Taskar Daliban Ilimi

Taskar Daliban Ilimi Alhamdulillah, wannan Ƙungiya ce wadda take yaɗa tunatarwa, wa'azantarwa, Faɗakarwa da Nasihohi.

19/01/2026

A kullum, ilimi shine gaba da komai. Karatu da ilimi sune su ke buɗe tunani da zuciya da kawo mafita; sune su ke haska rayuwa. Kuma, duk wanda ya yi su da gaske da kyakkyawar zuciya, sai ya zama mai amfani da amfanarwa.

A duk hirar da za'a yi, ka da ka taɓa yarda a ce maka karatu da ilimi abin banza ne, saboda ka ga wasu basu yi karatu ko ilimi ba amma suna samun abin duniya da dukiya - wannan ba ma'auni bane, saboda kowa na iya samu, mai ilimi da mara ilimi.

Karatu da ilimi wasu fasaha ne da suke saita rayuwarka kuma suke riko da kai wurin yanda za ka na inganta al'ummaranka da cimma abubuwa cikin hankali da basira da sauki.

Ba shakka, ba lallai ne ilimi da karatu su baka kuɗi irin na masu kuɗi ba, amma za su iya kareka daga wauta da ganganci irin na wasu masu kuɗin. Kuma, matukar kanada ilimi kuma ka kiyaye ilimi kuma kayi amfani da shi, zai taimakeka.

Matsalar a yau ita ce, wasu da yawa ba su tsayawa su yi karatu da kyau da gaske. An ɗauka sunan nan anje makaranta ko an samu takardan shaidar karatu shine, an samu karatu da ilimi. A karshe, tunda babu ilimin da gaske kuma ba a ga amfaninsa da kyau ba, sai su zaci rayuwarsu na makaranta abar banza ne kawai - kuma laifinsu ne.

A zahiri, ko wadanda ba su karatu da neman ilimi da muke gani suna samun kuɗi, za mu ga ba da wasa suke yin abubuwan da suke yi ba. Don menene za mu yi zaton in bamu yi karatu da kyau ba za mu samu amfani da cin moriyar ilimi? Dole sai mun rike abinda muke yi da kyau da gaske, kafin mu ga amfaninsa.

Karatu da ilimi ba abin banza ba ne, kuma duk wanda ya yi su da kyau, ba zai taɓa wulakanta ba - ko an so a wulakantar da shi. Don haka, mu dage. In zamu yi karatu, mu yi da kyau. Muna iya samun kuɗi k**ar jahilin da bai yi karatu ba, amma jahili ba zai taɓa zama mai ilimi ba - sai ya yi karatun da mu ka yi.

BIN ISAH. 2025.

16/01/2026

MUSULINCI HANYAR RAYUWA

Musulinci addini ne, amma bayan kasancewarsa addini, hanyar rayuwa ne. Shi yasa babu wani motsi ko wani abu da za ka yi a matsayinka na musulmi face sai ka ji musulinci yana da magana akanka gameda wannan abin.

Misali:

A musulinci ne kawai bayan ka samu dukiya mai yawan gaske, kuma bahaushe yace wai dukiya yaren mai ita take ji, to amma musulinci zai maka iko da wannan dukiyar, ya kafa maka sharuɗɗa guda biyar:

1. WAJIBI: Musulinci zai ce maka wajibi ne ka kashe wani yanki na kuɗinka akan wani aiki. Misali: Zakkah. Kuma Zakkar nan, musulincin ne dai zai faɗa maka irin mutanen da za ka bawa Zakkar.

Sauran misalan wajibci ya haɗa da biyan bashin da ake binka, kula da kanka da sauran waɗanda haƙƙinsu ke wuyanka. Duk wannan wajibi ne ka kashe dukiyar akansu. Wato dole ne. Idan ba ka yi ba, Allah Yana jiran zuwanka lahira. Za ka gane kurenka.

2. MUSTAHABBI: Musulinci zai ce maka akwai wasu abubuwa da yake kwaɗaitar da kai yinsu, bayan ka gama kashe dukiyar da ta zama maka wajibi ka kashe. Sai musulinci yace akwai waɗansu ayyuka masu kyau waɗanda idan ka yi su, za ka samu lada wajen Allah in har ka tsarkake niyyarka. Misali: gina masallaci, makarantu, asibitoci, rijiya, taimakon marayu, bada sadaqa kawai ga masu rauni (banda zakkah), biyawa yaran talakawa kuɗin makaranta ko magani.

Duk waɗannan ayyuka ne na lada. Idan ka yi su, ka samu kada. Wasunsu ma falala ce sosai za ka samu a lahira, k**ar gina masallaci da taimakon marayu. Waɗannan za su maida kai wani special mutum ne a cikin Al-Jannah ma. Wasunsu albarka suke ƙarawa cikin dukiyarka da rayuwarka. To abin nufi dai: waɗannan ayyuka idan ka yi, Allah zai baka lada. Idan ka ƙi yi, babu komai; yi zamanka babu lada babu zunubi.

