29/09/2025
LITININ, 29 GA SATUMBA
NASSI: ZAKARIYA 13:1-9
KAN MAGANA: SAKE MAIDOWA
Mun fara yin magana game da marmarin Allah na sake dawo da mutanensa cikin zumunci na gaskiya tare da shi saboda marmarinsa mai girma na ganin ya sadu da su.
Wannan zumuncin ya lalace a cikin Gonar Adnin sakamakon Faduwa (Farawa 3). Mutum ya cigaba da yin rayuwarsa cikin rashin biyayya da zunubi wanda ya raba shi da Allah.
Mutanen Yahuza su ma s**a sa kansu cikin irin wannan zunubin na rashin biyayya amma Allah ya sake maido da su ta wurin wani marmaro wanda ya tanada ta haka ya tsarkake su daga dukan zunubai da rashin tsarki.
Ya kuma yi magana ta bakin annabi cewar zai lalatar da dukan gumakan da s**a dauke hankalinsu daga gare shi ya kuma hukunta annabawan da s**a yaudare su. Wannan zai sa sauran rinjin su sake bunkas a cikin dangantakarsu tare da shi.
TAMBAYA:
Wadanne alloli ne da annabawan karya s**a raba ka da Allah?
ADDUA:
Ya Allah, ka bude idanun na in gane da mayaudaran annabawa ka kuma wadata ni da alherin ka yadda zan gujewa kowacce bautar gumaka da ke janyeni daga gare ka, cikin sunan Yesu. Amin.
ABINCIN YINI 2025