AMIH TV

AMIH TV AMIH TV Is a Islamic Broadcasting Medium That Transmitt progrmms based on Quran and sunnah of proph

15/08/2026

Daga cikin Siffar Ahlusunnah itace karatu da karantarwa ako wane lokaci, cikin dare da rana, mazansu da matansu

Ahlusunnah ku godewa Allah!!!

08/08/2026

Dr, ya kara da cewa a yanzu ba al'ummar Gombe ne kaɗai ke Adawa da siyasar Malam Fantami ba, hatta sauran gwamnonin Arewa na ganin shigar Isa Fantami wannan fage na siyasa tare da cimma nasarar Zama Gwamna, babbar barazana ce garesu duba da irin tarin ilimi da Allah ya bashi, haka da karbuwar da ya samu daga al'ummar Arewacin ƙasar,

Duba cikakken Bidiyo ta wannan link

https://youtu.be/0wMWzZi1mT0

Dr, ya kara da cewa a yanzu ba al'ummar Gombe ne kaɗai ke Adawa da siyasar Malam Fantami ba, hatta sauran gwamnonin Arew...
08/08/2026

Dr, ya kara da cewa a yanzu ba al'ummar Gombe ne kaɗai ke Adawa da siyasar Malam Fantami ba, hatta sauran gwamnonin Arewa na ganin shigar Isa Fantami wannan fage na siyasa tare da cimma nasarar Zama Gwamna, babbar barazana ce garesu duba da irin tarin ilimi da Allah ya bashi, haka da karbuwar da ya samu daga al'ummar Arewacin ƙasar,

Duba cikakken Bidiyo ta wannan link

Dr, ya kara da cewa a yanzu ba al'ummar Gombe ne kaɗai ke Adawa da ...

Muhadara! Muhadara!!  Muhadara !!!A halin yanzu ana gudanar da lacca ta musamman da Dr. Ukkasha Husain ke gabatarwa wacc...
09/07/2026

Muhadara! Muhadara!! Muhadara !!!

A halin yanzu ana gudanar da lacca ta musamman da Dr. Ukkasha Husain ke gabatarwa wacce aka yi wa take da (BIKIN BARBELA......) laccar wadda ta mayar da hankali kan muhimmancin lafiya da wasu tsirrai masu amfani ga lafiyar ɗan Adam, musamman zogale.

A cikin laccar, Dr. Ukkasha ya yi bayani dalla-dalla kan irin gagarumar gudunmawar da zogale ke bayarwa wajen inganta lafiyar jiki.

Ya bayyana cewa zogale na taimakawa wajen ƙarfafa garkuwar jiki, inganta ƙwaƙwalwa, lafiyar zuciya, gaɓoɓi da sauran sassan jiki.

Haka kuma, ya gabatar da hanyoyi daban-daban na sarrafa zogale da yadda ake amfani da shi cikin aminci domin samun cikakkiyar fa'idarsa ga lafiya.

Dr. Ukkasha, wanda ya fito daga Jihar Kaduna, ya halarci wannan cibiyar ta Al-majlisul Islami Hotoro, inda Dr Abdullahi M. Getso ya jagoranci tarbar sa.

A yayin taron kuma, Shaykh Abubakar Abbas ne ya gabatar da ta'alikai da karin haske kan muhimman batutuwan da aka tattaunawa.

A farkon jawabinsa, Dr. Ukkasha ya fara da wata magana ta hikima kan magungunan zamani. Inda ya bayyana cewa manufar wasu kamfanonin hada magunguna ita ce ci gaba da kasuwanci, yana mai cewa wasu magunguna kan rage alamomin cuta ne kawai ba tare da kawar da ita gaba ɗaya ba.

A cewarsa, magungunan gargajiya masu inganci, musamman zogale idan aka yi amfani da su yadda ya dace, na iya taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa jiki ya yaƙi cututtuka da kuma inganta lafiyar ɗan Adam baki ɗaya

Domin kallo sai ku latsa nan .

Address

Yan Dodo
Kano Outlying
234

Telephone

+2349011907887

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AMIH TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to AMIH TV:

Shortcuts

Share