07/06/2021
YANA YIN MU,UJIZA.
Naga masubi aduniya gaba daya dayawan su,suna cikin bakin ciki duk da suna yin addu'oi.
Yin addu'a,azumi,bayarwa,shuka iri,duk da haka rayuwarsu bai chanzuba kuma suna cikin takai ci,kewaye da su.
Wani pastor ya karbi sako awajen wata mace Yar kasar Kenya ta hanyar Facebook tace"limamin Krista,ina yin addu'a,shuka iri,yin rayuwar tsarki,kuma duk da haka banyi aure ba kuma babu abun da ke tafiya daidai arayuwata ina nemàn taimako sobada ina cikin takai ci a ruhaniyan ce".
Sautin sakon ya bai yana ciwon ta.
Na tambayi ubangiji mai yasa kristoci suna yin addu'a mai wuya duk da haka sak**akon karami ne ko kuma ba sak**ako da ya gamsar da addu'oi da kuma bayarwa. Bari muduba littafin, Markus 8:22-26.
S**a iso Betsaida.Aka kawo masa wani makaho,aka roke shi ya taba shi.23 ya k**a hannun makahon,ya kai shi bayan gari.Da ya tofa yau a idanunsa,ya dora masa hannu, Sai ya tambaye shi cewa "kana iya gani wani Abu ? 24 Sai makahon ya daga kai ,ya ce ,ina gani mutane kam, k**ar itatuwa nake ganinsu suna yawo."25 sai ya sake dora hannu a idanunsa.makahon ya zura ido kwar,ya warke,ya ga komai garau. 26 sai Yesu ya sallame shi ya koma gida,ya ce,"ko kauyen ma kada ka shiga.
Tambaya a nan
Mai yasa Yesu ya k**a hannun makahon ya kai shi bayan gari?
Mai yasa bai warkar dashi ba,a wannan wurin ba ?
Dalili shine:
*Wannan wurin yana gaba da nasaran shi.
*Wannan wurin yana gaba da makomarsa.
*Wannan wurin yana gaba da Albarkansa.
Har idan kana wuri mara kyau wato wurin da ba Allah ne ya shirya maba, komai addu'oi ka da bayarwa da azumi zai zamanto ba sak**ako don haka yana da kyau idan zaka fara wani aiki ka tambaye ubangiji shin wanna aikin ya da ce da ni,haka ma in zaka koma wani wuri ku nime nufin Allah kafin ku komai.