Al-Ikhlas TV

Al-Ikhlas TV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Al-Ikhlas TV, Minna.

✨ Al-Ikhlas TV 🌙
Sharing authentic Islamic knowledge in a simple and engaging way.
📖 Qur’an • Sunnah • Stories • Reminders
🎙️ Inspiring hearts, guiding youth, and spreading Da‘awah with sincerity.

23/01/2026
14/10/2025

“This life is a moment, spend it in obedience before it ends in silence.”

12/10/2025

Karatu fa na ta tafiya ba k**a hannun Dan Bidi'ah

Farouk Lawan, wanda ya wakilci mazaɓar Bagwai/Shanono a majalisar wakilai ya fadi haka ne a a wata sanarwa da ya fitar a...
12/10/2025

Farouk Lawan, wanda ya wakilci mazaɓar Bagwai/Shanono a majalisar wakilai ya fadi haka ne a a wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis bayan an sanar da sunan sa a cikin mutane 175 da shugaban ƙasa Bola Tinubu yafewa laifukan su.

Jaridar PI5NCH ta rawaito Lawan na cewa "wannan yafiya Allah ne Ya mun ta hannun Bola Tinubu. Ina mai godiya sosai da ka cire min damuwa da bakin ciki."

Gaskiya Ko Jita-Jita, Labarin Biliyan 50 Da Aka Ce An Sace A NAHCON Daga Ganiyu LamidiA Najeriya, jita-jita kan zama k**...
12/10/2025

Gaskiya Ko Jita-Jita, Labarin Biliyan 50 Da Aka Ce An Sace A NAHCON

Daga Ganiyu Lamidi

A Najeriya, jita-jita kan zama k**ar gaskiya idan aka yi ta maimaitawa. Labaran karya kan shafe na gaskiya, saboda mutane suna son jin labaran Al'ajabi, shakku ko mamaki. Mun taba jin labarin Madam Koi-Koi da Iliya dan Mai-Karfi, duk da ba gaskiya ba ne, amma mutane sun dade suna yada wannan labaran.

Yanzu haka, Hukumar Alhazan Najeriya, NAHCON, da Shugabanta Farfesa Abdullahi Saleh Usman, sun fada cikin irin wannan jita-jitar. Zargin wai an sace Naira biliyan 50 a hajjin da ya gabata. Labarin ya yadu Kamar wutar daji a kafafen sada zumunta da jaridu, amma babu wata hujja ko gaskiya cikin lamarin. Zargi ne kawai da 'Yan siyasa ke kara rura wutarsa.

Idan muka duba lamarin a hankali, za mu ga cewa wannan magana bata da tushe. A 2025, alhazai daga kudanci sun biya kusan Naira miliyan 8.78, yayin da na arewa s**a biya Naira miliyan 8.46. Idan aka raba Naira biliyan 50 da wannan farashi, zai bamu adadin alhazai kusan 5,700. Wato sai mutum ya karbi kudin alhazai fiye da dubu biyar da ba su tafi Hajji ba, ko kuma ya karkatar da kaso 12 na kudin dukkan alhazai s**a Biya a kasar sannan hakan za ta iya kasancewa.

Irin wannan satar ba abu ne mai sauki ba. Domin sai NAHCON da masu jiragen sama da masu masauki da masu abinci, da hukumomin jihohi su hada baki lokaci guda, kafin a iya cin wadannan kudade.

Sai kuma a ce irin wannan kudi sun bata amma majalisar wakilai da fadar shugaban kasa su yi shiru gaba daya. Wannan kusan ba zai taba yiwuwa ba.

A yau, babu wata Shaida da ta nuna an saci irin wannan kudi. Babu wanda ya fito da takarda ko shaidar batan kudin. Babu kasafin kudi wato (budget) da ya nuna wani gibi na wannan kudade Amma kawai sai labari keta yaduwa, domin mutane na son jin irin wadannan jita-jita.

Abin da nake gani a Najeriya ce kawai hakan ke faruwa. Idan sabon shugaba mai son ayi gyara ya hau, sai ya fara gyare gyare. Wadanda s**a saba da tsohon tsarin s**an ji haushi, su fara yada jita-jita don su bata sunan sabon shugaban. Sai a shaci labarin teburin Mai Shanyi a fitar da adadin kudi mai yawa k**ar “biliyan 50” don ta tada hankali da kawo CeCe-kuce a tsakanin jama'a

Gaskiya, Farfesa Abdullahi Saleh Usman yana kokarin tsaftace aikin Hajji. Ya rage almundahana, ya kara tsari. Wadannan canje-canje suna bawa wasu ciwon kai, musamman wadanda s**a saba cin moriyar tsohon tsarin.

