23/01/2026
SAƘON TAYA MURNA DA GOYON BAYA
GA HAKIMIN TULAI, KARAMAR HUKUMAR TORO JIHAR BAUCHI
Ƙungiyar Ci gaban Matasan Tulai (Tulai Youth Community Development Forum), tare da haɗin gwiwar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa, na miƙa saƙon taya murna da fatan alheri ga Hakimin Gundumar Tulai, Galadiman Toro, Alhaji Jafar Idris Muhammad, bisa wannan nadin sarauta da aka yi masa.
Muna kallon wannan nadin a matsayin abin alfahari kuma na cancanta, tare da yin imanin cewa gogewa, hikima da jajircewarsa za su taimaka wajen ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai da bunƙasa cigaban al’ummar Tulai baki ɗaya.
A madadin matasa da ’yan kasuwa na Mazabar Tulai, muna jaddada cikakken goyon baya mara yankewa ga jagorancinsa, tare da tabbatar masa da shirye-shiryenmu na yin aiki kafaɗa da kafaɗa da masarautarsa domin cimma cigaba mai ɗorewa.
Muna kuma kira ga al’ummar Tulai da su mara wa sabon hakimin baya, su kasance masu zaman lafiya, bin doka da oda, domin tabbatar da nasarar wannan sabon jagoranci.
Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba shi lafiya, hikima da nasara wajen sauke nauyin da aka ɗora masa, tare da tabbatar da zaman lafiya da dorewar cigaba a Mazabar Tulai, Karamar Hukumar Toro da Jihar Bauchi gaba ɗaya.