26/12/2025
Allah Subhanahu-Wata'ala Ya Halicci Bayinsa Ne Domin Su Shagaltu Da Bauta Masa Babu Dare Babu Rana.
Ta Yadda Mutum Zai Kasan Ce A Koda Yaushe Yanada Kusanci da Allah Subhanahu-Wata'ala.
To Daga Lokacin Da Mutum Ya Shagaltu Da Allah Subhanahu-Wata'ala.
Shi Kuma Daga Lokacin Ne Allah Subhanahu-Wata'ala Zai Kasance Tare Da Wannan Bawan Nasa.
Tun Daga Nan Duniya Harzuwa Ranan Lahira Allah Zai Ɗebe Masa Baƙincikin Duniya Da Baƙin Cikin Lahira Sannan Allah Zaiyi Masa Arziki Wanda Babu Iyaka Tun Daga Nan Duniya Harzuwa Lahira.
Wannan Shine Sakamakon Mutumin Dayayi Riƙe Allah Subhanahu-Wata'ala.Sannan Kuma Ya Shagaltu Da Allah Subhanahu-Wata'ala ɗin
Wato Ya Kasance Bai Ganin Kowa A Gabansa Sai Mahaliccinsa Idan Mutum Ya Tsinci Kansa A Wan'nan Yanayi To Haƙiƙa Baiyi Asaran Zuwa Duniya Ba Sannan Kuma Ya Sami Babban Rabo
------------ Sai Kuma Mutumin Da Ya Saki Allah Ya Shagaltu Da Wanin Allah.
To Haƙiƙa Shi Kuma Duk Mutumin Daya Saki Allah Subhanahu-Wata'ala Ya K**a Wanin Allah Subhanahu-Wata'ala To Daganan Shi Kuma Allah Subhanahu-Wata'ala Wata'ala Sai Ya Saki Wannan Bawan Shima.
To Daganan Ne Zakaga Mutum Ya Zama Bawan Duniya Sannan Kuma A Ƙarken Rayuwansa Zai Kasance Ne Yayi Asaran Duniyan Sa Da Kuma Lahiransa
Allah Subhanahu-Wata'ala Yasa Mudace Duniya Da Kuma Lahira AL-farman Annabin Rahama Da Iyalangidansa.
------------------Tunatarwa Ne : Tare Da Barka Da Ranan Juma'a
Daga : Khalid Ahmad Adam Al-Kudaneey