Amma fa, wannan ba yana nufin kada ayi a bincike ba. Idan akwai laifi, a bincika a fito fili dashi. Mutane na da hakkin sanin gaskiya. Amma su ma Yan NAHCON suna da hakkin kada a zalunce su da jita-jita marar hujja.

Har yanxu Hukumar EFCC ma bata fitar da wata shaida ba. Babu rahoton da ya tabbatar da wannan zargi. Abin da ke yawo kawai shi ne maganar “an sace biliyan 50,”

NAHCON tana da lissafi. Ana iya duba adadin alhazai, kwangiloli, da kudade. Idan akwai rashin gaskiya, sai a gani a rubuce. Wannan shi ne ainihin hanyar bincike, ba hira a Facebook ko WhatsApp ba.

Madam Koi-Koi bata taba wanzuwa ba, amma har yanzu mutane na jin labarinta. Haka ma wannan labari na biliyan 50, ya yadu ne saboda mutane sun riga sun yarda cewa gwamnati tana cike da rashawa. Amma imani ba hujja ba ne. Kuma gwamnati ba za ta yi aiki a bisa zato cewa kowa barawo ba ne.

A bari masu bincike su gama aikinsu. A bari gaskiya ta fito fili. Jama’a su nemi gaskiya da adalci, domin duka biyun suna aiki tare.

Gaskiya tana da daraja fiye da jita-jita. Kada mu bar karya ta maye gurbin gaskiya.

Ganiyu Lamidi
Masani ne kan manufofin gwamnati da gyaran gudanarwa a Najeriya.

DA DUMI-DUMI: Mun bada cikakken hadin kai ga hukumar EFCC domin a bincike mu nida sauran ma'aikatan hukumar NAHCON, domi...
08/10/2025

DA DUMI-DUMI: Mun bada cikakken hadin kai ga hukumar EFCC domin a bincike mu nida sauran ma'aikatan hukumar NAHCON, domin tabbatar da gaskiya, tare da jaddada cewa ba za ta kare duk wanda aka samu da laifi ba, inji shugaban hukumar NAHCON Farfesa Sheikh Abdullahi Sale Pakistan.

A yanzu haka EFCC ta k**a wasu manyan jami’an hukumar biyu, su ne Aliu Abdulrazak, kwamishinan kula da ma’aikata da kudi, da Aminu Y. Muhammed, darektan kudi, domin cigaba da bincike.

Rahotanni daga jaridar The Guardian sun bayyana cewa Farfesa Usman ya amsa gayyatar EFCC a babban ofishinta da ke Abuja, inda aka tambaye shi kan yadda aka gudanar da wasu kudaɗe da s**a kai kimanin ₦50 biliyan da s**a shafi shirye-shiryen aikin Hajji na 2025.

Bayan tambayoyi, hukumar ta bashi umurnin komawa gida, amma ta umarce shi da ya rika bayyana kansa a ofishinta kullum yayin da bincike ke cigaba akan hukumar ta su.

Abubuwan da ake bincike a kai sun hada da;

Amfani da ₦25 biliyan wajen biyan kuɗin tantuna a Masha’ir ba tare da cikakken izini ba.

₦7.9 biliyan da aka ce an ware don masaukin gaggawa.

₦1.6 biliyan da aka yi amfani da shi wajen tafiyar matan wasu jami’an gwamnati.

Muna Addu'ar ALLAH ya bayyana gaskiya.

29/09/2025

Zuwaga “Junaidu Abubakar Bauchi” da wannan gayen “Abulfatahi”

Abunda kukeyi ba dai-dai bane, kalaman tunzura jama’a ne da neman kawo tashin hankali acikin al’umma

Idan har dagaske ku malammai ne masu ilimi, idan har dagaske ku masoyan annabi ne (saw)

To ku haɗo littafai kuzo jahar kano domin zaman muƙabala da “Sheikh Lawan Triumph”

Idan kunyi nasara da hujjoji daga “Alƙur’ani da ingantattun hadissan Annabi saw” zamu yarda kune masoya annabi, kuma zamu koma ɗariƙarku
———————————

Wannan soki burutsun da kukeyi an daina yayinsa

Yanzu al’umma sun waye, da hujja suke addini, kuma wannan hujjar dole yakasance daga alƙur’ani ko hadissan annabi saw 📌

Amma kawai sai kaga mutum ya ɗora camera yana soki burutsu babu hujja, menene banbancinku da g-fresh ɗan TikTok??

Alhassan Mai Lafia

29/09/2025

Sai fa kunzo an muqabalar nan ko ko ba ku so

Address

Minna

Telephone

+2348069801797

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al-Ikhlas TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Al-Ikhlas TV:

Share