Tsoratarda Musulmi Daga Jinkirta Salla

Tsoratarda Musulmi Daga Jinkirta Salla TAHZIRIL MUSLIMINA MIN TA'KHIRISSALATI AN WAKTIHA WATAHRIMI TARKIHA, WATO TSOTARDA MUSULMI DAGA JINKIRTA SALLAH DAGA BARIN LOKACINTA DA KUMA HARAMTA BARINTA

One Day… It Will Be Just You and Your Deeds.No family. No friends. No wealth. No status. You will stand alone before All...
22/04/2026

One Day… It Will Be Just You and Your Deeds.

No family. No friends. No wealth. No status. You will stand alone before Allah and only your deeds will speak for you.

Allah says in the Qur’an:

“And every one of them will come to Him on the Day of Resurrection alone.”
(Surah Maryam 19:95)

And He ﷻ reminds us:

“That Day, people will depart separated [into categories] to be shown [the result of] their deeds. So whoever does an atom’s weight of good will see it, and whoever does an atom’s weight of evil will see it.”
(Surah Az-Zalzalah 99:6–8)

The Prophet ﷺ said:

“Three follow the deceased: his family, his wealth, and his deeds. Two return and one remains. His family and wealth return, but his deeds remain.”
(Sahih al-Bukhari 6514, Sahih Muslim 2960)

🤍 So prepare for that moment.
Fill your life with sincerity, repentance, and good deeds because your grave will only be illuminated by what you sent ahead.

Dua:
O Allah, forgive our sins, accept our deeds, and grant us light, ease, and mercy in our graves. Ameen.





ALLAHU AKBAR.ALLAH subhanahu wata'ala ya karbi rayuwar Sheikh Usman Kusfah Rigi-Rigi Muna rokon Allah ya jikansa da raha...
02/02/2026

ALLAHU AKBAR.

ALLAH subhanahu wata'ala ya karbi rayuwar Sheikh Usman Kusfah Rigi-Rigi

Muna rokon Allah ya jikansa da rahama ya gafartamasa.

Allah ya jikan musulami da s**a rigamu gidan gaskiya yayi mana afuwar gamawa da duniya lafiya Ameen.🤲🏾

*KANATSU KA KARANTA AKWAI DARASI ACIKI*((04)) Wata rana Manzon Allah (saww) ya shigo Masallacinsa sai ya tarar da wasu M...
08/08/2025

*KANATSU KA KARANTA AKWAI DARASI ACIKI*

((04))

Wata rana Manzon Allah (saww) ya shigo Masallacinsa sai ya tarar da wasu Mutane suna ta zance suna dariya.

Sai yace musu: "Amma da ace kuna tunowa da Mai yanke jin dadi (Mutuwa) da wannan ya shagaltar daku daga wannan abinda nake gani.

Ku yawaita Ambaton mutuwa domin wallahi babu wata rana da zata wuce fache sai QABARI (yayi ma kansa kirari) yana cewa:

"NINE GIDAN BAQUNTAKA! NINE GIDAN KADAITAKA!! NINE GIDAN TURBAYA!! KUMA NINE GIDAN TSUTSOTSI!!"

Idan aka zo binne Mumini acikin Qabarinsa, sai Qabarin yace masa:

"MARHABAN WA AHLAN.. WALLAHI KA KASANCE DAGA CIKIN MAFI SOYUWAR MUTANE AGARENI ACIKIN MASU TAFIYA ADORON QASA..

YANZU IDAN AN BINNEKA ACIKINA, NINE SUTURARKA NI ZAN AIKATA MAKA SAKAMAKON IRIN ABINDA KA KASANCE KANA AIKATAWA NE".

Nan take za'a fadada masa Qabarinsa har iyakar ganinsa, Kuma za'a bude masa Qofa zuwa gidansa na Aljannah.

Amma idan akazo za'a binne Kafiri ko Fajiri (Mai aikata manyan laifuka) Sai Qabarinsa yace masa:

"BA'A MARABA DAKAI, KUMA BA'A MURNA DA ZUWANKA.

KUMA WALLAHI KANA DAGA CIKIN MUTANEN DA NAFI QINSU DAGA MASU TAFIYA ADORIN QASA.

YAU ZA'A BINNEKA ACIKINA, NINE SUTURARKA, KUMA ZAN AIKATA MAKA SAKAMAKON IRIN AYYUKAN DAKA KASANCE KANA AIKATAWA".

