Al-injaz Media

Al-injaz Media Tattaunawa akan Addini da rayuwa

27/11/2025

Daren Juma'a da kuma yinin Juma'a, lokuta ne da ake son yawaita salati ga Annabi صلى الله عليه وسلم

21/11/2025

Allah maɗaukakin sarki

Hanyar sanin Allah subhanu wa ta'alaa itace wahayin da Allah ya saukar wa bayinsa ta hanyar Annabawa.

Idan ka kalli Alkur'ani zaka ga gaba ɗayan sa yana magana ne akan Allah da abinda yake da alaƙa dashi, don kodai kaga magana akan sunaye da siffofin Allah ko kuma umarnin Allah ko hanin sa, sai kuma abinda Allah ya tanadarwa masoyan sa masu yi masa biyayya, ko uƙubar da ya tanadarwa makiyan Addinin sa masu saɓawa umarnin sa, ko ya bada misali akan waɗanda s**ayi masa ɗa'a da yadda ya taimakesu ko maƙiyansa da yadda ya halakar dasu ko yayi masu talala mai kamar sake.

Abin nufi dai shine; Alkur'ani gaba ɗayan sa yana koyar da yadda za a san Allah da yadda za a sami yardarsa a kuma gujewa fushin sa don a sami kyakykyawar rayuwa a duniya da lahira.

Hamza Diso

19/11/2025
17/11/2025
08/04/2025

Ka tsaya a inda kake ka bautawa Allah a gurin.

Daga Abu Sa'ed Allah ya yarda dashi, wani mutumin karkara yazo gurin Annabi sallallahu alaihi wa sallam ya tambayeshi game da hijra ( Yana so ya baro kauyensu ya dawo gurin Annabi) Sai Annabi yace masa, ahir dinka, sha'anin hijrah Yana da tsanani ( nauye nauyenta da hukunce hukunce) Amma ka na da rakuma? Mutumin yace: Eh, Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) yace: kuma kana bayar da zakkarsu? Mutumin yace : Eh, Sai Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) yace: acikinsa akwai wacce kake bayarwa (ga mabukata) su tatsi madararta? Mutumin yace: Eh, sai Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) Yace: Kuma kana tatsar madarar idan anje bawa rakuman ruwa? Mutumin yace Eh, sai Annabi (sallallahu alaihi wa sallam) yace: ka yi aikinka (na da'a) a kauyen, Don Allah ba zai tauye Maka komai cikin ayyukanka ba.

Bukhari da muslim

جَاءَ أعْرَابِيٌّ إلى النَّبيِّ صلَّى اللهُ عليه وسلَّمَ، فَسَأَلَهُ عَنِ الهِجْرَةِ، فَقالَ: ويْحَكَ! إنَّ الهِجْرَةَ شَأْنُهَا شَدِيدٌ، فَهلْ لكَ مِن إبِلٍ؟ قالَ: نَعَمْ، قالَ: فَتُعْطِي صَدَقَتَهَا؟ قالَ: نَعَمْ، قالَ: فَهلْ تَمْنَحُ منها شيئًا؟ قالَ: نَعَمْ، قالَ: فَتَحْلُبُهَا يَومَ وِرْدِهَا؟ قالَ: نَعَمْ، قالَ: فَاعْمَلْ مِن ورَاءِ البِحَارِ؛ فإنَّ اللَّهَ لَنْ يَتِرَكَ مِن عَمَلِكَ شيئًا.
أخرجه البخاري كتاب مناقب الأنصار ب هجرة النبي صلى الله عليه وسلم وأصحابه إلى المدينة 2/257 الحديث 3923 وفي الزكاة ب زكاة الإبل عن على بن عبد الله.
وأخرجه في كتاب الأدب ب ما جاء في قول الرجل ويلك 3/170 الحديث 6165 عن سليمان بن عبد الرحمن.
وأخرجه مسلم كتاب الجهاد والسير ب المبايعة بعد فتح مكة..... 7/8 الحديث 1865 (مع المنهاج) عن أبي بكر بن خلاد الباهلي
ثلاثتهم ( على بن عبدالله وسليمان والباهلي) عن الوليد بن مسلم.
وأخرجه البخاري كتاب الهبة وفضلها ب فضل المنيحة 2/24 الحديث 2633 ومسلم 1865 عن الدارمي كلاهما ( البخاري الدارمي) عن محمد بن يوسف.
كلاهما ( الوليد بن مسلم و محمد بن يوسف) عن الأوزاعي عن الزهري عن عطاء بن يزيد عن أبي سعيد الخدري رضي الله عنه به.

Hamza Diso

05/04/2025

Annabi sallallahu alaihi wa sallam yace: Wanda ya yi kiyamullaili da Aya 10 ba za a rubutashi cikin rafkanannu ba, Wanda ya yi kiyamullaili da Aya 100 za a rubuta shi cikin masu yawan da'a, Wanda kuma ya yi kiyamullaili da Aya 1000 to za a rubuta shi cikin masu tarin Lada Mai yawan gaske.

Abu Dawud, Ibnu khuzaimah da Ibnu Hibban s**a ruwaito da isnadi Hassan zuwa Abdullah Dan Amr.

Ka daukarwa kanka wani rabo cikin dare Don samun kusanci da kuma soyayyar Allah madaukaki

Hamza Diso

Address

Kano
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al-injaz Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share