Karatuttukan Malaman Musulunci

Karatuttukan Malaman Musulunci ​Welcome! I am a digital creator providing original commentary and educational breakdowns of Islamic lectures. Contact: [email protected]
(4)

I offer unique perspectives on clerics' teachings through deep analysis and daily reflections.

Mu Yawaita Salati ga Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (saw)
10/09/2026

Mu Yawaita Salati ga Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (saw)

Ba za mu yarda cin mutuncin malamai ya zama arha ba. Idan na ce malamai, ina nufin na kowane ɓangare.— Umar Tijjani Hass...
10/09/2026

Ba za mu yarda cin mutuncin malamai ya zama arha ba. Idan na ce malamai, ina nufin na kowane ɓangare.

— Umar Tijjani Hassan, Esq.

Taron ya gudana a yau Alhamis, 10 ga watan Satumba, 2026 a Yakubu Gowon NYSC Camp Fanisau da ke Dutse a Jihar Jigawa.​Al...
10/09/2026

Taron ya gudana a yau Alhamis, 10 ga watan Satumba, 2026 a Yakubu Gowon NYSC Camp Fanisau da ke Dutse a Jihar Jigawa.

​Allah ya taimaka, ya ba su ikon aiki kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Amin.

Sanata Shehu Buba ya kai wa Sheikh Jingir ziyarar ta’aziyyar rasuwar Ma’ajin Ƙungiyar Izala, Al-Hafiz Bala Yusuf.Allah y...
10/09/2026

Sanata Shehu Buba ya kai wa Sheikh Jingir ziyarar ta’aziyyar rasuwar Ma’ajin Ƙungiyar Izala, Al-Hafiz Bala Yusuf.

Allah ya jikan Malam Bala da rahama.

Sheikh Musa Ayyuba Lukuwa ya yi karatun wanda ya karanto daga littafan Musulunci. Duk da cewa wasu za su iya cewa usulub...
09/09/2026

Sheikh Musa Ayyuba Lukuwa ya yi karatun wanda ya karanto daga littafan Musulunci. Duk da cewa wasu za su iya cewa usulubinsa bai yi musu ba, amma sun san cewa ba shi ne ya ƙirƙiro karatun ba, akwai shi a rubuce cikin littafan Musulunci.

Maimakon masu ilimi su ƙalubalanci Sheikh Lukuwa, sai wawayen gari saboda jahilcinsu da kuma zuga daga jahilan malamai, sai s**a fara cin alwashin hàlaka Sheikh Lukuwa, kamar yadda babban Tsagera, wato Mai Barewa, ya dinga sakin video episode-episode na zagi da barazana. Alhamdulillah, Ahlussunnah ansha su sun warke. An kàshe Sheikh Albani da Sheikh Ja’afar, don haka sun shirya wa ƙananan marasa kunya. A halin yanzu Mai Barewa na gidan gyaran hali. Wannan salon na ’yan bidi’a ya rushe nan take.

Maimakon waɗannan malamai su karbi tayin muqabalar da Sheikh Lukuwa yaketa aika musu, ko su sa Gwamnati ta shirya musu muqabala domin su titsiye Sheikh Lukuwa, sai s**a kauce wa jin kunya saboda sun ga yadda Mal. Lawan Triumph ya biya wa ’yan bidi’ar Kano karatu dalla-dalla.

Yanzu abin da suke so wai kawai Gwamnati ta ɗauki mataki a kan Sheikh Lukuwa, saboda sun rasa yadda za su yi da shi, ga shi kuma suna tsoron jin kunya idan aka haɗa musu zama da shi.

Tambaya zuwa ga waɗannan ƙungiyoyin Bidi’a kamar haka:

1. Me ya sa ba ku taɓa yin ganganmi domin tilastawa Gwamnati ta hana shirka da bidi’a a hubbarar Shehu ba?

2. Me ya sa duk kashe-kashe da sace-sacen mutane da ake yi a Jihar Sokoto, ba ku taɓa taro a kai ba?

3. Me ya sa kuka ƙi karɓar tayin muƙabalar da Sheikh Lukuwa ya aika muku?

4. Me ya sa ba za ku ce Gwamnati ta shirya muku zama da shi ba, sai dai ku ce Gwamnati ta ɗauki mataki a kansa?

Allah ka raba mu da bidi’a. Amin.

08/09/2026

Sanarwa ta musamman ga masu bibiyar wannan shafi namu mai albarka, a duba comment section

“Idan yana tsammanin, ko ire-irensa suna tunanin idan s**a yi irin wannan rubutun ko s**a yi irin wannan maganganun, ni ...
08/09/2026

“Idan yana tsammanin, ko ire-irensa suna tunanin idan s**a yi irin wannan rubutun ko s**a yi irin wannan maganganun, ni zan dawo na janye, wai kan abin da na faɗa sai in ce a bara na tsorata tunda mutane na faɗi magana sun fara lankwasa ta, to (indai nine) ai ka daɗe ba ka yi ba.”

Nine nan na faɗa, na ce na gamsu, ni Tinubu zan yi, kuma in sha Allahu dalilai na suna nan tafe. Kuma ko ban kawo dalili ko ɗaya ba, idan na ce ra’ayina ne, ai ban jin akwai abin da aka isa a yi. Indai wanda yake tallata Peter Obi, a matsayinsa na Musulmi ya yarda ya tallata Obi, indai shi bai yi laifi ba a Musulunce, to ni na yi laifi don na ce Tinubu zan yi?

- Sheikh Sani Isah Kano

07/09/2026

Sakon Godiya daga Shiekh Abdurrazak Yahya Haifan ga al-ummar musulmai.

Sheikh Abdurrazak Yahya Haifan yanzu haka yana gabatar da karatun Shu’abul Iman daga Area 11 Mosque, Abuja.
07/09/2026

Sheikh Abdurrazak Yahya Haifan yanzu haka yana gabatar da karatun Shu’abul Iman daga Area 11 Mosque, Abuja.

Bayan samun sabani na tsawon lokaci tsakanin Dr. Jabir Mai Hula da Sheikh Amore, a ziyararsa a Jihar Sokoto, Sheikh Adam...
07/09/2026

Bayan samun sabani na tsawon lokaci tsakanin Dr. Jabir Mai Hula da Sheikh Amore, a ziyararsa a Jihar Sokoto, Sheikh Adam Muhammad Albaniy Gombe ya jagoranci zaman sulhu tsakaninsu.

Lallai wannan abun a yaba ne sosai. Allah ya kawar da sabani a nan gaba tsakanin Malaman Sunnah. Allah ya saka wa kowa da alheri, Amin.

Address

Kano
Kano
700101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Karatuttukan Malaman Musulunci posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Karatuttukan Malaman Musulunci:

Shortcuts

Share