3. MAKRUHI: Akwai waɗansu abubuwa waɗanda Musulinci zai ƙyamaci ka kashe dukiyarka ta hanyarsu, amma ba zai k**a ka da lefi ba don ka kashe kuɗin naka ta hanyar. Don haka, idan ka karɓi ƙyamar ka ƙi kashewa, to sai ka samu lada. Amma idan ka kashe kuɗin naka ta hanyarsu duk da cewa musulinci yana ƙyamar hakan, to ba ka yi lefi ba. Ma’ana, babu zunubi.

Galibi irin wannan ya fi zuwa ne ta fuskar israfi da almubazzaranci. Wato ɓarnar dukiya. Ka kashe dukiyarka akan waɗansu abubuwa waɗanda babu wani buƙata, kuma babu wani amfani da zai dawo maka ko da ta hanyar morewa rayuwa ne. Kawai ka kashe kuɗi a banza saboda ka ga kana da kuɗi, alhali akwai wasu hanyoyin da idan ka kashe kuɗin, to ko dai ka samu lada, ko kuma ka more rayuwa.

Misali: ka san cewa plate ɗaya na abinci za ka iya ci a restaurant, amma sai ka yi order na plate har biyar kawai saboda nuna isa! Ka jagwalgwala duk abincin, ka tashi ka bari. Ƙarshe kawai a zubar. Wannan ka yi makaruhi. Haka zalika, ka ɗauki dukiyarka ka biya kuɗin silma don ka kalli wani shirin film, ko wasan ƙwallo. Haka kuma ɗiban maƙudan kuɗaɗe kawai ka bawa ƴan kwallo. Wannan duk tafiyarsu ɗaya, suna wannan babi.

4. HALAL: Akwai waɗansu abubuwa waɗanda idan ka kashe kuɗinka akansu, to babu yabo, babu fallasa. Wato, musulinci ba addini bane na takura da ƙetare iyaka wajen gudun duniya. Musulinci ya baka dama ka kashe kuɗinka domin samarwa kanka abubuwa na jin daɗi.

Misalai a nan: ka ci abinci mai kyau, mai gina jiki (balanced diet). Ka ɗinka kaya masu kyau (Getzner ma kuwa idan kana da hali). Ka gina gida mai kyau, ka zuba A/C ko’ina. Ka siya tikitin jirgi ka je yawon buɗe ido duniya, don ganin abubuwan ban mamaki. Waɗannan duk lafiya lau. Musulinci bai hana ka ba. Ka more rayuwarka cikin abubuwan da s**a halasta. Amfaninka ne, ko amfanin waninka. Wannan yayi.

5. HARAM: Akwai kuma waɗansu abubuwa waɗanda musulinci ya ja maka layi, ya hana ka. Ba ka isa ka yi su ba. Idan ka yi su, to lallai za ka gamu da fushin Wanda ya baka dukiyar, wato Allah. Har abada kada ka kuskura ka sanya ko sisi na dukiyarka cikin waɗannan harkokin.

Misalai a nan: Cin hanci, Rashawa, Riba (Intetest), C**a (su BetNaija, Gambling dai), ayyuka na shari’a ta haramta irin: shan giya, biyan karuwa don yin zina da ita, taimakawa azzalumai, kasuwancin giya ko aladu dss. Waɗannan duk musulinci ya hana ka zuba dukiyarka ciki. Idan kuma ka zuba, to Allah zai maka azaba ko dai tun daga nan duniya ya kwashe albarkar dukiyarka, ko kuma a lahira ya maka azaba da wuta, ko kuma ya haɗa maka biyun.

To shi yasa Musulinci bashi da kishiya. Duk wani addini da ka sani, ba kishiyar musulinci bane. Domin shi musulinci ba wai zallar addini bane mai nuna maka ibada, a’a. Baccin kasancewarsa addini, to hanyar rayuwa ne. Musulinci yana da abin cewa akan duk wani motsinka a duniyar nan.

Allah Ubangiji Ya sa mu dace.

✍️ Ibrahiym. A. El-Caleel
[email protected]

19/12/2025

Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Addu'a uku karɓaɓɓu ne, babu ƙoƙwanto acikin su: Addu'ar mahaifi ko mahaifiya, Addu'ar matafiyi, Addu'ar wanda aka zalunta.” [Albaniy ya inganta shi cikin sahihu Abu-dawud: 1536]

©️ Nusaiba Tasiu Abdulrahim

03/12/2025

kuyi raka'oi biyu na raka'atanal fajr kamin sallan asuba, sunfi duniya da abinda ke cikinta Alkhairi.

Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya kasance yana karanta: Suratul khafirun da Suratul Ikhlas a raka'oi biyu na raka'atanal fajr.

Jiddart Yusuf.

20/09/2025

Ga Ɗalibai na Ilimin Addini, A karatun addini, babu 'shortcut' na zama mai ilimi ko Malami, ta yanda za ka yi wasu dabarbaru cikin shekara ɗaya ko wani kankanin lokaci kawai sai ka zama mai ilimi ko Malami daidai da Malamin da ya shekara ashirin ko talatin ko arba'in yana karatu da karantarwa.

