Qudsiyya Aliyya Sufiyya

Qudsiyya Aliyya Sufiyya Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Qudsiyya Aliyya Sufiyya, Religious organisation, Off dendo Road, Sokoto.

A ƙalla Ita ɗariƙa, kayi riƙo da ita, idan ka riƙa ta, zá ta wanke zuciyar ka, ta ɗebe maka nafsu.Kamar yadda halarori B...
04/10/2022

A ƙalla Ita ɗariƙa, kayi riƙo da ita, idan ka riƙa ta, zá ta wanke zuciyar ka, ta ɗebe maka nafsu.
Kamar yadda halarori Biyar ne, haka muƙamin ruhi shi ma biyar ne, Daga Sirru, sai ruhu, sai ƙalbu sai aƙalu sai nafsu. Kamar ace hahutu, lahutu, jabarutu, malakutu da Nasutu, Halarori na Allah kenan. Don haka ta hanyar k**a azkarai shi ɗai kasa kayi fana'i cikin halarar farko har zuwa halara ta biyar, halarar ƙarshe. Idan ka gama waɗannan halarorin, ka káma azkaran da ya k**ata kullum asirinsu zai riƙa buɗemaka, amma da sharaɗin halarar ƙarshe, Halarar zamanin ka, kayi fana'i a cikin ta, idan baka yi fana'i a cikin ta ba, to waɗancan basuda amfani gareka, idan kayi fana'i cikin ta sai ta jáwoma waɗancan halarorin, ta gwada maka sirrin su, ka ƙaru, sannan ka ci gaba da tafiya, tafiya a cikin Allah bata da iyaka, tafiyar kashi uku ce: zuwa ga Allah, idan kakai ga Allah, aikin ka zai zama kanayin abu ne saboda Allah, ba don kowa ba,
Sannan tafiya da Allah, idan muƙamin ka yaci gaba, sai kaga ayukkan ka, ba kai kaɗai kakeyin su ba, tare da Allah kake yinsu, Kamar abin noma ne, kai ke noma amma dashi kakeyin noman, to haka Allah ya ke gareka.

Sai tafiya a cikin Allah, mai irin wannan tagiai, bai ganin kai nai, bai ganin aiki nai, bai ganin motsinai, komi ya barma Allah, don haka bai kai keyin aiki ba, Allah ke yin aikin da kanshi, sannan Allah ya ce kai kayi, don ya bashi láda wadda bata da iyaka. Wannan ita ce tafiya babba, tafiyar waɗanda s**a ƙare tarbiyya, duk motsin su a cikin Allah ne, ibadar su ta awá guda tafi ibadar Wanda bai san Allah ba shekara saba'in.

Faɗakarwa daga Khalifan sirrin faila (Halara ta 5) Shehu Ibrahim Aliyu bunza Sokoto (Qaddasallahu sirrahu) ga jama'a:A c...
04/10/2022

Faɗakarwa daga Khalifan sirrin faila (Halara ta 5) Shehu Ibrahim Aliyu bunza Sokoto (Qaddasallahu sirrahu) ga jama'a:

A cikin wani majalisi Khalifa Yace yana so ya faɗakar da mutane koda akwai waɗanda basu fahimta ba ko basu sani ba, don su sani
"Wannan zamani da muke cikin wani ƙarni ne wanda yake tattare da manya manyan Alkhairai, musamman ga mutanen Allah, saboda Allah ko da yaushe bai taɓa barin mutanen shi ba haka nan basuda jagora, kuma bai basu manyan Alkhairai ba.
Jagoran wannan zamanin, wanda za ka riƙawa ka samu Allah , kasamu tsira duniya da lahira, Shine maulanmu Shehu Aliyu bn Muhammad bunza Qaddasallahu sirrahu. Wanda bai sanshi ana fatar yanzu ya sanshi, Wanda ya sanshi amma bai riƙashibi, to Allah ya bashi dáma ya riƙashi, saboda wanga zamani da muke, muna cikin zamaninshi, kowane zamani, akwai waliyyin da Allah ke báshi, wanda ko wane mutunen Allah, yana ƙarƙashin shi, shi za'a riƙa, shi za'a bi, asámu biyan buƙata. Wannan zamanin in har baka sanshi ba , to kasan cewa shine Shehu Aliyu QS, kuma ba komi yake buƙata gareka ba illa ya sádáka da Allah, ya nemar maka rahamar Allah.
Sonshi kawai ya isheka kasamu Tsira lahira, ballantana ka káma hanyar shi, wanda ya k**a hanyar shi, tabbas zai sádáshi da Allah.
Idan ba ɗan ɗariƙa bane kai zai sáka ɗariƙa, idan kai ɗan ɗariƙa ne zai sá ka tarbiyya ya sádáka da halarar maulanmu Shehu Ibrahim r.a, ta faila, kuma ya sádáka da halarar shi ta sirrin faila, halara ta biyar, halarar wannan zamanin.

Alhamdu Lillah..

Daga bakin Khalifan sirrin faila, Shehu Ibrahim Shehu Aliyu bunza Sokoto QS.Khalifa yana Yawan káwo wannan hadisin a cik...
02/10/2022

Daga bakin Khalifan sirrin faila, Shehu Ibrahim Shehu Aliyu bunza Sokoto QS.
Khalifa yana Yawan káwo wannan hadisin a cikin majalisosan shi, inda ya ke cewa, "Manzon Allah yace" mafi soyuwar ayukka ga Allah shine wanda za ka dawwama kana yi koda ɗan kaɗan ne"

Anan Khalifa yana magana ne akan sauqin ɗariƙar tijjaniya wadda yana daga cikin Manya manyan sharuɗɗan ta na idan an shiga, ba'a fita har iya ƙarshen rayuwa, za'a dawwama a cikin ta ana karatun lazumman ta na safe da yamma wanda duk ba zai wuce minti talatin (30) ba idan aka haɗa su , sai wazifah wadda ita kuma bazata wuce minti Arba'in da biyar ba (45), kaga kenan awa ɗaya da minti Arba'in da biyar ne (1:45) kacal zaka cire a cikin awowi 24 da ke cikin yini ka bá Allah, wanda ya kasance yana yin wannan ibadar ta ɗariƙar tijjaniya a kullum har iya ƙarshen rayuwa, haƙiƙa ya siffantu da wannan hadisin na Manzon Allah SAW, sannan ya kasance Ábidi mai aikin da yafi soyuwa wurin Allah bisa ga ko wane aiki.

Allah ya bamu ikon kasancewa a cikin Bayin sa masu aiki mafi soyuwa gareshi, haƙiƙa ɗariƙar tijjaniya hanya mai sauƙin sada mutum da Allah kuma wadda ake samun yardar Allah a cikin ta ba tare da an wahala ba.

Dalilin ƙirƙiro ɗariƙun waliyyai:Su dai ɗariƙun sufáye, babban maƙsudin su shine kusantar da bawa ga Allah, su gwada ma ...
02/10/2022

Dalilin ƙirƙiro ɗariƙun waliyyai:

Su dai ɗariƙun sufáye, babban maƙsudin su shine kusantar da bawa ga Allah, su gwada ma mutum Allah, su nuna mai tawakkali da dogaro ga Allah a cikin ko wane hali, su karkatar da zuciyar mutum daga ganin talitta a cikin al'amurra zuwa ga ganin Allah a cikin komai da komai, wannan shine babban maƙsudin ɗariƙun waliyyai, Kuma a haƙiƙanin al'amari shine aikin annabawa da manzanni.

