11/01/2020
*AHIBBA'UL UMMAH!!!* *AHIBBA'UL UMMAH!!!*
*AHIBBA'UL UMMAH!!!*
AHIBBA'UL UMMAH ASSOCIATION,
MOTTO: ISLAMIC CHARITY & DEVELOPMENT ORGANIZATION,*
N.D.C U/KAJI TUDUN WADAN RIGACHIKUN KADUNA.
AIKI GA MAI KARE KA
ZIYARAN KUNGIYAR AHIBBA'UL UMMAH KARO NA FARKO .
A ranar goma ga watan janairun shekara ta dubu biyu da ashirin ne kungiyar AHIBBA'UL UMMAH karkashin jagorancin shugabanta MAL. Ahmad Muhammad. s**a kaddamar da ziyara ta musamman zuwa ga malamai da shuwagabannin unguwa.
A karon farko kungiyar ta samu ziyartar mutane biyu, inda aka gabatar musu da kungiyar tare da kudurorin ta da aikace aikacen ta kasantuwar kungiyar ta samu lokaci mai tsawo tana gudanar da aikace aikacen ta, hakan yaja hankalin shugabanta ya kaddamar da ziyara ta musamman zuwa ga malamai da shugabannin unguwar domin a kara musu sani game da kungiyar, dukka a matakin ci gaba.
*Mutun na farko da kungiyar takai ma ziyara shine, Malan. Abdullahi Ibrahim limamin babban masallacin juma'a na Abubukar siddiq,
*Mutun na biyu kuwa shine Sarkin U/kaji Alhaji Sade Mamman zango
Alhamdulillah , masu iya magana s**ace, " Abinda babba ya hango, yaro ko ya hau tsauni ba ze hango ba " Shawarwari masu fa'idah, lallai kwalliya ta biya kudin sabulu, Allah y ya kaimu ziyara karo na biyu.
*Yahaya Isah*
*Ahibba'ul Ummah*
*Social media*
*11/01/2020**