10/07/2023
YADDA SALAF KE KULA DA MATANSU
Daga shafin Dr. Kabir Asgar
Al-Imam Azzahabiy (RahimahulLah) ya naƙalto labarin Kulthum Ɗiyar Abubakar (RA). Kulthum ta ce: "Na kasance ina addu'a ina cewa: Ya Allah! Ka ba ni miji nagari mai kula da addini, kuma wanda zai lulluɓe ni da soyayya"
Da Allah ya tashi karɓan addu'arta sai a azurta ta da Ɗalhat Ɗan Ubaidullahi (Ɗaya daga cikin mutanen nan goma da aka wa bushara da aljanna).
Kulthum tana ba da labarin irin yadda mijinta ke ji da ita sai ta ce:
"Ɗalhatu ya kasance idan ya kalle ni sai ya yi hailala.
In ya jiyo muryata sai ya yi murmishi
In na fashe da kuka, shima sai ya fashe da kuka
Ba ya yin barci sai ya tabbatar da cewa an gyara min gadona
In ya idar da sallah ba ya yi ma kansa addu'a sai ya fara da ni
In ba ni da lafiya, yakan shiga cikin damuwa, kai ka ce zafin ciwon a jikinsa yake
Ba shi da kwanciyar hankali sai ya ganni zaune a kusa da shi
In muna cin abinci yakan riga ni kai loma bakina
Na kasance abin alfaharinsa a ɓoye da sarari"