10/10/2026
BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA MASU CIN MUTUMCIN UNIFORM DIN AGAJIN JIBWIS
Zuwa ga: Wadanda abin ya shafa da daukacin al'umma masu amfani da kafafen sada zumunta (Social Media).
Assalamu Alaikum Warahmatullah Wabarakatuh,
Wannan sako ne mai cike da mamaki, tawaye, da kuma takaici kan irin halayya da dabi’un da wasu mutane s**a sa a gaba a kafafen sada zumunta na zamani. Abin takaici ne yadda aka koma amfani da Uniform din Agaji na JIBWIS wanda ke wakiltar mutunci, sadaukarwa, da hidima ga addinin Musulunci wajen aikata abubuwan da s**a sabawa siffar 'yan agaji.
Uniform din 'Yan Agaji ba kayan wasan kwaikwayo ba ne, kuma ba kayan neman "followers" ko "likes" ba ne a Tik Tok, Facebook, ko Instagram. Kayan ceto ne, kayan agaza wa al'umma ne, kuma rigar mutunci ce da magabata s**a gina da kyakkyawan suna da jinin guminsu.
Irinsu Shin Me Suke Aikatawa?
A yau, ana kallon wasu marasa kishin addini da mutuncin kungiya suna:
Karya da Kazafi: Amfani da rigar agaji wajen tsara labaran karya ko dorawa mutane sharrin da basu aikata ba.
Cin Mutunci da Wulaqanci: Sanya uniform din ana raye-raye, wasannin banza, ko barkwanci maras mutunci wanda ke zubar da kimar kungiyar JIBWIS na Kasa.
Rusa Aiki Mai Kyau: Batan bakin da mutum guda yake yi yana shafar dubban 'yan agaji na tsakani da Allah wadanda ke tsaye a rana, ruwa, da sanyi domin kiyaye tsaro da lafiyar al'umma.
Lura: Duk wanda yake sanye da wannan uniform, yana dauke da amana da hoton kungiyar JIBWIS gaba daya. Idan ka zubar da mutuncin rigar, ka zubar da mutuncin dubban 'yan agaji ne wadanda ke sadaukar da lokacinsu kyauta domin Allah.
🗣️Ameer Makarfi
Abubakar Idris Funtua
(State S.A Media II, F.A.G Of JIBWIS Katsina State Directorate)
10/10/2026