1. A gaskiya, shi kansa wannan tunani da yunkuri alama ce ta rauni da lalacewar al'amarin mai son neman ilimi. Babban abu na farko da zamu fahimta shine, shi التأهيل للتعليم الشرعي - samun cancanta na zama Malami mai koyar da ilimi na Sharia, sai ka samu التأصيل العلمي - kafuwa na ilimi, ma'ana sai ka samu tushe na rikewa da zai rike abinda kake koya na ilimi - k**ar jijiya ga bishiya. Ka yi tunani yaya jijiyan bishiya yake samuwa har yayi karfi.

A bayan samun tushe mai karfi ta hanyan koyon صغائر العلوم - ilimomi kananu da suke haifar maka da alaqa tsakaninka da kananun abubuwa na ilimi, da wannan ka ke fara ginuwa zuwa ga samun manyan ilimai. Kuma, da lokaci mai tsawo ake wannan! Sannan, shi wannan lokaci da kake ɗauka kana karatu shine babban hanyan samun ilimin ba abinda kake koya ba zalla; a waɗannan lokuta na koyo kake ginuwa a tunani da riskar abu kuma kake gane abubuwa da fahimtarsu.

2. Haka nan, k**ar yanda kowa ya sani, daga kananun ilimi ake tafiya zuwa ga manyan ilimomi - كبائر العلوم . Sannan, ba tafiya bace ta الإنتقال المباشر - wato, tashi na kai-tsaye a lokaci guda. A'a, الإنتقال التدرجي - tashi ne mai mataki-mataki a cikin lokuta masu tsayyi. A duk gaɓa, mutum daɗa ginuwa yake yi ta yanda kokarin gaggawa wurin wucewa kan iya haifar wa mutum asara na ilimi da fahimta da gogewa.

A nan, babban abu da zamu daɗa fahimta shine, su waɗannan صغائر العلوم da كبائر العلوم abubuwa masu surori k**ar haka:

صغائر العلوم = الفروع، الجزئيات، الأدوات
Ilimomi da suke na rassa da sassa da kayan aiki na fahimta da nazari cikin abinda ake koyo ko karantawa. Abinda mu ke iya kira da ilimomi na kasa.
كبائر العلوم= الكليات، المبادئ، القواعد العامة
Manyan ilimai na bayanan hukunci masu gamewa da tushe na asalin sako da ka'idadoji masu gamewa. Abinda muke kira da ilimomi na sama.

3. A nan, bisa tsarin koyo, daga "kasa" ake tafiya zuwa "sama", ma'ana daga rassa ake isa zuwa ga tushe, ta yanda duk wanda bai koyi rassa ba ba zai samu isa zuwa ga tushe ba. Kuma da samun tushe ake zama Malami ba da rassa ba - amma kuma, dole sai an samu rassa.

Bisa wannan ne, aka samu zance na azanci da ake wa ɗalibai na ilimi:
من حرم الأصول حرم الوصول
"Duk wanda bai samu usul na ilimi ba, ba zai samu isa zuwa ga ilimi ba." A nan, rashin samun الأصول usul ɗin yana faruwa ne da rashin samun الفروع waɗanda suke kai mutum zuwa ga usul ɗin. Wanda kuma ya rasa usul ba zai kai zuwa yanda ake so ba. A nan, ana iya fassara wannan zance haka:
من حرم الفروع حرم الأصول حرم الحصول
"Duk wanda bai samu sassa na ilimi ba, ba zai iya samu tushen ilimi ba, kuma ba zai samu ilimi ba."

4. A bisa wannan, za mu ga shi yasa ake fara koyon kananun littafai kafin a fara koyon manya a kowani babi. A babin النحو ko الصرف ko البلاغة ko الإنشاء ko الإملاء, duk sai a duba wasu kananun littafai masu sauki, sai a fara da su. A hankali, daga kananu masu saukin sako da bayani, sai a tafi manya masu dunkulallen sako da bayani - wanda sai anyi sharhi ga mutum.

A bangaren القرآن a tajwidinsa da tafsirinsa da qira'arsa, daga haka ake farawa. Haka nan, a babin الحديث a mustalahunsa da littafansa da aka rubutasu, daga kanana zuwa manya. Haka nan, a babin العقيدة sai a fara da littafan tauhidi masu sauki wurin bayanin waye Allah SWT zuwa masu girma suke dunkele bayanai wadanda ake cire hukunci daga cikinsu. Haka, a الفقه a usul din da qawaid ɗinsa. Da sauransu.

5. A dukkan hanyar nan, za mu lura kowani bangaren ilimi da ake koya yanada kananu da manyan bangarori - kuma ba a fahimta ilimi na sama sai an fahimci na kasa. Kuma, da lokaci ake amfani kuma lokaci mai tsayyi. Tabbas, ya k**ata mutum yayi mamaki ace kawai zai samu ilimi a kankanin lokaci kuma ya fahimci yanda zai yi amfani da ilimin wurin gina fahimtar mas'aloli da gina hukunci akan mas'aloli. Saboda, ba kawai zallar karanta littafi ko haddaceshi ba, kana bukatar sanin wurin amfani da ajiye karatun, da haɗa alaqa tsakaninsa da yanuwansa.

