21/09/2023
Zo Ka Ji Dariqar Shehu Tijjani Bata Saba Ma Shari'a Ba.
Wanda Yake Lazumi Sai Dayan Iyaye (Uwa Ko Uba) S**a Kira Shi Zai Amsa Kiransu Kuma Babu Komai Gare Shi Na Jabaru.
Wanda Yayi Magana Da Ta Zarce Kalma Biyu A Cikin Lazumi To Wannan Jabaru (Istigfari Guda 100)Ta K**a Shi Bayan Ya Gama Lazuminsa.
Wanda Ya Samu Rabkannuwa Cikin Lazuminsa Da Ragi Ko Kari Shi Ma Jabaru Ta K**a Shi (Istigfari Guda 100) Bayan Ya Kammala Lazuminsa Amma Idan Ragi Ne Sai Ya Cika Abinda Ya Rage Sannan Yayi Jabaru.
Wanda Ya Samu Masu Wazifa Suna Wazifa Zai Yi Niyya Ne Ya Bi Su Abinda Ya Yi Saura Ya Cika Bayan An Kammala Amma Zai Faru Daga Farko Ne.
Wanda Yake Lazumi A Cikin Masallaci Sai Kuma Lokacin Sallah Yayi Liman Ya Zo, Zai Kula Ne Da Inda Ya Tsaya Ya Tashi Ya Bi Jama'in Sallah Bayan An Kammala Sallah Sai Ya Cika Lazuminsa.
Wazifa Da Zikirin Juma'a Cikin Jam'i Wajibi Ga Wanda Ya Karbi Dariqar Shehu Tijjani Sai Dai In Da Wata Larura Da Hana.
Amma Mata Wazifarsu Da Zikirin Juma'a Duk A Gida Ne.
Ba'a Tilasta Ramuwa Ba Ga Wanda Zikirin Juma'a Ya Kubuce Masa Sai Dai Ya Rasa Alkhairai Masu Yawa Amma Za'a Iya Biyanta Hailala Dubu Daya (1000) Ko Sama Da Haka.
Babu San Rai Ko Ganin Dama Cikin Dariqar Shehu Tijjani Sai Tsantsar Koyi Da Annabi Muhammad Salawatullahi Wasalamuhu Alayhi.
Allah Ya Ba Mu Ikon Kulawa Da Abinda Muka Karba Na Lazumi Da Gaskiya Allah Ka Cire Mana Riya Ko Ganin Mun Fi Wani Albarkar Saukaken Safar Maulaya Ahmad Bin Muhammad At-Tijaniyy (RTA)
Mun Gode Shehu 🙏🙏🙏
Allah Yakara Lafiya Da Nisan kwana.
Tijjaniyya24TV
Sayyada Ummuhani Ibrahim Niasse Tv
Baye Mansur TV
Sharubutu TV
Imam Junaidu Abubakar Bauchi
Prof. Ibrahim Maqari