Maulanmu Shehu Aliyu bunza QS ya yi bayani game da dalilin da yasa sufáye s**a ƙago ɗariƙu.
Shehu yace a lokacin Manzon Allah SAW, Sahabbansa basu buƙatar ɗariƙa don saduwa da Allah, saboda ganin fuskar Manzon Allah ya' isa yasa su gane Allah, hasken Zatin Manzon Allah ya isa yayi musu taraƙƙi zuwa ga Halarar Allah subhanahu wata'ala. Shi yasa basu buƙatar wata ɗariƙa domin saduwa da halarar Allah mai tsarki.
Manzon Allah, shine ɗariƙar su.

Bayan wafátin Annabi SAW, sai wannan daraja ta ganin jikinai ta gushe, hasken ya tafi, mutane suna ta nisantar Allah kaɗan-kaɗan, har aka kai bagiren da Sahabbai s**a ƙare , tabi'una da tabi'uttabi'una suma s**a ƙare , hasken ya gushe, sai bidi'o'i s**a fara bayyana, Shi'anci da khawarijance da mu'utazilanci da masu ilmin manɗiƙi a cikin addini, dukkanin su masu gurɓatattun aƙidodi s**a bayyano a cikin Musulunci.

Nan Allah ya bayyanar da waliyyai domin su maida bayin Allah a saman wannan tafarkin sunna na gaskiya, cikin fatahin Allah su ka zo da ɗariƙu, da azkaran tsarkake zuciya masu kusanta mutum da Allah, bisa tafarkin Manzon Allah.

Wannan shi ne sanadin naƙalto ɗariƙu na waliyyan Allah.

Waliyyan Allah, suke haƙiƙanin magáda sirrin Manzon Allah.

Aal-e-Imran 3:103وَٱعْتَصِمُوا۟ بِحَبْلِ ٱللَّهِ جَمِيعًا وَلَا تَفَرَّقُوا۟ۚKuma ku yi daidami da igiyar Allah gabã ɗay...
29/09/2022

Aal-e-Imran 3:103

وَٱعْتَصِمُوا۟ بِحَبْلِ ٱللَّهِ جَمِيعًا وَلَا تَفَرَّقُوا۟ۚ

Kuma ku yi daidami da igiyar Allah gabã ɗaya, kuma kada ku rarraba.

Haqiqa yin riqo da igiyar Allah a zamo tsintsiya maɗaurinki ɗaya bai wuce kasancewa a cikin waɗannan asrarai guda 5 ba :

A hadu a cikin Allah (Subhanahu wata'ala)
A haɗu cikin Manzon Allah. (S a w)
A haɗu a cikin Shehu Ahmad tijjani. (R.a)
A haɗu a cikin Shehu Ibrahim inyass. (R.a)
A haɗu a cikin Shehu Aliyu bunza Sokoto. (QS)

Wannan na Ishara da haɗuwa a cikin halarori biyar (5)

An haɗu a cikin uluhiya
An haɗu a cikin Muhammadiyya
An haɗu a cikin Ahmadiyya
An haɗu a cikin Ubudiyya
An haɗu a cikin Qudsiyya Aliyya

Tabbas babu wata igiya da takai wannan ƙwari, kuma babu wata Reza ko yuƙa ko mak**ancin haka da keda kaifin da zai iya yanke wannan Hablu Ta Allah, idan mun haɗa kanmu k**ar yadda waɗannan igiyoyin s**a haɗa mu (Mu Ahlul sirril Faila) to fa babu Abinda zai iya raba mu kuma babu abinda zai iya yi muna barazana a faɗin dunyar nan domin Allahu shine ƙarfin mu , Muhammadu ne abin koyon mu, Ahmad da Abdu da Aliyu sune abun tawassulin mu, jagororin mu, Kuma sune hasken mu a cikin duhun nan da ake kira DUNIYA.

Allah ya ƙara muna son juna da tausayin juna da kuma taimakon juna, don Alfarmar mai sirrin nan na ahadiyya.