A duk wannan tafiya, batu ne na البناء العلمي - samun ginuwa na ilimi da yake kaiwa zuwa ga التأصيل العلمي - samun kafuwa a ilimi wanda ya ke kaiwa zuwa ga التحصيل العلمي - samun ilimi wanda ya kaiwa zuwa ga التأهيل للتعليم الشرعي - cancanta a wurin koyar da ilimi na Shari'a, saboda, yanzu mutum ya samu matsayin shiga cikin martabar mutane da ake kiransu أهل العلم ma'abota ilimi wadanda s**a cancanta a kirasu da العلماء - Malamai na Addini.

6. A nan, muna iya tuna, abinda mai littafin تعليم المتعلم طريق التعلم ya ambata na abubuwan da duk mai neman ilimi zai kudurcesu a yayinda ya saka aniyar neman ilimi:

ألا لا تنال العلم إلا بستة
سأنليك عن مجموعها ببيان

ذكاء وحرص واصطبار وبلغة
وصحبة أستاذ وطول زمان

A dunkule sune: Kokarin fahimta. Kwadayin ilimi mai karfi. Juriya da hakuri na gaske. Guzarin hanya. Zama da koyo a wurin Malami. Ɗaukar tsawon lokaci ana koyo. Daukar lokaci ana koyo, ba kokarin neman ilimi a kankanin lokaci ba.

A babin nan, zamu tuna zance da ke ambatawa don ishara zuwa ga ilimi baki baya samuwa a lokaci guda. Suna cewa:
من جمع العلم جملة فاته جملة
"Wanda ya nemi tara ilimi gaba-ɗaya a lokaci guda, haka ilimin zai rabu da shi gaba-ɗaya a lokaci guda." Yana tara ilimi, ilimin yana tafiya, yana rabuwa da shi. Saboda, ilimi ginuwa yake yi, da haka ya ke taruwa; ba wai a gine kawai yake ba, ana samunsa sai ya zauna.

7. Haka nan, Malam mai Ta'alimu ya nuna mana babban abu a wurin النية في طلب العلم - kulla niyya a wurin neman ilimi shi ne:
وينبغي أن ينوي المتعلم بطلب العلم رضاء الله والدار الآخرة وإزالة الجهل عن نفسه وعن سائر الجهال
"Sannan, mai neman ilimi a yayin neman iliminsa ya k**ata ne ya yi niyya: neman Yardar Allah da Gidan Lahira, kuma don ya gusar wa kansa da jahilci sannan da ma sauran wadanda basu da ilimi..."

A asali, mutum yana neman ilimi ne don neman Yardan Allah da Rabon Lahira, kuma ya samu ilimi akan abinda ya jahilta, sannan sai yayi amfani da iliminsa wurin ilimantar da sauran wadanda basu da ilimi. Ilimi ba ana fara nema don a zama Malami bane. Sannan, ba abu ne na son burge wani da mutum zai ce yinsa a kankanin lokaci shine abinda zai saka a ji sa ko a gansa ko ace ya yi karatu har yana karantarwa.

8. A fahimta, ba laifi bane don mutum ya koyi ilimi don ya karantar da mutane - hasalima, wannan yana daga cikin مقاصد طلب العلم - makasudin neman ilimi, a samu ilimi kuma a karantar da mutane. Hasalima, wanda ya yi ilimi kuma ya ɓoye ilimi, abinda ake kira da كتمان العلم ya zama ba ya karantar da jama'a, wannan ilimi nasa zai zama abin azaba garesa a Ranar Lahira. Amma, son karantarwa ba ya nufin العجلة في طلب العلم وجمعه - gaggawa a neman ilimi da tarashi.

A takaice, yana da kyau, mu fahimci, samun ilimi yana bukatar lokaci mai tsayyi. Sannan, ga dukkan mai son karatu don ya karantar da al'umma, batun sanya lokaci wa neman ilimi ba nasa bane. Neman ilimi a wurinsa har abada ne, har ranar da zai bar duniya. Malamai suna cewa:
إن صناعتنا هذه من المهد الى اللحد
"Ita wannan sana'a tamu daga zanin goyo ne har zuwa cikin ramin kabari."

Don haka, mai neman ilimi na addini, kuma da niyyar karantarwa da zama Malami na Addini, bayada lokacin da zai bar karatu da neman ilimi, kuma da wannan kokarin karatu da karin neman ilimi yake kara wa kansa النضوج في العلم - nuna a ilimi da kuma الرسوخ في العلم - tabbatuwa cikin ilimi - abubuwa da suke haifar wa mutum fahimta na gaske da hukunci na gaske a cikin mas'aloli na ilimi da ilimantar da al'umma da ake bukatar shiryarwa zuwa ga kyakkyawar rayuwa a Gidan Duniya da Gidan Lahira.

Allah SWT ya datar damu.

BIN ISAH. 2025.

