14/07/2025
Shugaba Bola Tinubu ya nuna alhinin rasuwar tsohon shugaban ƙasar inda ya miƙa ta'aziyarshi ga matar marigayin Aisha Buhari.
Shugaban ya kuma umarci a yi ƙasa-ƙasa da tutocin Najeriya domin girmama tsohon shugaban.