Shehu na cewa "shi ɗan Halara a duk inda yake to yasani ba shi kaɗai yake ba , yana tare da halarar da duk abinda ta ƙunsa baki ɗayanta saboda sirrin ta na Ahadiyya da ihaɗar ta a kowane bagire cikin ko wane lokaci"

Ashe kenan komi yawan mu, abu ɗaya muke ko mi rarrabuwarmu a záhiri to a baɗini wuri ɗaya muke, abinda duk ya sáméka, ya sámèni, abinda da duk ya sàmeni kai ma ya sáméka, abin Alhairi ko akasin haka.

إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلَّذِينَ يُقَٰتِلُونَ فِى سَبِيلِهِۦ صَفًّا كَأَنَّهُم بُنْيَٰنٌ مَّرْصُوصٌ

lalle Allah Yanã son waɗanda ke yin yãƙi dõmin ɗaukaka KalmarSa, a cikin safu k**ar sũ gini ne mai ɗamfarar jũna.

Bayanin Akan Zawiyya.Maganganu a cikin wani majalisi na khalifan Shehu Aliyu bunza Sokoto, Shehu Ibrahim Aliyu bunza Sok...
29/09/2022

Bayanin Akan Zawiyya.

Maganganu a cikin wani majalisi na khalifan Shehu Aliyu bunza Sokoto, Shehu Ibrahim Aliyu bunza Sokoto QS:

A cikin wani majalisi na khalifan sirrin faila, Shehu Ibrahim Shehu Aliyu bunza QS, ya yi taqaitacen bayani akan sirrin Zawiyyoyi na waliyyai, ya bayyana bambanci tsakanin Ordinary Masallaci da zawiyya, idan mutum ya yi salloli biyar 5 a cikin zawiyya, tamkar yayi salloli Ashirin da biyar ne 25 ne, dalili kuma shine, dalili shine, ma'anar zawiyya shine "ɓangare", kowace zawiyya tana da ɓangaren huɗu, ɓangaren gabas da yamma, kudu da Arewa, haɗi da mihrabi sun zama biyar, idan ka yi sallah ɗaya a ciki za'a linka ta sau biyar 5, saboda sirrin ɓangaroran nan 5 kowane ɓangare na ɗaukar sirrin sallah ɗaya, kaga sun zama salloli ishirin da biyar acikin kowace sallah, a taqaice, sallah ɗaya a cikin zawiyya na ɗauke da sirrin sallolin yini ɗaya, yin salawatul khams a cikin zawiyya na dai-dai da yin salloli ɗari da Ashirin da biyar (125).

Yaƙara da cewa kafin zawiyya ta samun wannan sirrin sai in ta kasance zawiyya mai izinin wanda ya kai har zuwa ga Maulanmu Shehu Ahmad tijjani r.a.

Khalifa ya ce, k**ar yadda komi na Musulunci ke ɗauke da matakai uku, haka shi ma sirrin Zawiyyoyi, yace Zawiyyoyi sun kasu kashi uku, akwai:
Zawiyyar Ɗariqa (Tijjaniya)
Zawiyyar Faila
Zawiyyarsirrin faila.

Kuma k**ar yadda Tajallin ƙarshe ke ɗauke sirrin tajallin da ya gaba ce shi ya haɗa da nashi sirrin, haka yin Sallah a cikin zawiyar sirrin faila ya ɗauke sirrin sallah a cikin Zawiyyoyin tijjaniya da na Faila, ma'ana idan kayi salla a cikin zawiyar sirrin faila to kasamu ladar yin Sallah ga waɗancan Zawiyyoyin sannan kana da wani sirri na daban da waɗancan can básudashi. (Zálika fadlullah yutihi man yasha).

A kullum muna cewa babu abinda zamu yi ma Allah sai Godiya da zaɓenmu da yayi ya sámu a cikin wannan farar tafiya mai tare da ɗinbin asrarai wanda hankali bai ɗauka sai dai zuciya tayi imani kurum. Kuma Mun yi imani, mun gaskata duk abinda waliyyai s**a faɗa mana.

Alhamdu Lillah.