Nan take sai Qabarin ya matseshi, har sai Qasusuwan hakarkarinsa sun shige cikin junansu.

(Sai Manzon Allah ya sanya yatsunsa cikin junansu -abisa misali).

Sannan za'a turo masa wasu Manyan MACIZAI GUDA SABA'IN (MASU MIYAGUN KAMANNI).

DA ACE 'DAYAN CIKINSU ZAI HURA QASAR DUNIYAR NAN DA BAKINSA, DA HAR ABADA DUNIYAR NAN BA ZATA TA'BA TSIRO DA CIYAWA BA.

ZASU YI TA SARANSA, SUNA CIZONSA HAR ZUWA LOKACIN DA ZA'A TAFI FILIN HISABI."

- Imam Tirmizy ne ya fitar da Hadisin. sannan Ibnul Jawzy ma ya kawoshi acikin babi na biyu acikin littafinsa mai suna AHWALUL QUBOUR.

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!!

YA ALLAH KA KYAUTATA QARSHEN MU KA BA MU CIKAWA DA IMANI.

Sadiqu Sani Gandi Na Annabi Muhammadu✍️

🌴 FALALAR TUBA DA ISTIGFARI🌴📜 Manzon Allah ﷺ yace "Yaku mutane ku tuba zuwa ga Allah, domin lallai ni ina tuba a wuni sa...
05/08/2025

🌴 FALALAR TUBA DA ISTIGFARI🌴

📜 Manzon Allah ﷺ yace "Yaku mutane ku tuba zuwa ga Allah, domin lallai ni ina tuba a wuni sau ɗari".
📚 صحيح مسلم ٢٧٠٢

📜 Manzon Allah ﷺ yace "Madalla ga wanda aka samu Istigfari mai yawa acikin takardarsa".
📚 صحيح ابن ماجه ٣٠٩٣

📜 Manzon Allah ﷺ yace "Babu wani mutum da zai aikata wani zunubi, sannan ya tashi yayi tsarki (Alwala), sannan yayi sallah raka'a biyu, ya nemi gafarar Allah, face Allah ya gafarta masa".
📚 حديث حسن ، رواه الترمذي ٤٠٦

▪️Malamai s**a ce
"Idan mutum ya nemi gafarar Allah ya tuba gareshi, tuba ingantatta, kuma ya ciratu zuwa ga zunubi, Allah zai karɓi tubansa, kuma zai gafarta masa. Idan ya sake komawa zuwa ga zunubi sannan ya nemi gafarar Allah kuma ya tuba, tuba ingantatta kuma ya ciratu zuwa ga zunubi, Allah zai karɓi tubansa, kuma ya gafarta masa. Kamar haka, laifin zunubin da yawuce ba zai dawo ba, tare da tuba ingantatta. Allah maɗaukaki yace
(وَإِنِّي لَغَفَّارٌ لِّمَن تَابَ وَءَامَنَ وَعَمِلَ صَالِحًا ثُمَّ ٱهۡتَدَىٰ) طه ٨٢ ، وقال : (إِنَّ رَبَّكَ وَاسِعُ ٱلۡمَغۡفِرَةِ) النجم"
📓 فتاوى اللجنة الدائمة ٣١٩/٢٤

▪️Ibnul Qayyum رحمه الله yace
"Abubuwa huɗu suna jawo arziƙi: (i) Tsayuwar dare (ii) Yawaita istigfari lokacin safiya (iii) Yawaita sadaka (iv) Ambaton Allah a farkon yini da ƙarshensa".
📘زاد المعاد ٣٧٨/٤

▪️Ibn Kathir رحمه الله yace
"Duk wanda ya siffanta da siffar Istigfari Allah zai sauƙaƙa masa arziƙinsa, zai sauwaƙa masa al'amarinsa, zai kiyaye sha'aninsa da ƙarfinsa".
📙تفسير ابن كثير ٣٢٩/٤

▪️ Ibnul Qayyum رحمه الله yace
Wanda ya dauwama yana Tasbihi sirrikansa zasu warware (buƙatunsa zasu biya). Wanda ya dauwama yana Tahamidi (Godiya ga Allah) alkhairai zasu bibiyeshi. Wanda ya dauwama yana Istigfari za'a buɗe masa abubuwan da s**a kulle mashi".
📕الداء والدواء ١٨٨

