Dankwano Islamic Foundation

Dankwano Islamic Foundation ILIMIN ADDINI DA TARBIYYA

20/03/2025

MARTANI GA 'YAN KUR'ANI ZALLA!

(Wajibcin Riko Da Sunnar Annabi S.A.W)

Tare Da: Malam Abubakar Huguma.

An Fara Tafsirin Ramadan (1446/2025) a Garin Dutsinma Jihar Katsina.  Malaminmu Malam Musa Muhammad Dankwano zai gabatar...
02/03/2025

An Fara Tafsirin Ramadan (1446/2025) a Garin Dutsinma Jihar Katsina.

Malaminmu Malam Musa Muhammad Dankwano zai gabatar har karshen watan Ramadan.

17/12/2024

Labarin Sababin Tuban Wani Babban Malami

17/12/2024
21/07/2024

Yin Ladabi Ga Manya

18/01/2024

Ku karbe allunan daga hannun fasiki!

Wata rana A'amash (Sulaiman Ibn Mihran) sun fita kai gawa makabarta, sai wani ya yi masa jan-gora, da aka zo dawo wa sai ya kauce hanya da shi, lokacin da s**a shiga cikin sahara, sai ya ce da A'amash, ka san a ina kake? Kana sahara kaza, kuma ba zan mayar da kai gida ba sai ka cika min alluna na da hadisi. Sai A'amash ya ce, to rubuta, bayan ya cika masa allunansa sai ya mayar dashi gida. Suna shigowa garin Kufa sai ya ba wa wani allunan ya rike masa. Lokacin da ya kai A'amash kofar gidansa sai ya cukume shi ya ce, ku karbe allunan da ke hannu fasiki. Sai ya ce, ya baban Muhammad, ai ba sa nan, bayan ya fitar da tsammanin samunsu sai A'amash ya ce, duk hadisan da zantar da kai a cikinsu karya ne. Sai ya ce da shi, saninka da Allah ya fi karfin ka yi karya.
Nuzhatul Fudhala'i, 1/653.
A'amash babban malamin hadisi ne, mutumin Kufa, yana da tsanani game da ruwaya, don haka dalibai suke shan wahala kafin ya zantar da su hadisi. Akwai labaransa makatan wannan masu ban mamaki. Ya rasu a shekara ta 148 a Kufa. Allah ya yi masa rahama. Amin

Address

NO (1023) UNGUWAR WAMBAI, GWALE KANO Way
Kano

Telephone

+2348079059979

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dankwano Islamic Foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Dankwano Islamic Foundation:

Share