11/01/2024
*DAGA CIKIN ADDU'O'IN SHIGA MASALLACI*
Daga Abdullahi Ɗan Amru Ɗan Âas (Allah Ya ƙara musu yarda), daga Manzon Allah ﷺ:
*Cewa ya kasance idan zai shiga masallaci sai ya ce: "A'OUZU BILLAAHIL AZEEM, WA BI WAJHIHIL KAREEM, WA SULTANIHIL QADEEM MINASSHAITANI-RRAJEEM" sai ɗaya daga masu ruwayar ya ce da malaminsa: wai shikenan abunda Annabi yake faɗi? Sai Sahabin ya ce eh. Sai Sahabin ya ce: "Idan mutum ya fadi wannan addua, sai shaiɗan ya ce: an kare shi (wanda yayi addu'ar) daga gare ni a yau bakiɗaya."*
_Abu Dawood_
Ma'anar Addu'ar: Ina neman tsarin Allah Mai Girma, da kuma albarkacin zatinSa Mai karamci tare da alfarmar daɗaɗɗen mulkinSa (da Ya kare ni) daga Shaiɗani jefaffe (korarre daga rahamar Allah).
KHALID ARZAI