Masjid Mus'ab Bin UMAIR KOFA

Masjid Mus'ab Bin UMAIR KOFA Jami'u ABU-HURAIRAH, Kofa

Assalamu Alaikum !A jiya Talata 21st July, 2026 sakataran wannan kwamiti mai albarka na AL-YATAAMA, kuma na'ibin Liman n...
22/07/2026

Assalamu Alaikum !

A jiya Talata 21st July, 2026 sakataran wannan kwamiti mai albarka na AL-YATAAMA, kuma na'ibin Liman na II na Masallacin Mus'ab Bn Umair, Kofa, watau Malam Umar Nasir Kofa ya bar gida Nijeriyya domin zuwa ƙasa mai tsarki don gudanar da aikin Umara.

Malam Umar tare da wasu daga cikin mutanan wannan gari mai albarka sun bar gida Nijeriyya a jiya Talata da misalin karfe 11 na safe wanda yanzu haka sun sauka a kasa mai tsarki domin gudanar da ibadah.

Muna addu'ar, Allah ta'ala yasa suyi ibada karbabbiya, ya kuma dawo mana dasu gida lafiya.

Sanarwa: Abdulrazak Aminu Kofa, Publication Chairman, AL-YATAAMA Foundation, Kofa.

17/07/2026

Khudubar Juma'a Daga Masallacin Mus'ab Bn Umair, Kofa

Maigabatarwa: Mal. Nasir Zakariyya

Maudu'i: Godiya a Bisa Ni'imar Allah

Assalamu alaikum wa rahamatullahi wa bara katuhu.A madadin Hukumar ilimin bai daya ta jahar Kano (SUBEB) Tareda hadin gu...
14/07/2026

Assalamu alaikum wa rahamatullahi wa bara katuhu.

A madadin Hukumar ilimin bai daya ta jahar Kano (SUBEB) Tareda hadin guiwar ma aikatar ilimi ta karamar hukumar Bebeji.
A Kar kashin shugabancin wannan makaranta Mai suna kamar haka.
GJSS KOFA CO EXIST

Shugabancin makarantar yana farin cikin gayyatar al'ummar wannan gari da kewayansa maza da mata gurin gagarumin bikin yaye dalibai maza da mata na shekarar 2025/2026.
Kimanin dalibai {212} Wanda s**a Kammala karatunsu a matakin karamar sakandire.

Muna addu'a tareda rokon Allah madaukakin sarki ya yiwa abin da aka karanta albarka Ameen.

10/07/2026
26/06/2026

Khudubar Juma'a Daga Masallacin Mus'ab Bn Umair, Kofa

Maigabatarwa: Mal. Umar Nasir Kofa

Maudu'i: Tunatarwa Akan Lamarin Mutuwa

Innalillahi wa'inna ilaishi raji'un ! !! !!!A yammacin wannan rana ta Alhamis 10th Muharram, 1448 wanda yay daidai da 25...
25/06/2026

Innalillahi wa'inna ilaishi raji'un ! !! !!!

A yammacin wannan rana ta Alhamis 10th Muharram, 1448 wanda yay daidai da 25th June, 2026 Allah ya karbi ran daya daga cikin mutane masu kima a garin Kofa, watau Alhaji Danladi Kofa.

Marigayin ya rasu sakamakon rashin lafiya wanda ya dade yana fama da ita a tsaitsaye, inda daga jiya Laraba zuwa yau rashin lafiyar ya tsananta kafin daga karshe Allah ya karbi ransa a yammacin yau.

Kafin rasuwar sa, Alh. Danlami Kofa ya kasance daya daga cikin jiga-jigan mutane a garin Kofa dama karamar hukumar Bebeji baki daya.

Alhaji ya hidimtawa Kofa ta fuskoki da dama wanda ya hada da: Addini, zaman takewa, ilimi, jagoranci, sulhu, shugabanci dasauransu.

Kafin rayuwar sa ya kasance daya daga cikin 'yan kwamitin Masallacin Mus'ab Bn Umair, Kofa, haka zalika yana daya daga cikin 'yan kwamitin marayu na AL-YATAAMA Foundation, Kofa dasauransu

Ko shakka babu marigayin ya bayar da gudunmawa mai tarin yawa danganin tabbatuwar cigaban garin Kofa dama karamar hukumar Bebeji baki daya.

Abune bayyanan ne cewa Alhaji mutum ne mai gaskiya, amana, yawan Ibadah, kyautata mu'amala dasauran kyawawan halaye.

Muna addu'ar Allah ta'ala yay masa rahma, ya haskaka makwancin sa, ya taimaki bayan sa, ya bawa iyalansa da abokanan sa jure wannan babban rashi.

Abdulrazak Musa Kofa

Publication Chairman AL-YATAAMA Foundation.

19/06/2026

Khudubar Juma'a Daga Masallacin Mus'ab Bn Umair, Kofa

Maigabatarwa: Mal. Zakariyya Abubakar

Maudu'i: Zaburarwa Akan Yawaita Ayyukan Alkhairi a Cikin Wannan Sabuwar Shekarar (1448-2026).

12/06/2026

Khudubar Juma'a Daga Masallacin Mus'ab Bn Umair, Kofa

Maigabatarwa: Mal. Ramadan Aminu

Maudu'i: Yiwa Kai Hisabi Kafin........

Address

KOFA
Kano
711104

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Masjid Mus'ab Bin UMAIR KOFA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category