Al-Ahzab 33:23مِّنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ رِجَالٌ صَدَقُوا۟ مَا عَٰهَدُوا۟ ٱللَّهَ عَلَيْهِۖ فَمِنْهُم مَّن قَضَىٰ نَحْبَهُۥ وَ...
26/09/2022

Al-Ahzab 33:23

مِّنَ ٱلْمُؤْمِنِينَ رِجَالٌ صَدَقُوا۟ مَا عَٰهَدُوا۟ ٱللَّهَ عَلَيْهِۖ فَمِنْهُم مَّن قَضَىٰ نَحْبَهُۥ وَمِنْهُم مَّن يَنتَظِرُۖ وَمَا بَدَّلُوا۟ تَبْدِيلًا

Daga mũminai akwai waɗansu mazãje da s**a gaskata abin da s**a yi wa Allah alkwari a kansa, sa'an nan a cikinsu, akwai wanda ya biya bukãtarsa, kuma daga cikinsu akwai wanda ke jira. Kuma ba su musanya ba, musanyawa.

1026                                    ﷽Tajallin wireless technology na zamani wanda shine kusan ace ya kewaye ko'ina a...
25/09/2022

1026

Tajallin wireless technology na zamani wanda shine kusan ace ya kewaye ko'ina a duniyar kimiyya ta zamani an assasashi ne akan sirrin wani WAVE (haske na baɗinin zahiri) da ake kira "Radio Waves"

Haske (Light) na zahiri ya kasu kashi bakwai 7, ishara da Tajallin sirrin fatiha, (wannan Hasken wanda muke gani dashi a zahiri (visible light) Wani bangare ne daga cikin waɗannan haskaken guda bakwai 7), Ana yi musu suna da "Electromagnetism".

Ana kiran Zatin da ke ɗauke da waɗannan haskaken "Electromagnetic spectrum" an jera sune ɗaya zuwa bakwai 1-7 da qadarar saurin kowane haske daga cikinsu (wave length) da kuma hasken zarrorin da kowane haske (wave) yake ɗauke da shi (photon energy).
(photon na nufin zarrar dake ɗauke da hasken zahiri, k**ar neuron na cikin qwaqwalwa).

Wannan hasken da muke gani dashi (visible light) shine na huɗu 4 a jerin haskaken bakwai 7. Sauran haskaken (Waves) ɗin idanuwanmu basu ganinsu.
Ga yadda jerin su yake bisa ga tsarin gwargwadon hasken da suke ɗauke da shi:

1) Infrared rays, (2) X rays, (3) Radiowaves, (4) Microwaves, (5) Gamma rays, (6) UV rays.

Wannan Radio Waves ɗin mai ɗauke da sirrin wireless technology (kimiya da ke sádarwa ba tare da wasiɗa wadda ake gani ba) shine na farko 3 a cikin jerin.
Yana ɗauke da sirrin qudsiyya, domin qudsiyya wireless ce (baɗini), kuma saboda Radio Waves na nufin haske wanda ke RADIATING (ma'ana yake bazuwa ya game ko'ina a cikin ƙanƙanin lokaci), shiyasa zaka iya sadar da saƙonka kilomita Dubbai a cikin daqiqa saboda sirrin "speed of light", wannan sifa ta qudsiyya ce, haskenta shi ke game ko'ina a cikin qanqanin lokaci.

Longitudinal waves shine hasken záti (zahiran), Domin shi ke motsi (vibration) sama da ƙasa (up and down) shi ke ɗauke da hasken lantarki (electricity).

Abun lura anan shine, Tajallin wireless technology wanda da shine muke saduwa da juna baɗinan a cikin Halara ta hanyar social media da sauransu, sirrin hasken qudsiyya ne shiyasa wannan tajallin bai yi zuhuri ba sai da Mai qudsiyyar ya bayyana (QS).

Wannan darasi ne mai faɗin gaske, an taƙaita shi ne.

Alhamdu Lillah.

