Nurul Faidhaty Makurdi

Nurul Faidhaty Makurdi Nurul Alfaidha

Ahlan bisharil Maulidi
16/08/2026

Ahlan bisharil Maulidi

NURUL FAIDHATY MAKURDI TA KAI ZIYARAR GIRMAMAWA ZUWA GA AMBASSADOR SHEIKH NASIR ADO MUSA A BAUCHIA ci gaba da ziyarar da...
11/07/2026

NURUL FAIDHATY MAKURDI TA KAI ZIYARAR GIRMAMAWA ZUWA GA AMBASSADOR SHEIKH NASIR ADO MUSA A BAUCHI

A ci gaba da ziyarar da tawagar Nurul Faidhaty Makurdi ke gudanarwa a Jihar Bauchi, tawagar ta kai ziyarar girmamawa ga Amb Sheik Nasir Sheik Ado Musa ɗan fitaccen malami Sheikh Ado Musa, a gidansa da ke Bauchi.

Ziyarar ta gudana cikin yanayi na ƙauna, girmamawa da kyakkyawar mu'amala, tare da musayar shawarwari da addu'o'i domin ƙarfafa haɗin kai da ci gaban harkokin addini da na ƙungiyar.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya sanya wannan ziyara albarka ta zama sanadin ƙarfafa haɗin kai, kyakkyawar haɗin gwiwa da ci gaba ga Nurul Faidhaty Makurdi da kuma al'ummar Musulmi baki ɗaya.

Allah Ya ƙara ɗaukaka malamai, Ya haɗa zukatanmu a kan alheri, Ya albarkaci shugabanninmu da hikima da ikhlasi, Ya kuma ba ƙungiyarmu nasara da ɗorewar ci gaba.

Allah Ya amsa. Ameen.

– Tawagar Yaɗa Labarai (Media Team)
Nurul Faidhaty Makurdi

11/07/2026
ZIYARAR KUNGIYAR NURUL FAIDHATY MAKURDI ZUWA JIHAR BAUCHIAlhamdulillahi Rabbil-'Alamin.Tawagar Nurul Faidhaty Makurdi ta...
11/07/2026

ZIYARAR KUNGIYAR NURUL FAIDHATY MAKURDI ZUWA JIHAR BAUCHI

Alhamdulillahi Rabbil-'Alamin.

Tawagar Nurul Faidhaty Makurdi ta isa Jihar Bauchi lafiya, inda ta fara wannan Ziyara a Raudha (kabarin) Lisanul Faidha, Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.A.). Wanda yake a Sheikh Dahiru Usman Bauchi Islamic Center Bauchi

Allah Madaukakin Sarki Ya sanya wannan ziyara ta kasance cikin da samun Madadi da Taraqi da kuma albarka, Ya ba dukkan 'yan Kungiyar lafiya da kariya, Ya kuma mayar da mahalartan gida lafiya cikin rahamarsa.

Allah Ya amsa. Ameen.

– Tawagar Yaɗa Labarai (Nurul Faidhaty Media Team)

Alhamdulillah Barakallahu lakuma
24/06/2026

Alhamdulillah
Barakallahu lakuma

Come one come all
20/06/2026

Come one come all

إنا لله و إنا إليه راجعون الموة لا يضر من قد سعدا         بل هو راحة لمن قد رشداKungiyar Nurul Faidhaty na alhinin rasuw...
15/06/2026

إنا لله و إنا إليه راجعون
الموة لا يضر من قد سعدا
بل هو راحة لمن قد رشدا

Kungiyar Nurul Faidhaty na alhinin rasuwar daya daga cikin DattawanMu na Zawiyan Jagaran wannan Kungiyar Mai Albarka Sheikh Salisu Arifullah R.A wato Malam Baballau wanda ya rasu a ranar 14 ga watan June, 2026.

Muna mika ta'aziyyarmu ga 'yan Zawiya baki da iyalansa. Allah ya jaddada Rahma a gareshi

Ya Kyautata namu bayan nashi Alfarman Annabi Muhammadu S.A.W AMIN

SAKON TA'AZIYAR
✍️NURUL FAIDHATY MEDIA TEAM

12/05/2026
Kungiyar NURUL FAIDHATY na mika sakon taya murna ga daya daga cikin membanmu Ubaidullahi Ahmed, bisa nasarar kammala Pro...
01/04/2026

Kungiyar NURUL FAIDHATY na mika sakon taya murna ga daya daga cikin membanmu Ubaidullahi Ahmed, bisa nasarar kammala Program na National Youth Service Corps (NYSC).

Hakuri, jajircewa, da sadaukarwar da ka nuna wajen ci gaban kasa abin a yaba ne matuka. Muna taya ka murna tare da fatan samun babban rabo

Muna addu’ar wannan nasara ta zama farkon manyan nasarori a rayuwarka ta gaba.
Muna sake taya ka murna!

📝NURUL FAIDHATY MEDIA TEAM

Address

U
Makurdi

Telephone

+2347049151072

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Nurul Faidhaty Makurdi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Nurul Faidhaty Makurdi:

Shortcuts

Share