Idan mutum baya son wani ko kuma baya ƙaunar wani, ba a kallon haka a matsayin wani abu na yancin kai ko zuciya kaɗai, s...
10/08/2025

Idan mutum baya son wani ko kuma baya ƙaunar wani, ba a kallon haka a matsayin wani abu na yancin kai ko zuciya kaɗai, sai dai a duba ta fuskar addini. A Musulunci ƙin mutum ba tare da dalilin shari'a ba, zalunci ne, ƙetare haddi ne. Idan aka samu saɓani tsakanin mutane, addini ya koyar da a gyara zuciya, a nemi sulhu, a yafe wa juna. Ƙaunar mutum saboda Allah da kuma ƙin sa saboda Allah, shi ne abin da ake so, k**ar dai idan aka ƙi mutum, to a ƙi shi saboda aikinsa na saɓo ko rashin bin umarnin Allah, ba don halittarsa ko asalinsa ba.

Idan mutum baya son wani, hanyoyin da Sahabbai ke bi sun haɗa da gyaran zuciyarsu ta hanyar yin sulhu, kuma "Ba ya halatta ga musulmi ya ƙi ɗan uwansa sama da kwanaki uku... Bukhari da Muslim". Ko da mutum baya son wani, hakan ba shi ne zai hana ya yi masa adalci a magana ko mu'amala ba. Sahabbai suna yi wa wanda su ke da saɓani da shi addu'a, suna neman Allah Ta'ala ya shiryar da shi. Haka kuma suna guje wa yin gulma ko cin mutuncin mutum a bayansa. Abin da ba a yarda da shi ba, ƙin mutum saboda ƙabilarsa, asalinsa, halittarsa, talaucinsa ko wani abu na son zuciya. Ƙarancin sani ne ke sabbaba haka an kuma yi gargaɗi sosai a kansa, kuma ba a yarda a riƙe ƙiyayyar har ta hana haɗin kai cikin al'amuran jama'a ba.

A wannan aya ta 9 cikin suratul Hujurat, Allah Ta'ala ya sanar da muminai yadda ya k**ata su yi sulhu idan jama'a biyu daga cikinsu s**a yi rikici ko saɓani. Ya umarce su da su sasanta bisa hukunci da shari'ar Allah a kan abin da su ke da saɓani a kai. Idan kuwa ɗaya daga cikin ɓangarorin ta ƙi amincewa da sulhu, ta cigaba da yin zalunci ko ta'addanci a kan ɗayar, Allah Ta'ala ya ba wa muminai izinin yaƙar ɓangaren nan mai zalunci, har sai ta koma ta yarda da hukuncin Allah. Idan kuma sun dawo s**a amince da hukuncin Allah, sai a yi musu sulhu cikin adalci. Allah Ta'ala kuma ya umarci muminai da su tabbatar da gaskiya da adalci a cikin hukuncinsu, domin lalle Allah yana son masu adalci cikin hukuncinsu. Allah Ubangiji Ta'ala ya sa mu dace, ya shiryar da mu.

Ibrahim Abdu Hamza.

31/07/2025

A Suratu Yusuf, a kullum, ka ke tafiya cikin Surar nan, sai kaga wasu hanyoyin Allah na musamman, na yanda Allah SWT yake gudanar da al'amuran halitta da bayi.

1. A farkon surar nan, an buɗe ne da batun Mafarkin Annabi Yusuf:
{ إِذۡ قَالَ یُوسُفُ لِأَبِیهِ یَـٰۤأَبَتِ إِنِّی رَأَیۡتُ أَحَدَ عَشَرَ كَوۡكَبࣰا وَٱلشَّمۡسَ وَٱلۡقَمَرَ رَأَیۡتُهُمۡ لِی سَـٰجِدِینَ }
"Ka tuna lokacin da Yusufu yace da babansa: "Ya Babana, lallai nayi mafarkin taurari goma sha ɗaya da rana da wata, na gansu suna yi mini sujada."
[Surah Yūsuf: 4]

Bisa abinda Annabi Yusuf ya ambata, sai babansa Annabi Yakubu yace:
{ وَكَذَ ٰ⁠لِكَ یَجۡتَبِیكَ رَبُّكَ وَیُعَلِّمُكَ مِن تَأۡوِیلِ ٱلۡأَحَادِیثِ وَیُتِمُّ نِعۡمَتَهُۥ عَلَیۡكَ وَعَلَىٰۤ ءَالِ یَعۡقُوبَ كَمَاۤ أَتَمَّهَا عَلَىٰۤ أَبَوَیۡكَ مِن قَبۡلُ إِبۡرَ ٰ⁠هِیمَ وَإِسۡحَـٰقَۚ إِنَّ رَبَّكَ عَلِیمٌ حَكِیمࣱ }
"Kamar haka ne Ubangijinka zai zaɓeka, ya kuma sanar da kai wani abu daga fassarar mafarki, Ya kuma cika ni'imarsa a gare ka da kuma iyalan Yakubu k**ar yanda tuntuni ya cikata ga iyayenka Ibrahim da Ishaqa, lallai Ubangijinka Masani ne Mai hikima."
[Surah Yūsuf: 6]

Amma yaya wannan mafarkin zai tabbata ko yaya zai faru? Annabi Yusuf bai sani ba, kuma, mahaifinsa ma bai sani ba. Annabi Yakubu ya fahimci mafarki ne mai girma.

