13/07/2025
SHI YA KIRKIRI ABINDA BABU YA SANYA A NASSIN,
Ga yadda Hadisin yake, yazo a Sahihul Bukhari kan lamba ta 2788, Muslim kuma a lamba ta 1912
Sayyadina Anas Bin Malik (R.T.A) ya ruwaito cewa:
كان رسول الله ﷺ يدخل على ام حرام بنت ملحان، فتطعمه، وكانت تحت عبادة بن الصامت، فدخل عليها رسول الله ﷺ فاطعمتْه، ثم جعلت تفلي رأسه، فنام، ثم استيقظ وهو يضحك، فقالت: ما يضحكك يا رسول الله؟ قال: ناس من امتي عرضوا عليّ غزاة في سبيل الله، يركبون ثبج هذا البحر ملوكا على الاسرّة، او مثل الملوك على الاسرّة. قالت: يا رسول الله، ادع الله ان يجعلني منهم، فدعا لها، ثم وضع رأسه ثم استيقظ وهو يضحك، فسألته، فقال مثل مقالته، فقالت: ادع الله ان يجعلني منهم، فقال: انت من الاولين.
MA'ANA:
MANZON ALLAH ﷺ yana ziyartar Ummu Haram bint Milhan (RA), tana gabatar masa da abinci. Tana auren Ubada bn al-Samit (RA). Wata rana, MANZON ALLAH ﷺ ya ziyarce ta, ta bashi abinci, sannan ta fara taje masa gashi. Sai ya yi barci, daga baya ya farka yana dariya. Ta ce: "YA MANZON ALLAH, me ya sa kake dariya?" Sai ya ce: "Na ga wasu mutane daga cikin al’ummata suna tafiya a saman teku (ruwa) suna yin jihadi a kan tafarkin ALLAH, kamar sarakuna a kan gadon sarauta."
Ta ce: "Ya Manzon Allah, ka roƙi Allah ya sa in kasance cikin su." Sai ya yi mata addu’a. Sai ya sake kwanciya, daga baya ya farka yana dariya. Ta sake tambayarsa, sai ya ce daidai da yadda ya fada a baya. Ta ce: "Ka roƙi Allah ya sanya in kasance cikin su." Sai ya ce: "Ke cikin farkon su k**e."
ABIN LURA:
Sunan kwarkwata a larabci shi ne الجراد a cikin lafazin hadisin baki dayansa babu inda hakan yazo, sannan kuma babu inda komin gwarancin bagware zai fassara taje gashi da sunan ana cire kwarkwata, jingina hakan ga MANZON ALLAH (S.A.W) kuma su'ul adabne.
BA ANNABI (S.A.W) ba, ko iyalan gidansa ALLAH ya tsarkakesu daga dukkanin abin kazanta kamar yadda yazo cikin fadin ALLAH
إنما يريد الله ليذهب عنكم الرجس أهل البيت ويطهركم تطهيرا
KWARKWATA ALAMACE TA KAZANTA, DUK WANDA AKA JINGINAWA ITA AN JINGINA MASA MUMMUNAR SIFFA, ALLAH KUMA DA KANSA YAKE FADI YA TSARKAKE AHLIN GIDAN ANNABTA DAGA KOWACCE IRIN KAZANTA.
SABODA HAKA, KADA A RUDI MUTANE, BABU INDA WANNAN LAFAZIN YAZO A CIKIN NASSI, FACE SHI WANNAN BAWA MARA NEMAN ALBARKA SHINE YA KIRKIRI ABINSA YA JINGINAWA MANZON ALLAH (S.A.W).
YA YARDA KUSKURE YAYI YA FITO YA GYARA KUMA YA JANYE KO KUMA GOMNATI TA DAUKI MATAKIN HUKUNCI A KANSA, IRIN YADDA AKA DAUKA A KAN MAGABACINSA A IRIN WANNAN LAYIN, DAN GUDUN KADA YA ZAMO SILAR TAYAR DA TARZOMA.
ALLAH YA SHIRYA.
ALHAMDULILLAH.