▪️Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai

Yakai Ɗan-uwa mai Albarka ka yaɗa wannan saƙo, zaka samu lada. Domin lallai duk wanda yayi nuni kan aikin alkhairi kamar ya aikata ne

Allah Ka bamu ikon tuba ingataciya..🤲

RASHIN SALLAH A CIKIN JAM'IWata rana MANZON ALLAH (ﷺ) Suna tafiya tare da wani sahabinsa sai ga wani Raƙumi ya taho aguj...
27/07/2025

RASHIN SALLAH A CIKIN JAM'I
Wata rana MANZON ALLAH (ﷺ) Suna tafiya tare da wani sahabinsa sai ga wani Raƙumi ya taho aguje tare da wani mutumi yana binsa da wuƙa yana so ya cimmasa, Raƙumin nan yana zuwa gaban ANNABI (ﷺ) Sai ya tsaya yana haki yana cewa na tsira, can kuma sai ga wani mutum da zabgegiyar wuƙa ya iso wajen ANNABI (ﷺ) Shima yana ta haki, sai ANNABI (ﷺ) yace masa "Mai za ka yi da wannan sharɓeɓiyar Wuƙa?" sai yace "Wannan Raƙumin nawa ne shi zan yanka saboda bayayamun biyayya"

Sai MANZON ALLAH (ﷺ) ya tambayi Raƙumin cewa "Haka ne ba ka yi masa biyayya?" sai Raƙumi yace "Eh haka ne amma ba wai haka nan kawai ba, ina da dalili mai ƙarfi"
Raƙumi yace "Wannan mutumi Musulmi ne amma ba ya yin sallar isha'i a cikin jam'i, wata rana ma sai ya yi barcinsa ya falka sannan zai yi ta, ni kuma ina tsoron ka da azabar da za a yi masa ta shafe ni tunda a gidansa nike"

Sai ANNABI (ﷺ) yace wa mai Raƙumi "Haka ne?" sai yace "Eh haka ne" amma na daina daga yanzu, ka zama shaida akan haka
Sai Raƙumi yace tunda ka daina to nima na daina yi ma rashin biyayya, sai ANNABI (ﷺ) ya sasanta tsakaninsu s**a koma gida.

Yanzu waye ya san irin yanda muke wulaƙanta yin sallah a jam'i musamman lokacin da ake kallon ƙwallo? ALLAH ya shiryamu shirin Addinin Musulunci, ameen ya hayyu ya qayyum

Tsoratarda Musulmi Daga Jinkirta Salla

Manzon Allah tsira da amincin Allah su dawwama a gare shi yace,, '' Duk wanda ya haɗa salloli biyu batare da wani uzuri ...
25/07/2025

Manzon Allah tsira da amincin Allah su dawwama a gare shi yace,, '' Duk wanda ya haɗa salloli biyu batare da wani uzuri ƙwarara ba, to kuwa yajewa wata kofa daga kofofi manya na zunubi".

Kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su dawwama a gare shi yace "Duk wanda yabar sallah da gangan to Allah ya rubutu sunansa a kofar wuta daga jimlar wanda zaya shigeta" A wata faɗar kuwa akace wanda yabar sallah da gangan haƙiƙa aikinsa ya ɓaci".

Allah yasa mudace, ayi follow na wannan page mai albarka watoTsoratarda Musulmi Daga Jinkirta Salla

Kai CHONKA ya kai mai barin sallah. Kana raye a cikin duniya kana ta wahala kuma kana ta gajiya domin neman jin daɗin ra...
25/07/2025

Kai CHONKA ya kai mai barin sallah. Kana raye a cikin duniya kana ta wahala kuma kana ta gajiya domin neman jin daɗin rayuwa. Kuma kana kwaɗayin yardar mutum ɗan'uwanka. Allah maɗaukaki ya umurce ka da yin sallah, ya kuma sanya ta tsira a gareka daga wuta, amma kai sai ga ka kana wofintar da ita, kana yin kasalar yinta kuma kana wulaƙanta ta.