Ayoyin Allah na halarar qudsiyya a cikin jikin ɗan Adam:A cikin jikin ɗan Adam matashi wanda ya qosa akwai ƙassa (bones)...
24/09/2022

Ayoyin Allah na halarar qudsiyya a cikin jikin ɗan Adam:

A cikin jikin ɗan Adam matashi wanda ya qosa akwai ƙassa (bones) 206. Sunfi hakan yawa da yana ƙarami, wasu qassa s**an game da wasu (merging) a lokacin da yake girma.

Su ƙassa na ɗan adam k**ar sune zatinsa, domin su s**a ba jikin shi sifa (Structure) shiyasa sunan qashi da larabci yake (Azmu), wannan kalmar ita ce tushen kalmar (Azeem) wadda ke ishara da tajallin zàti.
Kenan ƙassa mutum na ɗauke da sirrin zatinsa zahiran.

Wannan lambar 206 baɗinnta (Digital root) 8 ne, saboda 2+0+6= 8. 8 symbol (Ishara) ce ta qudsiyya, ishara da ke nuna baɗinin zatin mutum (ƙassansa) ƙudsiyya ce.

Idan aka buga hisabil jumali na kalmomin ilmullah (علم الله) zai bada 206. Adadin qassan jikin ɗan adam. Wannan yana nuna yadda waɗannan ƙassan ke ba jiki siffarsa zahiran, haka Ilimin Allah ne yabayyanar da zatin mutum baɗinan , Abun lura a nan shine, zatin mutum na tare da isminsa, da af'alu da sifatu ɗinsa. Don haka dukkanin awalimu ɗinsa.

Ilmullahi anan yana ishara da halarar qudsiyya domin ita tayi tajalli da Dukkanin ulùmu Acikin baɗini, kuma baɗinin shine ya bayyanar da ilmoman zàhiri. Shi yasa acikin Alqur'ani Allah SWT yake cewa : فَٱعْلَمُوٓا۟ أَنَّمَآ أُنزِلَ بِعِلْمِ ٱللَّهِ "ku sani an saukar da shi (Qurani) da ilmin Allah" Ma'ana ai da zatinsa har ma qudsyyarsa domin su ke qunshe da ilimin na Allah zahiran wa baɗinan.

Kuma hisabin kalmomin ilmullahi 206 ne a zahiri, 8 (qudsiyya) a baɗini, sannan kuma kalmomin biyu ne 2, ishara da qudsiyya.

Ataqaice wannan yana qara nuna muna cewa halarar qudsiyya ita ce sirrin ɗan Adam domin ita ce sirrin zátinsa zahiran wa báɗinan.

Isharar ihaɗa ta Ilmullahi (qudsiyya), ba a cikin jikin ɗan Adam kawai ya tsaya ba, sammai da ƙassai gaba ɗaya, shi ya bayyanar da su (it gives structure to the universe) kuma shi ke riqe da su k**ar yadda ƙassan mutum ke riqe da jikinsa. Domin Harafi bakwai ne (علم الله) , 7 kuma sirrin zuhuri ne.

Ilmu, qudsiyya ne, domin hisabin shi 130 ne, 130 Kuma 4 ce saboda 1+3+0 = 4, k**ar yadda maulanmu shehu Aliyu ya bayyana huɗu tana zuhuri da qudsiyya, Allahu ko shine zatin.
Kaga Ilmullahi zati ne da qudsiyya, domin tare suke basu rabuwa, k**ar yadda Hasken electricity da magnetism suke (ga waɗanda s**a san ilmin kimiya) basu rabuwa shi yasa ake cewa "electromagnetism).

Allah ya qara fahimtar da mu sirrin tajallin sa a cikin sammai da ƙassai da kuma kawunanmu sannan da isharorin da suke ɗauke da shi.
Albarkacin mai sirrin zamunna.

Alhamdu Lillah...

Address

Off Dendo Road
Sokoto

Telephone

+2349160334775

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Qudsiyya Aliyya Sufiyya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Qudsiyya Aliyya Sufiyya:

Share