26/08/2026
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.
ina mai sanar da ku cewa Babban Limamin Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta Tarayya kuma shugaban majalisan malamai na abuja Jibwis, Sheikh Muhammad Auwal Maigaskiya, anyi masa aikin tiyatar ido a idonsa na dama ayau.
Saboda halin da yake ciki da kuma lokacin murmurewa bayan tiyatar, bazai samu damar jagorantar sallah na tsawon makonni 3 zuwa 4 ba.
Muna roƙon kowa da kowa da ya tuna da Babban Limamin a cikin addu’o’inku. Allah Ya ba shi cikakkiyar lafiya cikin gaggawa, Ya dawo masa da ganin idonsa, Ya kawar da dukkan ciwo da wahalhalu, Ya ba shi lafiya da ƙarfi domin ya ci gaba da hidima ga Addinin Musulunci da al’ummar Musulmi.
اللهم رب الناس أذهب البأس، واشفِ أنت الشافي، لا شفاء إلا شفاؤك، شفاءً لا يغادر سقماً.