuma Babban Limamin Garin Uba, Sheikh Abdullahi Imam, wanda ya ba mu shawarwari masu amfani tare da yi mana addu’o’i.

Allah ya saka masa da mafificin alkhairi, Ya kuma haɗa kan Musulmi a duk inda suke. Ameen.

Address

Opposite Modibbo Bello Zawiya Uba Adamawa
Uba

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Qafilatul Mahabbah Islamic Foundation Uba Branch posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share