A cikin farin ciki, Annabi Yakubu har yayi bayani ga Annabi Yusuf na abinda ya fahimta daga mafarkin nasa cewa, zaɓi ne ya samu na Allah kuma zai samu ilimin fassarar mafarki da ni'ima. Amma Annabi Yakubu bai san cewa, sai ya rasa Annabi Yusuf ba, kuma sai ya shiga damuwa - sai an haɗu da jarabawa.

2. A har yanzu, Annabi Yakubu da yake bayanin kunshin mafarkin nan na falala da Annabi Yusuf zai samu, amma bai iya tsinkayar ita batun mafarkin na zahiri da Annabi Yusuf ya ambata ba, na cewa, "Naga taurari goma sha biyu da rana da wata, na gansu su na mini sujada". Annabi Yakubu bai san me ake nufi a wurin ba.

Tun daga wannan mafarki, Annabi Yusuf ya fara shiga hanyar tabbatuwarta, amma shi ma bai sani ba, kuma Babansa ma bai sani ba. Al'amura daga wannan sai wancan, daga wannan jarabawa sai wancan. Annabi Yusuf bai san cewa, wancan mafarki tanada hanya ba.

3. A karshe, bayan komai ya faru, tun daga Annabi Yusuf da yanuwansa, da rabuwarsa da mahafinsa, da zaman kurkuku da halin damuwa na Annabi Yakub ya shiga, da fitinar gidan Sarki. A karshe, ita mafarkin babba ta zo ta faru - ita ma k**ar a mafarki. Allah SWT yace:

{ فَلَمَّا دَخَلُوا۟ عَلَىٰ یُوسُفَ ءَاوَىٰۤ إِلَیۡهِ أَبَوَیۡهِ وَقَالَ ٱدۡخُلُوا۟ مِصۡرَ إِن شَاۤءَ ٱللَّهُ ءَامِنِینَ }
"Lokacinda s**a shiga wurin Yusufu, sai ya jawo iyayensa kuma yace: "Ku shigo Masar yanda Allah ya ga dama kuna amintattu."
Surah Yūsuf: 99

{ وَرَفَعَ أَبَوَیۡهِ عَلَى ٱلۡعَرۡشِ وَخَرُّوا۟ لَهُۥ سُجَّدࣰاۖ وَقَالَ یَـٰۤأَبَتِ هَـٰذَا تَأۡوِیلُ رُءۡیَـٰیَ مِن قَبۡلُ قَدۡ جَعَلَهَا رَبِّی حَقࣰّاۖ وَقَدۡ أَحۡسَنَ بِیۤ إِذۡ أَخۡرَجَنِی مِنَ ٱلسِّجۡنِ وَجَاۤءَ بِكُم مِّنَ ٱلۡبَدۡوِ مِنۢ بَعۡدِ أَن نَّزَغَ ٱلشَّیۡطَـٰنُ بَیۡنِی وَبَیۡنَ إِخۡوَتِیۤۚ إِنَّ رَبِّی لَطِیفࣱ لِّمَا یَشَاۤءُۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡعَلِیمُ ٱلۡحَكِیمُ }
"Sai ya kuma dora mahaifansa akan gadon mulki, kuma s**a faɗi suna masu gaisuwa a gare shi, kuma yace: Ya Babanmu, wannan shine fassarar mafarkina na tun tuni. Lallai Ubangijina ya mayar da shi gaskiya; hakuka kuma ya kyautata min lokacin da ya fitar da ni daga kurkuku, Ya kuma zo da ku daga ƙauye bayan Shaiɗan ya shiga tsakanina da Yanuwana. Lallai Ubangijina mai tausasawa ne ga wanda ya ga dama. Lallai Shi ne masani mai hikima."
Surah Yūsuf: 100

4. Haka nan, mu lura da wani abu mai muhimmanci. A karshen zancen Annabi Yakubu ga Annabi Yusuf a farkon al'marin, yace masa:
إن ربك عليم حكيم
"Lallai Ubangijinka masani ne, mai hikima."

A haka, shi ma Annabi Yusuf, a karshen zancensa ga mahaifinsa a karshen al'amari, yace masa:
إنه هو العليم الحكيم
"Lallai Allah Shi ne masani mai hikima."

A karshen Surar nan, za mu ga haduwar farkonta da karshenta. Abinda Annabi Yusuf bai sani ba dangane da mafarkinsa, a yanzu ta zo ta bayyana a fili, kuma Babansa Annabi Yakubu shi ma ya gani a zahiri. Amma shin sun san za'a zo nan a farko? Basu sani ba. Annabi Yusuf yayi fama, haka ma, Babansa yayi fama, amma duka akan hanya na isa zuwa ga wani al'amari da Allah SWT ya nuna musu farkonsa mai cike da kyau da farin ciki.

