Autan Zakirai

Autan Zakirai Tunatarwar Addini da Ilimantarwa

02/06/2026
Wani rahoto da Pew Research Center ya fitar a shekarar 2025 ya nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta biyar a duniya cikin ƙasash...
02/06/2026

Wani rahoto da Pew Research Center ya fitar a shekarar 2025 ya nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta biyar a duniya cikin ƙasashen da ke da mafi yawan al’ummar Musulmi.

Kididdigar ta bayyana cewa Musulmi sun kai kusan kashi 54 cikin 100 na yawan al’ummar Najeriya, adadin da ya kai kimanin mutane miliyan 124.

Idan Ziyarar Annabi S A W ta wuya ta a gareni, to ganinsa acikin Zuciya ta bazai taɓa gogewaba.~ Sheikh Ibrahim Inyas
02/06/2026

Idan Ziyarar Annabi S A W ta wuya ta a gareni, to ganinsa acikin Zuciya ta bazai taɓa gogewaba.

~ Sheikh Ibrahim Inyas

Annabi Muhammad ﷺ yace ''kalmomi guda biyu ,masu sauki a harshe (wajen fada), masu nauyi a sikelin lada (ranar Alƙiyama)...
02/06/2026

Annabi Muhammad ﷺ yace ''kalmomi guda biyu ,masu sauki a harshe (wajen fada), masu nauyi a sikelin lada (ranar Alƙiyama)masoya a gurin Allah Mai Rahma sune: Subhanallah wa bihamdihi , Subhanallahil azeem.

Sahih al-Bukhari 6682.

Allah ya bamu ikon karanta su ameen.

Duk mai zaton cewa kasancewar mu mutanen kirki ne yasa muka zama Tijjanawa to ya sake tunani.Tijjaniyya ce ta mai damu m...
02/06/2026

Duk mai zaton cewa kasancewar mu mutanen kirki ne yasa muka zama Tijjanawa to ya sake tunani.
Tijjaniyya ce ta mai damu mutanen kirki bawai mune muka shigo da kirkin ba.

Duk abunda za a gani daga garemu na kirki to Kayanta ne, saɓanin haka kuma wannan Sharrin Nafsun mune kawai.

Barka Masoya Shehu

Nana A'isha (RA), ta ce “Manzon Allah ﷺ bai taɓa ɗaukar wa kansa fansa ba a kan wani abu, sai dai idan an keta alfarmar ...
02/06/2026

Nana A'isha (RA), ta ce “Manzon Allah ﷺ bai taɓa ɗaukar wa kansa fansa ba a kan wani abu, sai dai idan an keta alfarmar Allah, sai ya ɗauki mataki saboda Allah.”

Sahihul Bukhari da Sahih Muslim

Allah Ya sa mu koyi yafiya, haƙuri da kyawawan ɗabi'u daga rayuwar Annabi ﷺ

Manzon Allah s a w ya koremin duk wani asharari daga tafiyata, Sai yakoromin wasu kalar mazaje, masu tsoron Allah, shiry...
02/06/2026

Manzon Allah s a w ya koremin duk wani asharari daga tafiyata, Sai yakoromin wasu kalar mazaje, masu tsoron Allah, shiryayyu, masu Ilimi, rabautattu.

~ Sheikh Ibrahim Inyas

YANZU-YANZU: wasu da ake zargi da kasancewa ’yan daba sun farmaki babban shehin Ɗariqar Tijjaniyya, Sheikh Sharif Tijjan...
01/06/2026

YANZU-YANZU: wasu da ake zargi da kasancewa ’yan daba sun farmaki babban shehin Ɗariqar Tijjaniyya, Sheikh Sharif Tijjani Faira na unguwar Badawa, Nasarawa a Jihar Kano, tare da wasu daga cikin muridansa.

Lamarin ya faru ne a ranar 30/05/2026 da misalin ƙarfe 5:30 na yamma, a lokacin da shehin da mabiyansa suke gudanar da shirye-shiryen wani taro.

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun kai farmakin ne tare da yin barazana, inda aka ce sun sha alwashin sai sun ga ƙarshen rayuwar shehin.

Bayan faruwar lamarin, an kai rahoto ga jami’an tsaro a Badawa Division Police Station domin ɗaukar matakin da ya dace. Sai dai rahotanni sun nuna cewa har yanzu waɗanda ake zargi da hannu a cikin harin suna ci gaba da yawo a cikin unguwar tare da mak**ansu ba tare da an ɗauki wani kwakkwaran mataki a kansu ba.

Ko da yake jami’an tsaro sun bayyana cewa sun k**a mutum ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi, har yanzu sauran suna cikin unguwar suna zirga-zirga ba tare da wata matsala ba, lamarin da ya haifar da damuwa a tsakanin al’umma.

Masu ruwa da tsaki da mabiyan shehin sun yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta gudanar da cikakken bincike tare da kamo dukkan waɗanda ake zargi domin tabbatar da adalci da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Kuyi Mana Share Don Sakonmu Ya Kai Inda Ya Kamata

Litinin Ita Ta Zo Da Haske Da Shiriya Ga Talikai Lokacin Da Suke Cikin Tsananin Duhu Da Ɓata!Barka Da Zuwa Yā Rasūlal-Lā...
01/06/2026

Litinin Ita Ta Zo Da Haske Da Shiriya Ga Talikai Lokacin Da Suke Cikin Tsananin Duhu Da Ɓata!

Barka Da Zuwa Yā Rasūlal-Lāh ﷺ

Address

Rogo World
Takum
660001

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Autan Zakirai posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share