Madrasatu Sufyan Litahfizil Qur'an

Madrasatu Sufyan Litahfizil Qur'an Islamiyya Primary School. Community page

08/09/2024

Alhamdulillah Hamdan Kasîran.

Allah Ya azurta ni da samun ƙaruwar ƴa mace a wannan rana.

" Ina rokon Allah Ya tsare ta da zuriyarta daga sharrin Shaidani korarre daga rahamar Allah "

Ni da mai jegon da jaririyar duk muna lafiya. Alhamdulillah.

(Almighty Allah in his infinite mercy has blessed me with a baby girl, pls pray for her)

06/06/2024

WASU DAGA KYAWAWAN ADDU'O'IN DA MANZON ALLAH (s.a.w) YAYI WA SAHABINSA MU'AWIYAH DAN ABI SUFYAN (R.A)...

# Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:-
‎((اللهم علم معاوية الكتاب والحساب وقه العذاب)).

Ma'ana: ((Ya Allah Ka sanar da Mu'awiyah Littafi, da Hisaabi, Ka kuma tsare shi daga Azaba)). Tabbas addu'ar Annabi karbabbiya ce.

# Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce wa Mu'awiyah:-
‎((اللهم اجعله هاديا مهديا واهد به)).

Ma'ana: ((Ya Allah Ka sanya shi mai shiryarwa, kuma Shiryayye, Ka kuma shiryar ta hanyarsa)). Tabbas addu'ar Annabi karbabbiya ce.

Allah ya qara yarda wa Mu'awiyah da Aliyu da Abubakar da Umar da Usman da sauran sahabbai baki daya, Allah ya qara mana kaunarsu ya tashemu a tutarsu, tutar Annabin rahama Manzon Allah.

(via: Dr Jalo Jalingo(H) )

23/05/2024

Allah Ya azurta Kano da sarki mai addini mai nagarta da kimanta al'umma da martabata, da tsare mata mutunci. Duk wanda zai zama alheri a Kano Allah Ya kawo shi, duk wanda zai zama barazana ga al'umma da addininta da al'adunta masu kyau Allah Ya yi nesa da shi. (Ameen).

~malam Nuhu Ubale Ibrahim

12/01/2024

الصبر: عند الصدمة الاولى.

23/11/2023

ALIYYU IBN ABI ƊALIB !!

Sayyadina Ali Sahabin Annabi ne, ɗan uwa Manzon Allah kuma Sirikinsa, shine na huɗu a cikin khalifofin musulunci (bayan Abubakar, Umar da Usman).

Jarumi ne a cikin Sahabbai kuma faƙihi malami a cikin Sahabbai.

Allah ya ƙara yarda wa Ali da Abubakar da Umar da Usman da Mu'awiyah bn Sufyan da Sauran Sahabbai baki ɗaya.

Allah ya ƙara yarda da Aminci a garesu, Allah ya karbi rayuwarmu muna masu yarda da biyayya garesu.

17/11/2023

Ƴan uwa kada fa mu shagala, yau Juma'a mu yawaita Salati ga Annabin Rahama.

01/11/2023

MU'AWIYAH ƊAN ABI SUFYAN.

Cikakken Sunansa Shine:-
Mu'awiyya bn Abu-Sufyan bn Sakhr bn Harr bn Umayya bn AbdusShams bn AbduManaf bn Ƙutayyu bn Manaf Alƙurashiyyu Al'umawiyyu.

Mu'awiyya ɗan uwan manzon Allah ne domin sun haɗa Nasaba da Annabi s.a.w a kakansa na biyar wato ABDU-MANAF.

Mu'awiyya Surukin Manzon Allah ne domin Annabi s.a.w ya Auri ƴar uwar Mu'awiyya wato HABIBA BNT ABI-SUFYAN.

Mu'awiyya Sahabin Manzon Allah ne, Surukin Manzon Allah ne, Sakataren (marubuci) Manzon Allah ne kuma Amintacce (wanda suke rubuta wahayi) ne a wajen Manzon Allah..

MU'AWIYYA SAHABI NE MAI FALALA DA DARAJA.
Allah ya ƙara yarda a gareshi dashi da Mahaifinsa da ƴar uwarsa (matar manzon Allah) da Sauran Sahabbai baki ɗaya.

01/05/2022

قال تعالى: "فمن شهد منكم الشهر فليصمه"

Ɗan uwa shin watan kake azumta ko wasu kwanaki na watan?

Shari'a dai cewa tayi a azumci watan, kuma watan yana iya cika kwanakinsa wani lokacin kuma baya cikawa.

Allah ya karbi ibadunmu ya bamu dacewa.

27/06/2021

SHIN KANA SO ƊANKA/ƳARKA SU HADDACE ALƘUR'ANI ??

Assalamu alaikum warahmatullah.

Hukumar Madrasatu Sufyan Litahfizil Qur'an dake unguwar Gadon kaya, Ta fara tattara sunayan Daliban aji na musamman Mai gajeran zango na haddar Al'Qurani Mai girma a wata 18 a ranekun Asabar da Lahadi tsawon mako 60.
Maza da Mata wandanda s**a iya karanta Al'Qurani sosa.

Don Karin bayani a kira wannan:

Atika Uba Kamfa
08063866800
08092818111

Ku taimakawa ya'yanku su haddace Al'Qurani zasu zama sanadin daukakarku a Ranar alkiyama.

22/06/2019

Koyon Alkur'ani daban haka ma Bara da Roqo daban.
Ma'abota Alkur'ani basu yin Bara domin suna da wadatar zuci.

15/05/2019

Watan Ramadana yayi Nisa sosai !!

Mun gode Allah, wai har anyi azumi goma yau.
Hakika lokacin yana matukar sauri. Dan uwa muyi kokari mu ribaci kwanakin da s**a rage mana a cikin wannan wata mai albarka.

Ya kamata mu qara dagewa mu ninka ayyukan alkhairi na ibada da mukeyi, wallahi kana zaune kamar yau zakaji watan ya qare.

Babbar asara ne Ramadan yazo ya tafi bamu ribaceshi yanda ya kamata ba.
Kamata yayi mu watsar da wannan gurbatacciyar siyasar, siyasar da take son haifar da gaba a tsakaninmu, mu shagala da karatun Alkur'ani da salloli da zikiri da salatin Annabi.

Allah ya karbi ibadunmu ya bamu dacewa.

15/05/2019

Alhamdulillahi.

Madrasatu Sufyan Litahfizul Qur'an dake Unguwar Gadon kaya, Kano na sanar da cewa mun kammala zango na karshe a wannan shekarar karatu ta 2018/19.
Hutu ya fara daga 07/ramadan zuwa 11/shawwal, Kuma Insha Allah da zarar an dawo hutu za a fara daukar sabbin dalibai.
A madadin daraktar makaranta muna yiwa iyayen dalibai fatan alkhairi da fatan dacewa da dukkan alkhairan dake cikin wannan wata mai albarka. Allah ya karbi ibadunmu ya bamu dacewa, Allah yayi mana jagora.

Address

No_ 355 SKG/Kaya Gadon Kaya Quarters
Kano

Opening Hours

Monday 15:30 - 18:00
Tuesday 15:30 - 18:00
Wednesday 15:30 - 18:00
Saturday 08:30 - 18:00
Sunday 08:30 - 18:00

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Madrasatu Sufyan Litahfizil Qur'an posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share