First aid group of jibwis saminaka detachment

First aid group of jibwis saminaka detachment Domin sanarwa fadakarwa ilmantarwa

09/04/2025

Mashaallah

Ana Qara sanarma alumman garin saminaka cewa tunda anwayi gari yau anaruwan Sama za ayi sallane amasllacin Kampa damisal...
16/06/2024

Ana Qara sanarma alumman garin saminaka cewa tunda anwayi gari yau anaruwan Sama za ayi sallane amasllacin Kampa damisalin 9:30 akulada lokaci

Suhaib Abdullahi saminaka lere East divisional Commandant kaduna State
23/01/2024

Suhaib Abdullahi saminaka lere East divisional Commandant kaduna State

28/07/2023

Mashaallah ayau juma'a dasafennan wani bawan Allah yabada masara asiyar 400 akofan masallacin kampa saminaka

AIKIN AGAJI A YAU Lalle Duniya da Al'umma sun tabbatar wannan Aiki na Agaji Yana da matukar mahimmanci a rayuwar Al'umma...
27/07/2023

AIKIN AGAJI A YAU

Lalle Duniya da Al'umma sun tabbatar wannan Aiki na Agaji Yana da matukar mahimmanci a rayuwar Al'umma.

'yan Agaji na bada Gudummuwa ta bangaren bada Taimakon Farko ga maras lafiya ko Wanda yaji rauni, Karaya, Shan guba, saran maciji, konar wuta, suma (Daukewar numfashi), zubar jini, farfadiya da sauran su.

Bayan Nan 'yan Agajin wannan kungiya na bada Gudummuwar su a wuraren tarurruka da kungiyar Jibwis take shiryawa ta hanyar bada kulawa wajen shirya wajen taron, yadda taron zai kasance, tsaftace wajen taron, bada tsaro da Kuma kare Dukiyoyin Al'ummar da sukazo wajen taron.

'yan Agaji na kula da yadda wajen wa'azin kungiyar zai kasance wajen bada kulawa da dukkan Abubuwan da muka zayyana a sama sannan da bada sauti domin jiyar da malarta, haske, wajen zama da kula da masu Saida kayayyaki a wajen da ganin cewa lalle ba'a zalunci Al'umma ba.

'yan Agaji na kula da wuren sallar Idi, Juma'ah, masallatan yau da kullin, wuraren sallar Tuhajjud, makarantun kungiyar Jibwis da sauran wuraren gudanar da Ayyukan Addinin muslunci.

'yan Agaji basu tsaya anan ba sune harda bada Gudummuwa wajen tafiyar Alhazai kasa Mai tsarki domin ganin mahajjata Basu samu wata matsala ba.

'yan Agajin na zuwa makabartu domin bada kula da Gyara dukkan wani kabari da ya samu matsalar ruftawa ko Ambaliyar ruwa ko Kuma tono daga Dabbobi.

Allahu Akhbar, 'yan Agaji na bada kulawa a Asibitoci yayin lokacin yajin Aikin ma'aikatan kiwon lafiya domin kula da wadanda suke kwance a Asibitocin.

'Yan Agaji masu Albarka mutane ne masu Girmama juna, karamci, zumunci, hakuri, tunani Mai kyau, juriya da Ikhlasi.

Ya Allah ga bayinka masu Albarka 'yan Agaji masu bada Gudummuwa wajen cigaban Addinin muslunci, Allah Ka sa Albarka a rayuwar su, Allah Ka sa su gama da Duniya lafiya, Allah Ka Albarkaci iyalan su, Allah Ka tsare musu mutuncin su.

Naku:
Suhaib Abdullahi Saminaka
First Aid Group Of Jibwis Nigeria

Allhu akhbar Allah yaima Dan autan agaji rasuwa Jana izarsa karfe 8:00 nasafen yau talata Allah yaimasa rahama yasa maic...
18/07/2023

Allhu akhbar Allah yaima Dan autan agaji rasuwa Jana izarsa karfe 8:00 nasafen yau talata Allah yaimasa rahama yasa maiceton iyauensane

Innalillahi wa inna ilaihirrajiun Allah yayima Dan autan agajin saminaka rasuwa adaren yau za ayi Jana izarsa gobe talat...
17/07/2023

Innalillahi wa inna ilaihirrajiun Allah yayima Dan autan agajin saminaka rasuwa adaren yau za ayi Jana izarsa gobe talata dasafe Allah muke roqa yaimasa rahama

Alhamdulillah majalissan agajin saminaka kenan awajan kaddamarda Dora mukamai gawanda suraina daka matsayin unit zuwa de...
06/12/2022

