27/06/2026
TOTAL SUBMISSION TO AHLUL BAITY RECORD – A Sahun Muzahara
A wannan rana mai tarihi, TOTAL SUBMISSION TO AHLUL BAITY RECORD (TS2AB) sun fito a cikin sahun masu muzaharar Ashura, don nuna cikakkiyar wulayar mu ga Imam Husain (AS) da kuma bayar da mummunar amsa ga Yazid da irin mugayen ra’ayinsa.
Fitowarmu a wannan sahu ba kawai alama bace, illa kuwa wata shaida ce ta daukakar saƙon Husaini — cewa mu matasa ne da muke bin tafarkin Ahlul Baiti (AS) da ƙin zalunci da munafunci a kowane zamani.
Me Muke Nufi da Wannan Fitowa?
Wulaya ga Imam Husain (AS): Muna bayyana cewa zuciyarmu da aikace-aikacenmu na goyon bayan Ahlul Baiti ne.
Baraa daga Yazid: Muna nesanta kanmu daga Yazid da mabiyansa – wadanda s**a haddasa wannan mummunar kisan kiyashi.
Sadar da Saƙo: Muna sanar da duniya cewa 'yan Husaini har yanzu suna raye, suna jaddada saƙon adalci da gaskiya.
Saƙo ga Duniya:
> “Na fita ne domin gyara cikin al'ummar kakana... Ina so in umarci alheri kuma in hani mummuna, in bi hanyar kakana Manzon Allah (SAWA) da kakana Ali bn Abi Talib (AS).”
— Imam Husain (AS)
Wannan shi ne saƙonmu — mu kasance masu tsayawa da gaskiya, kawar da zalunci, da girmama Ahlul Baiti (AS) da ƙin biyayya ga mummunan tsarin Yazid.