24/02/2020
-ZAMAN SAYYIDA FATIMA (AS) A GIDAN MIJI SAMFUR NE GA MA'AURATA.
-Sayyida Fatima (as) ta rayu tare da Mijinta Imam Ali (as) rayuwa dayyiba, Wacce take dauke da dubban darusa ga maโaurata a zamantakewar aure.
-Alal Misali Yazo a kan cewa Imam Ali (as) Yana cewa; โTun da Muke da Fatima ba ta taba bata Min rai ko ta Saba min a Wani alโamari ba.
-Imam Ali (as) Yace: "Na kasance idan dube ta duk bakin ciki da damuwa da Yake tattare da ni Yakan gushe, Kuma Wallahi tun da Muke da ita ban taba bata Mata ta rai ba, ko in tilasta ta a kan Wani alโamari ba, har Allah (T) Ya amshe ta.โ
-Haka Nan Sayyida Fatima (as) a Cikin Wasiyyar da ta Yiwa Imam Ali (as) take tambayarsa cewa: โShin Tun da Muke da kai na taba saba Maka?.โ Sai Imam Ali (as) Yace A'a, Sai Sayyada Fatima ta ce Masa, Allah ta'ala Ya Saka Maka da Alkhairi.
-Bari Na kawo Mana Wata Kissa don Mu dauki darussa a cikinta: "Wata Rana Imam Ali (as) Ya Wayi gari Yana jin Yunwa, Sai Yace; โYa Fatima (as)! Akwai Wani abu a Wajenki na abinci?โ Sai ta ce; โAโa, Ina ranstuwa da Wanda Ya girmama Babana da Annabta, Ya kuma girmama ka da Wasicci, ba abin da na Wayi gari da shi na abinci.โ
-Sai Sayyada Fatima tace: โBabu wani abinci gare mu tun kwanaki biyu da S**a gabata, face abin da na 'Dan fifita ka da shi a kaina da Kuma Wadannan โYaโyan Namu, Hasan da Husain (as).โ
-Sai Imam Ali (as) Yace: Mata; โYa Fatima (as)! Me ya sa ba ki Sanar dani ba domin in nemo wani abu?โ Sai Sayyada tace: โYa Baban Hassan! Ina Jin kunyar Ubangijina in Kallafa Maka abin da ba ka da iko da shi.โ
Ya Allah! Ya Allah!! Ya Allah!!!
-To 'Yan uwa Mata kun dai ji Yadda Sayyada Zahra (as) ta rayu Cikin tausayi da Jinkan Mijinta.
-Sayyida Fatima (as) ta Kasance tana lura da alโamuran gidanta kuma tana aiwatar da bukatun gidan bisa dogaro da kokarinta, Saboda ita bata kasance tana dogaro da Masu hidima ko bayi ko โyan aiki ba, duk rayuwarta ta kasance jihadi ne da kokari.
-Sayyada Fatima (as) ta Kasance tana nika, ta yi amfani da dutsen nika da