Manzon Allah tsira da amincin Allah su ƙara dawwama a gare shi yace, Duk wanda yabar sallar La'asr haƙiƙa dukkanin ayukkansa sun ɓaci" A cikin wata riyawar kuma aka ce "Duk wanda yabar sallar La'asr ta wuce shi kamar an kwashe masa iyalinsa da dukiyarsa ne baki ɗaya

Allah yasa mu gyara, kuyi follow na wannan page mai albarka wato Tsoratarda Musulmi Daga Jinkirta Salla

Aɗa'u ɗan yasar ya ce " shi ( wailun ) wani kwari ne a cikin jahannama, ita kanta jahannama tana neman tsarin Allah daga...
25/07/2025

Aɗa'u ɗan yasar ya ce " shi ( wailun ) wani kwari ne a cikin jahannama, ita kanta jahannama tana neman tsarin Allah daga bala'in zafin wailun, kuma shi ne mazaunin masu jinkirta sallah daga LOKACINTA

An tambayi Hassan al_busari game da ayar da Allah ke cewa bone ya tabbata ga masallatan da suke marabkana daga barin sallolinsu" sai yace Ana nufin wanda yake barin sai lokacin sallah ya shige sannan ya yi".wasu kuma daga cikin masu tafsir s**ace "wanda idan yayi sallar a cikin LOKACINTA bayayin farinciki, kuma in ya jinkirtata bayajin ɓaƙinciki, kuma baya ganin cewa gabatar da ita a cikin lokacinta shi ne alheri, kuma jinkirta ta babban laifi ne, don wannan yana daga mutuwar zuciya

Shi kuma wahab ɗan munabbahi yace yana mamakin yadda mutane ke yiwa wanda ya mutu kuka alhali kuwa mai makon suyiwa wanda zuciyarsa ta mutu kuka, domin kuwa mutuwar zuciya yafi rabuwa da duniya musifa

Ku tarbemu a gaba kaɗan, ku kuma yi follow na wannan page mai albarka wato Tsoratarda Musulmi Daga Jinkirta Salla

SHIN KA IYA SALLAH GAWA ?To bari in bayyana mataki-mataki yadda ake gudanar da Sallar Gawa (Salatul Janazah) a Musulunci...
25/07/2025

SHIN KA IYA SALLAH GAWA ?

To bari in bayyana mataki-mataki yadda ake gudanar da Sallar Gawa (Salatul Janazah) a Musulunci. Wannan salla tana da sauki amma tana bukatar fahimta da tsabta da niyya.



***YADDA AKE SALLAR GAWA (SALATUL JANAZAH)

✅ Sharuɗɗan Sallar Janaza:

1. Gawa ta zama Musulmi.

2. A wanke ta, a nade da likkafani.

3. A shimfiɗa gawa a gaban masu salla.

4. Jama’a su tsaya cikin layi (ba ruku’u, ba sujada).

5. A yi niyya.

**** Matakan Sallar Gawa:

1. Niyya (a zuciya):
“Zan yi sallar janaza ga wannan mamaci domin Allah.”
(Ba a furta niyya da baki).

2. Takbira na Farko:

Ka ce “Allahu Akbar”

Ka karanta Fatiha (Bismillah har zuwa Walad-daallin. Ameen ba dole ba)

3. Takbira na Biyu:

Ka ce “Allahu Akbar”

Ka karanta Salati ga Annabi (SAW):
“Allahumma salli ala Muhammadin wa ala aali Muhammadin...”

4. Takbira na Uku:

Ka ce “Allahu Akbar”

Ka yi addu’a ga mamaci, kamar:
“Allahummaghfir lahu warhamhu wa ‘aafihi wa’fu anhu...”
(In mamaci mace ne: laha maimakon lahu)

5. Takbira na Hudu:

Ka ce “Allahu Akbar”

Ka yi addu’ar karshe, kamar:
“Allahumma la tahrimna ajrahu wa la taftinna ba’dahu...”

6. Sallama:

Ka ce “Assalamu Alaikum wa Rahmatullah” (sau ɗaya, a dama kawai ko dama da hagu).

📝 Lura:

Ba a yin ruku’u ko sujada.

Ana yin sallar ne da tsaye idan mutum na da lafiya.

Za a iya yin sallar mutum ɗaya ko da jama’a ba su da yawa.

Kuyi F0ll0wing din Wannan shafin 👉 Tsoratarda Musulmi Daga Jinkirta Salla Domin Samun Fadakarwa Tunatarwa da sauran karatun Addini

Address

Gandi
Rabah

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tsoratarda Musulmi Daga Jinkirta Salla posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share