A tsarin Allah SWT a matsayinsa na Masani kuma Mai hikima, za ka ga abubuwa amma Allah SWT shine masanin hakikaninsu - don haka, kayi imani da Shi kuma ka rike Shi. Ta yiyu abubuwa su zo maka a sura na rashin jin daɗi da wahala a farko, amma a karshe bayan zamani mai tsawo, su zama maka abin farin ciki da alheri na karshe. Haka nan, ta yiyu ka yi nasarar cimma wani mummunan aiki kuma ka yi murna da farin ciki a farko, amma a karshe, wannan mummunan aiki ya zama maka nadama da bakin ciki - k**ar yanuwan Annabi Yusuf da yanda a karshe abu ya faru. Annabi Yusuf ya samu daraja akansu bayan duk abinda s**a yi.

A karshe, bayan yawo cikin nauyin sakkonnin Qurani, kuma, za ka kara tabbatar da cewa: Quran ba tsarin zance ne na Dan Adam ba, don ba a tsarin zubin Dan Adam yake tafiya ba.

Allah SWT ya cika rayuwarmu da Hasken Qurani.

Bin Isah. 2025.

31/07/2025

Duk yadda rayuwa ta ke, ya zama dole ka yi ƙoƙari ka gano maƙasudin halittarka, hakan na buƙatar neman ilimi daga fannoni daban-daban na rayuwarka, domin kai wa ga fahimtar manufar da Allah Ta'ala ya halicce ka domin ta. Duk wani abu da zai hana ka aiwatar da abin da ya zama wajibi gare ka, to ya dace ka yi masa tsari ko ka bar shi gaba ɗaya.

Domin wajibi na da daraja fiye da komai, kuma babu abin da ya k**ata ya fi shi muhimmanci a gare ka. Wasa na halak su ne waɗanda shari'a ta amince da su, ba kowanne irin wasa ba ne halal musamman ga Musulmi. Akwai hujjoji bayyanannu da ke nuna Allah Ta'ala bai yi halittar mutum da aljanu ba sai domin su bauta masa. Don haka lokaci mai matuƙar muhimmanci ne a gare ka, ya dace ka riƙa amfani da shi wajen neman ilimi da abubuwan da za su taimake ka wajen bautar Allah.

23/07/2025

Duk wani halin koyi da nagarta suna a rayuwar Manzon Allah SAW, ya ishe wa kowa abin koyi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi. Allah Ubangiji Ta'ala ka taimake mu wajen fahimta da koyi da shi tare da biyayya ga dukkan abin ya zo mana da shi na umarni da hani.

Ibrahim Abdu Hamza.

23/07/2025

Son zuciya zalunci ne, wanda ke jawo nadama mara amfani, hali ne da mutum ke sanya kansa, sannan ya aikata abin da ya zuciyarsa ta so ta hanyar saɓawa gaskiya, adalci da kuma dokoki don cimma wasu buƙatu ko manufa.

Son zuciya masifa ce da mutane ke faɗawa cikinta, don samun biyan buƙatunsu ta hanyar bijire wa gaskiya ko dokokin da aka shimfiɗa gare su. Sau da yawa a dalilin son zuciyar mutum ɗaya na iya zama sanadin rushewar wasu da dama.

Son zuciya sanadi ne da ke halaƙar da wasu a nan duniya, son zuciya ke sa wasu sayar da lahirarsu akan duniyar su, son zuciya ke sa wasu halakar da wasu ta hanyar sanin cewa su sun halaka, shi ke sa a dinga kallon ba daidai ba a matsayin daidai da kuma kallon ba daidai ba a daidai, son zuciya ke sa ƙin gaskiya da raina ma'abotanta.

Son zuciya na daga cikin alamomin raunin imani ga Musulmi, kuma na daga abubuwan da ke halakar da masu aikatawa k**ar yadda magana ta gabata, saboda hakan na hana bin umarnin Ubangiji Allah Ta'ala ta hanyar yin adawa ko ƙin bin umarni da haninsa.

Idan muna neman tsira da ceto Musulmi, dole mu yi haƙuri da kuma jurewa tsaya wa a inda Allah Ubangiji Ta'ala ya umurce mu, mu bi umarni da hanin Allah da Manzonsa, mu jajirce wajen bin ka'idoji da dokokin da addinin Musulunci ya zo mana da su. Allah Ta'ala ya tsare mana imanin mu, ya kuma kare mu daga biye wa son zuciyoyin mu.

Ibrahim Abdu Hamza.

18/07/2025

Ba a buƙatar mutum ya kasance a wata ƙungiya ko wani shiri kafin a gane shi a matsayin Musulmi, Addini guda ɗaya ne wajen Allah, shi ne Musulunci, kuma shi ne addinin da Annabi Muhammad SAW ya zo da shi ya karantar.

Bai gina wani tsarin ƙungiya ba, bai buƙataci wani ya bi wani suna ko ra'ayi kafin ya karɓe shi ba. Abin da ake buƙata shi ne mutum ya karɓi Musulunci da gaskiya, ya bi Allah da Manzonsa, ya tsayu a kan ibada da kyawawan ayyuka.

