12/01/2026
FIRST AID GROUP OF JIBWIS NGURU YOBE STATE.
1ST SHEIKH SHERIFF TAHIR DETARCHMENT SEMINAR/CAMPING 2026/1446AH.
Alhamdulillah , dukkanin yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda cikin amincewar sa ya nuna mana farkon wannan seminar/ Camping har zuwa ƙarshen ta , anyi taro lafiya an gama cikin aminci.
A madadin Sheikh Sheriff Tahir Detarchment wanda s**a shirya wannan taro mai albarka ina miƙa saƙon godiya da kuma bangajiya ga dukkanin al'ummar da s**a jajircewa wajen ganin cewa an tafiyar da wannan taro cikin nasara tun daga Committee na shirye shirye har zuwa mahalarta wannan taro , haƙiƙa badon jajircewar ku ba da bamu cimma gaci ba.
Yabo na musamman zuwa ga dukkanin kungiyoyin da s**a bada lokacin su s**a karantar damu kamar Nigeria Police Force , NDLEA , Fire Service , Nurse , jinjina ta musamman ga malaman Addinin mu da s**a bada lokacin su kuma s**a nuna goyon bayan su ga wannan taro Allah ya saka musu da alkhairi.
Haka zalika yabo zuwa ga ƴan Uwa baƙin mu da s**a zo daga maƙotan garuruwa wanda s**a haɗa da Birniwa , Hadejia , Jajaimaji , Karasuwa , ba shakka munji daɗin amsa gayyatar mu da kukayi muna godiya bisa wannan karamci.
Daga karshe muna fatan wannan ya zama na farko amma ba na ƙarshe ba In sha Allahu ta'ala, Allah ya nuna mana na gaba da alkhairi.
Allah ya sakawa kowa da Alkhairi 🤲
Mun gode 🙏
Sheikh Sheriff Tahir Detarchment Leader,
Lawan Usman.