Garkuwan shugabah sk

Garkuwan shugabah sk Umarni da Kyakkyawa, hani ga mummuna

KTSHBKATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISIONRANA TA FARKO (1): WA'AZIN GORON SALLAH.A yau Talata 3 ga watan Shawwal Hijrah dag...
02/04/2025

KTSHB
KATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION

RANA TA FARKO (1): WA'AZIN GORON SALLAH.

A yau Talata 3 ga watan Shawwal Hijrah daga makka zuwa madina shekara 1446 dai dai da 1 ga watan Aprilu Miladiyya Haihuwar Annabi Isah (A.S) shekara ta 2025 Hukumar Hisbah ta karamar hukumar katsina a karkashin jagorancin malam shamsu kabir ta gabatar da wa'azin goron sallah rana ta farko a babban masallacin Juma'ah na garin shinkafi katsina.

A inda Sheik Malam Zainu Abubakar ya gabatar da wa'azi da kuma Shugaban Hukumar hisbah na karamar hukumar katsina malam shamsu kabir ya gabatar da ta'aliqi akan wa'azin, wanda yayi gabatar kuma malam Muhammad Isah Sardauna.

Maudu'in wa'azin shine: Tarbiyya da kuma Muhimmancin ta a
Musulunci.

Wa'azin yayi magana akan:

1. Ma'anar Tarbiyya
2. Yaya ake bada Tarbiyya
3. Minene Hukuncin Tarbiyya a Musulunci.
4. Sharuddan cikar tarbiyya.
5. Muhimmancin Tarbiyya a Musulunci.
Daga karshe Babban Limamin Masallaci Sheik Ibrahim Idris ya rufe taron da addu'a.

Reported by:
Sardauna ICT Unit Hisbah Board KTLG

Katsina Local Government HISBAH command has appreciated the activities of Katsina state Television Service for introduci...
26/03/2025

Katsina Local Government HISBAH command has appreciated the activities of Katsina state Television Service for introducing programs that project the good image of Islam to the general public.

The Management of the command under the leadership of Malam Shamsuddeen Kabir made the appreciation when they paid a courtesy visit to the station.

Commander Shamsu Kabir explained that the visit is imperative in view of the importance of Media towards improving the lives of the people in a community.

He said the number of the Islamic programmes being aired by KTTV assist to enlighten people to know more about the religion of Islam.

Katsina Local Government HISBAH Media team reports that the commandant used the time of the visit to pray for the repose of the life of Governor Dikko Radda،'s Mother who died recently.

The General Manager of Katsina State Television Service Malam Abba Zayyan assured the support and co-operation of KTTV to all Katsina Local Government HISBAH command activities.

Malam Abba Zayyan advised the HISBAH team on various aspects that could improve their activities for the betterment of the common man.

Katsina Local Government HISBAH Command Media Team

KTSHBKATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.SHUGABAN HUKUMAR HISBAH NA JIHAR KATSINA TARE DA SHUGABAN HUKUMAR HISBAH NA KARAM...
25/03/2025

KTSHB
KATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.

SHUGABAN HUKUMAR HISBAH NA JIHAR KATSINA TARE DA SHUGABAN HUKUMAR HISBAH NA KARAMAR HUKUMAR KATSINA SUN HALARCI TARON BADA TALLAFIN SHINKAFA.

A yau talata 25 ga watan Ramadan 1446 dai dai da 25 ga watan Maris Miladiyya ta 2025 babban Kwamandan hisbah na jihar katsina Shiekh Aminu Usman (Abu Ammar).PhD tare da Shugaban hukumar hisbah na karamar hukumar katsina malam shamsu kabir sun halarcin taron bada tallafin shinkafi wanda Hadin gwaiwar Gwamnatin jihar katsina da Gidauniyar Dangote ta bayar.

Wanda taron ya gudana ne a Muhammad Dikko Stadium (Karakanda), kowane mutane daga sashe na kowane wards sun samu tallafin shinkafar.

Reported by
Sardauna ICT Unit Hisbah Board KTLG

KTSHBKATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.SHUGABAN HUKUMAR HISBAH NA KARAMAR HUKUMAR KATSINA YA JAGORANCI RUFE TAFSEER AL-Q...
24/03/2025

KTSHB
KATSINA LOCAL GOVERNMENT DIVISION.

SHUGABAN HUKUMAR HISBAH NA KARAMAR HUKUMAR KATSINA YA JAGORANCI RUFE TAFSEER AL-QUR'ANI MAI GIRMA NA WATAN RAMADAN 1446 A GARIN BARDA.

A yau Litinin 24 Ga watan Ramadan Hijra ta 1446 dai dai da 24 ga watan Maris Miladiyya ta 2025 shugaban hukumar hisbah na karamar hukumar katsina malam shamsu kabir ya jagorancin Rufe Tafseer Al-Qur'ani mai Girma na watan Ramadan 1446 a garin Barda wanda kungiyar NAJWA ta gabatar a wannan shekarar 1446/2025.

A inda shugaban hukumar hisbah na karamar hukumar katsina ya gabatar da nasiha sosai wajen kiyaye zamantakewar iyali, biyayya kula da tarbiyya tare da jan hankali akan neman ilimi a ko da yaushe.

Reported by
Sardauna ICT Unit Hisbah Board KTLG.

Address

Katsina

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Garkuwan shugabah sk posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share