Al'ansar Islamic Movement

Al'ansar Islamic Movement واعتصموا بحبل الله جميعا ولا تفرقوا

Wannan qungiya an kafata a shekarar 2015 qarqashin jagorancin Imamul-fasihiy (اِمَامُ الفََصِيحِي) tare da hadin gwiwar wasu qungiyoyin addinin musulunci. Wannan qungiya ta dauki gabarar yaqar dukan wata bidi'ah a ban qasa da izinin Allah (ﷲ), fatan 'yan uwa ma'abota kishin addinin musulunci za'a shigo don ba da gudun mowa cikin wannan qungiya mai albarka.

Babu bukatar karin bayani; domin wannan ban-bancin a bayyane ya ke.Allah ya a datar da mu.
01/09/2024

Babu bukatar karin bayani; domin wannan ban-bancin a bayyane ya ke.

Allah ya a datar da mu.

10/08/2024

"Yan uwa lallai mu kara komawa ga Allah, ku mu gyara kura-kuren mu tsakanin mu da shi, tabbas za mu gyara.

© Al'ansar

09/08/2024

Allahumma Salli Alã Sayyidina Muhammad, Wa Alã Ãli Sayyidina Muhammad.

© Al'ansar

08/08/2024

Mu lazimci yawaita salati a rana da kuma daren Juma'a, hakika akwai dace cikin yawaita salatin Annabi (SAW).

© Al'ansar

08/08/2024

Allah ya kawo wa al'umma saukin motsin rayuwar da ake fama da shi.

Kuma ya wadata su da dukkan abin bukata.

Mu dinga taimakon na kasa da mu, musamman a cikin yanayin nan da ake ciki na kunci da talauci, da sannu taimakon Allah z...
29/07/2024

Mu dinga taimakon na kasa da mu, musamman a cikin yanayin nan da ake ciki na kunci da talauci, da sannu taimakon Allah zai yi mana kawanya. Kuma mai taimaka wa ba ya rasa wa.

Allah waffaqar da mu.

© Al'ansar Islamic Movement (AIM)
29th July 2024

20/07/2024

Mafi girman farin-ciki a duniya shi ne; mutum ya wayi gari Musulmi, zuciyar sa cike da soyayyar Annabi Muhammad (SAW).

© Al'ansar

Idan Shehin ka ko Malamin ka ya zo da dai-dai; ka tafi tare da shi cikin dai-dan. Amma idan ya zo da sa6anin dai-dai kuw...
20/07/2024

Idan Shehin ka ko Malamin ka ya zo da dai-dai; ka tafi tare da shi cikin dai-dan. Amma idan ya zo da sa6anin dai-dai kuwa; to lallai ka ratse masa.

Wannan shi ne batu na gaskiya.

Allah ya waffaqar da mu.

©️ Al'ansar Islamic Movement ((AIM))
20th July 2024

19/07/2024

Ilimi ne kadai ke iya haskawa mutum tafarki mafi kyawun da zai bi, jahilci kuwa babu abinda ya ke haifarwa sai nadama!

© Al'ansar

19/07/2024

Yau Juma'a mai albarka, rana ce ta yawaita Salati ga Annabi (SAW), tare da dagewa wurin ambaton Allah da Istighfari.

© Al'ansar

18/07/2024

Daga illolin da aka yi wa al'ummar Musulmi a wannan zamanin shi ne kautar da hankulan su ga barin harkokin ilimi.

© Al'ansar

17/07/2024

Mu sanya lura game da duk wani tafarkin da za mu bi, sannan mu yi masa alqalanci da Kitabu da Sunnah.

© Al'ansar

Address

Dorayi Chiranchi Kano, Imamul-fasihiy's Home. No: 703 (08132076078)
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Al'ansar Islamic Movement posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share