Alhamdulillah majalissan agajin saminaka kenan awajan kaddamarda Dora mukamai gawanda suraina daka matsayin unit zuwa detachment a anguwan tudun fulani. Kudu detachment muna yimuku addu'a na alkhairi Allah ya baku ikon jagoran alummanku yakareku da karewansa

KARATUNMU NAYAUAkwai abubuwa guda uku Wanda aikin bada taimakon farko ya dogara akansu, wasu masana ilimin bada taimakon...
29/07/2022

KARATUNMU NAYAU

Akwai abubuwa guda uku Wanda aikin bada taimakon farko ya dogara akansu, wasu masana ilimin bada taimakon farko suna kirabsu Ginshikan bada taimakon farko, da sauransu (1) BANDEJI (2) JINI (3) KASHI. Zamu fara da bandeji, duk wani dauredaure ko rufe rauni ko maratayi ana amfanine bandaeji, wasu lokuta ana amfanida bandeji Mai kusurwa uku wani lokaci Kuma badamai kusurwa uku akeyiba anayine da wani kalan daban, abin nufi anan SUNANSU BANDEJI.
Sai Jini shikuma yanada alaka da kowani sasanni najiki, kumako ina yananan don gudanar da aikinsa,.
Wadannan sune ginshikan bada taimakon farko da muke dasu.
Da Kashi dalilin kawoshi lura da irin amfaninshi da Kuma mahimmanci wurin gudanarda harkokinmu na yau da kullum.

Suhaib Abdullahi Saminaka

22/07/2022

INSHA ALLAH KAMAR YADDA MUKA SANAR MUKU CEWA ZAMU FARA KARATUTTUKA WADANDA SUKEDA ALAQADA AIKIN AGAJI TOCIKIN YARDAN ALLAH ZAMU DUNGA KAWO MUKU ADUK RANAN JUMA'A
DAGA BISANI AKWAI TANBAYOYI DAZUSU DINGA BIYO BAYA WANDA ZA ADUNGA BAMA DUKWANDA YAFI BADA AMSAN DAYAI DAIDAI KYAUTAN KATI CIKIN YARDAN ALLAH KUCIGABA DABIBIYANMU MUNA GODIYA DABIN WANNAN SHAFIN MAISUNA (First aid group of jibwis Saminaka)

DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJINQAIMunagodema Allah akan ni'imominsa dayaimana marasa misaltuwa abin farinciki shine daya...
15/07/2022

DASUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAIJINQAI

Munagodema Allah akan ni'imominsa dayaimana marasa misaltuwa abin farinciki shine dayayomu musulmai tabbas saidai muce alhamdulillah.
Awannan dandali Mai albarka zamu dunga kawo muku karatuttuka wadanda sukeda alaqada aikin agaji cikin yardan Allah nankusa bada dadewaba insha Allah mungode

SALLAR IDIN LAYYA J.I.B.W.I.S SAMINAKA1443/2022.ANA SANAR DA AL'UMMANMU ZA'A GUDANAR DA SALLAR IDIN WANNAN SHEKARAR 1443...
09/07/2022

SALLAR IDIN LAYYA J.I.B.W.I.S SAMINAKA
1443/2022.

ANA SANAR DA AL'UMMANMU ZA'A GUDANAR DA SALLAR IDIN WANNAN SHEKARAR 1443AH/2022M KAMAR HAKA:

RANA- ASABAR (10/12/1443- 09/7/22) A HARABAR MAKARANTAR (GOVERNMENT COLLEGE SAMINAKA)

LOKACI- 09:00AM

NB: IN AN TASHI DA RUWA ZA'A GUDANAR DA SALLAR A MASALLACIN JUMA'AH NA KAMPA SAMINAKA IN-SHA ALLAHU.

FATUN LAYYA: ANA NEMAN SADAKAR FATUN LAYYA, AKWAI YAN AGAJI A MASALLATAI DON KARBAN FATUN IN-SHA ALLAHU

MUNA FATAN ALLAH YA NUNA MANA LOKACIN YA KARBA IBADUNMU AMIN.

SHUGABAN KUNGIYAR AGAJIN SAMINAKA JIBWIS SAMINAKA DETACHMENT (AMINU MUHAMMAD ABUBAKAR)
MAI SANARWA.

Address

Ahmadu Bello Way Saminaka
Saminaka

Telephone

+2347064106526

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when First aid group of jibwis saminaka detachment posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to First aid group of jibwis saminaka detachment:

Share