Yanzu muna ganin wasu na mayar da shi tamkar wata ƙungiya ko ƙabila, inda suke ganin idan ba daga cikinsu ba, to kai ba kowa ba ne a addini, tunani dai wanda babu asali a cikin Qur'ani da Sunnah. Addinin Musulunci yana da hujjoji bayyanannu, kuma komai da ake yi a cikinsa yana buƙatar hujja daga Allah da Manzonsa, ba daga ra'ayin mutum ba.

Babu addini da Allah ke karɓa sai Musulunci, ba za a bauta wa Allah ta hanyar ƙungiya, ko al'ada, ko wani tunani da ba a gina shi da hujja ba. Manzon Allah SAW da Sahabbai sun nuna a aikace cewa tafarkin gaskiya shi ne bin Musulunci daidai da yadda Allah ya saukar bisa koyarwar Annabi Muhammad SAW.

Tabbas Manzon Allah SAW ya isar da saƙon Allah, kuma ya sauke amanar da Allah SWT ya ɗora masa, kuma ya koma ga Allah alhalin jama'arsa ko al'umarsa tana kan hanya wadda babu karkata a cikinta, darenta k**ar ranarta babu kuma wanda ke kauce mata sai halakakke. Ya nuna wa al'umarsa dukkanin alkhairi domin su yi riƙo da shi don samun tsira, ya kuma gargaɗe su daga dukkan sharri don su guje masa.

Mu daina ƙyamar juna, mu guji wulakanta juna bisa la'akari da ƙungiya ko ɓangaranci. Mu tuna da manufar rayuwarmu ita ce mu bauta wa Allah shi kaɗai bisa koyarwar masoyinmu Annabi Muhammad SAW, mu kuma roƙi Allah ya karɓe mu, ya tsare mana imani, ya sa mu mutu a kan tafarkin Musulunci na gaskiya.

Ibrahim Abdu Hamza.

18/07/2025

Ba a buƙatar mutum ya kasance a wata ƙungiya ko wani shiri kafin a gane shi a matsayin Musulmi, Addini guda ɗaya ne wajen Allah, shi ne Musulunci, kuma shi ne addinin da Annabi Muhammad SAW ya zo da shi ya karantar.

Bai gina wani tsarin ƙungiya ba, bai buƙataci wani ya bi wani suna ko ra'ayi kafin ya karɓe shi ba. Abin da ake buƙata shi ne mutum ya karɓi Musulunci da gaskiya, ya bi Allah da Manzonsa, ya tsayu a kan ibada da kyawawan ayyuka.

Yanzu muna ganin wasu na mayar da shi tamkar wata ƙungiya ko ƙabila, inda suke ganin idan ba daga cikinsu ba, to kai ba kowa ba ne a addini, tunani dai wanda babu asali a cikin Alƙur'ani da Sunnah. Addinin Musulunci yana da hujjoji bayyanannu, kuma komai da ake yi a cikinsa yana buƙatar hujja daga Allah da Manzonsa, ba daga ra'ayin mutum ba.

Duba hadisin da ya nuna yadda al'umma za su rabu gida har saba'in da kusan uku 73. Kaso ɗaya ne daga ciki za su tsira daga azabar Allah, su ne waɗanda su ke bin hanya da fahimta ta Annabi da sahabbansa. To kalli yadda zamanin da muke ciki ya cika da ruɗani na rarrabuwar kai daga Ƙungiyoyi da ra'ayoyi.

Babu addini da Allah ke karɓa sai Musulunci, ba za a bauta wa Allah ta hanyar ƙungiya, ko al'ada, ko wani tunani da ba a gina shi da hujja ba. Manzon Allah SAW da Sahabbai sun nuna a aikace tafarkin gaskiya shi ne bin Musulunci daidai da yadda Allah ya saukar bisa koyarwar Annabi Muhammad SAW.

Tabbas Manzon Allah SAW ya isar da saƙon Allah, kuma ya sauke amanar da Allah SWT ya ɗora masa, kuma ya koma ga Allah alhalin jama'arsa ko al'umarsa tana kan hanya wadda babu karkata a cikinta, darenta k**ar ranarta babu kuma wanda ke kauce mata sai halakakke. Ya nuna wa al'umarsa dukkanin alkhairi domin su yi riƙo da shi don samun tsira, ya kuma gargaɗe su daga dukkan sharri don su guje masa.

Mu daina ƙyamar juna, mu guji wulakanta juna bisa la'akari da ƙungiya ko ɓangaranci. Mu tuna da manufar rayuwarmu ita ce mu bauta wa Allah shi kaɗai bisa koyarwar masoyinmu Annabi Muhammad SAW, mu kuma roƙi Allah ya karɓe mu, ya tsare mana imani, ya sa mu mutu a kan tafarkin Musulunci na gaskiya.

Ibrahim Abdu Hamza.

Address

Kano
AREWAREGION.

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Taskar Daliban Ilimi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Taskar Daliban Ilimi:

Share