25/05/2025
AIYUKAN HISBAH A TAƘAICE
1. AL-IHTISAB A FANNIN IMANI .
Yin wa’azi da umarni da kyakkyawan aiki a bangaren koyar da rukunan addini da imani.
2. AL-IHTISAB a FANNIN IBADU .
Kula da tsarkakewa da gyara a fannin ibadu kamar sallah, azumi, zakka, da sauran ayyukan ibada.
3. AL-IHTISAB A FANNIN MU’AMALATU.
Kula da halaltacciyar mu’amala a cikin kasuwanci, ciniki, da huldar yau da kullum.
4. AL-IHTISAB A FANNIN HALAYE. Yi wa mutane nasiha don gyaran dabi’u da kyautata halaye kamar gaskiya, aminci, da ladabi.
5. AL-IHTISAB A FANNIN HUKUNCI.
Kula da adalci da bin dokokin shari’a a yayin aiwatar da hukunci.
6. AL-IHTISAB A FANNIN GYARA. Gudanar da ayyuka don gyaran al’umma da kawar da barna da munanan dabi’u.
7. AL-IHTISAB TSAKANIN SASSA NA AL’UMMAR MUSULMI
Samar da tsari mai kyau na hada kan sassa daban-daban na al’umma ta hanyar umarni da kyakkyawan aiki da hani ga mummunan aiki.
8. AL-IHTISAB A KAN SHUGABANNI DA MASU IKO.
Kula da shugabanni da yi musu nasiha da basu shawara don tabbatar da adalci da bin dokokin shari’a.
9. AL-IHTISAB A KAN MALAMAI
Jawo hankalin malamai akan karantawa da wa'azi da tsage gaskiya cikin hikma ba tare da tsoro ko kwaɗayiba.
10. AL-IHTISAB A KAN MASU KUƊI.
Jawo hankalin masu wadata da arziki wajan taimakon addini da al'umma, wajan gina tattalin arziki mai Albarka da inganci da halacci bisa koyarwar addinin Musulunci.
11. AL-IHTISAB A KAN MA’AIKATA . Bibiyar ayyukan ma’aikata don tabbatar da kula da aiki da gaskiya da aminci.
12. AL-IHTISAB A KAN JAMI'AN TSARO.
Haɗa kai da jami'an tsaro don tabbatar da zaman lafiya, adalci da kare hakkin jama’a.
13. AL-IHTISAB A KAN WADANDA AKE ZARGI DA LAIFI DA MASU AIKATA LAIFIN
Yi musu nasiha da tsoratar da su fushin Allah, da jawo su a jiki don nuna musu hatsarin karya dokar Allah da abin da hakan zai jawo a duniya da lahira, Kula da su don tabbatar da an hukunta su bisa doka da kuma basu damar gyara halayensu.
14. AL-IHTISAB A KAN TALAKAWA. Yin nasiha da wa’azi ga talakawa don inganta zamantakewar al’umma da kuma kare kyawawan dabi’u.
15. AL-IHTISAB A KAN ƊAN HISBAH,
Jawo hankalin ma'aikatan Hisbah wajan kiyaye mutuncin aikin Hisbah da biyayya ga dokoki da tsoran Allah, da Haɗin kai.