Jibwis Godogodo branch

Website

Jibwis Godogodo branch AQidan Sunnah

Saturday Rabi’ul Awwal 9, 1448AHSaturday , August 22, 2026KUNGIYAR JAMA’ATUL IZALATIL BID’AH WA’IKAMATIS SUNNAH  (KADUNA...
23/08/2026

Saturday Rabi’ul Awwal 9, 1448AH
Saturday , August 22, 2026

KUNGIYAR JAMA’ATUL IZALATIL BID’AH WA’IKAMATIS SUNNAH (KADUNA STATE) A FADAR MAI MARTABA SARKIN JAMA’A

Shugaban Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS) na Jihar Kaduna, Alh. Adamu Ibrahim, ya kai ziyarar ban girma Fadar Mai Martaba Sarkin Jama’a

Mai Martaba Sarkin Jama’a, Dr. Muhammad Isa Muhammad II, CON, tare da tawagar Majalisar Masarautarsa, sun tarbi Shugaban da tawagarsa da karamci da girmamawa.

Ziyarar ta zo ne a matsayin wani ɓangare na ayyukan Da’awah da Ƙungiyar IZALA ke gudanarwa a fadin jihar. A cikin wannan aiki, Ƙungiyar ta tura Malamai zuwa sassa daban-daban na Jihar Kaduna domin gudanar da wa’azi da kira zuwa ga addinin Allah.

Albishirin Ku 'Yan Najeriya Musamman Mutanen Jahar KADUNA da Kewaye!GAGARUMAR MUHADARA A SULTAN BELLO KADUNA! Shugaban J...
09/07/2026

Albishirin Ku 'Yan Najeriya Musamman Mutanen Jahar KADUNA da Kewaye!

GAGARUMAR MUHADARA A SULTAN BELLO KADUNA!

Shugaban JIBWIS Kaduna, Shugaba Adamu Ibrahim na farin cikin gayyatar al’ummar Musulmi zuwa gagarumar muhadara ta musamman, a munasabar auren diyar Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun, da ɗan Dr. Ibrahim Jalo Jalingo.

Malamai da manyan baki za su halarta, ciki har da Imam Dr. Abdullahi Bala Lau, Shugaban JIBWIS Nigeria, Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun, Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina Sautussunnah, Professor Abdullahi Saleh Pakistan, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, Sheikh Lawal Abubakar Shuaibu Trimp, Sheikh Abubakar Abdulsalam Baban-Gale, da Sheikh Dr. Abdulkadir Saleh Kazaure.

Rana: 24 MUHARRAM 1448H, 9th JULY 2026.

Wuri: Masallacin Juma'ah na Sultan Bello-Kaduna.

Lokaci: Tsakanin Maghrib zuwa Isha'i.

Muna roƙon Allah Ya sanya alheri, albarka da zaman lafiya a wannan aure, Ya kuma sa mu amfana da faɗakarwa da nasihohin malamai.

Sanarwa: 📢

Ibrahim Shehu Giwa,
PRO JIBWIS Social Media,
Kaduna State.

WA'AZIN JIHA A KAURU LGShugaba Adamu Ibrahim, Sheikh Aliyu Abdullahi TelexImam Muhammad Auwal Abdullahi A madadin Kungiy...
16/06/2026

WA'AZIN JIHA A KAURU LG

Shugaba Adamu Ibrahim,
Sheikh Aliyu Abdullahi Telex
Imam Muhammad Auwal Abdullahi

A madadin Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa-iqamatis Sunnah ta Kasa Reshen Jihar Kaduna na gayyatar 'Yan Uwa Muslimi zuwa gagarumin Wa'azin Jiha da Da'awah da Kungiyar ta shirya inda za'a shiga lungu da sako na Karamar Hukumar Kauru.

Ayyukan Da'awah zasu fara daga:-
1. Ranar Alhamis 18/06/2026 za fara da Da'awah a garuruwa 40 na Karamar Hukumar.
2. Ranar Juma'a 19/06/2026 Malamai zasu gabatar da Huduba da Wa'azi kafin zuwan Liman, sai karatuttuka tsakanin Magariba da Isha'i a Masallatan Juma'a 35.
3. A ranar Asabar 20/06/2026 za a gabatar da karatuttuka na Iyayanmu Mata da safe a karkashin jagorancin Nisa'us Sunnah JIBWIS a Masallatan Juma'a 35.
4. Da Daddare za a gabatar da gagarumin Wa'azi a Garin Kauru ta Karamar Hukumar.

Malamai masu Wa'azi:-
1. Sheikh Aliyu Abdullahi Telex
2. Dr. Yusuf Ibrahim Kubau
3. Sheikh Jamilu Abubakar Albani
4. Dr. Muhammad Aliyu Low-cost
5. Dr. Nuruddeen Zubairu Dembo
6. Sheikh Nasir Yusuf Khdir
7. Sheikh Aminu Ibrahim Sautussunnah
8. Sheikh Aminu Saminaka
9. Dr. Yahya Lawal Asgar
10. Sheikh Umar Shehu Zaria
11. Dr. Muhammad Sani Abubakar
12. Barr. Adam Muhammad Almandawy
13. Sheikh Ibrahim Adam Almadany
14. Dr. Shuaibu Rabiu IMAMUD-Da'awah
15. Sheikh Ishaq Ibrahim Hayin Banki
16. Imam Muhammad Auwal ElWazeee
17. Imam Nuruddeen Muhammad Mujaheed
18. Dr. Ahmad Libiya
19. Sheikh Dalhatu Bello Amaru
20. Dr. Auwal Yunus
21. Dr. Jamilu Abdulkadir Assudany
22. Dr. Abubakar Shuaibu Jumare
23. Dr. Ahmad Ateeq Auwal.
24. Sheikh Shuaibu Salihu Zaria.

Da sauran Malamai da Alaramomi

An tanadi Malamai sama da 162 wadanda zasu gabatar da ayyukan Da'awar, Muhadarori da Wa'azi saboda muhimmanci da girman aikin

Taken Wa'azin "MU KOMA GA TAUHIDI"

Allah Ya bada ikon halarta, Amin.

SANARWA:
Aliyu Ahmad Jampalan
Sakataren Kungiyar

Ta Hannun:
Ibrahim Shehu Giwa
PRO JIBWIS SOCIAL MEDIA,
Kaduna State.

09/05/2026

Alhamdulillah

*MALAMAI 183 A SOBA*Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta jihar Kaduna ta shirya gagarumin sh...
08/04/2026

*MALAMAI 183 A SOBA*

Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta jihar Kaduna ta shirya gagarumin shirin Da’awah, inda za ta tura Malamai 183 zuwa lungunan karamar hukumar Soba domin gudanar da ayyukan Da'awah da wa’azin Jiha.

Za a gudanar da wannan babban taro ne kamar Haka:

1. Ranar Alhamis 09 ga Afrilu: Za'a yi ayyukan Da'awah, a lunguna da sakunan, na fadin Karamar Hukumar.

2. Juma'ah 10 April, hudubobin Juma'a, da Pre-Khudbah, da Muhadarori.

3. Asabar, 11 ga Afrilu, 2026: Wa'azin Mata da Gagarumin Wa'azin Jiha.

Duk zasu gudana ne a karkashin Jagorancin:

Shugaban Jiha, Shugaba Adamu Ibrahim, da Shugaban Majalisar Malamai, Imam Aliyu Abdullahi Telex da
Daraktan Agaji, Imam Muhammad Auwal Abdullahi

Taken wannan Da’awah da Wa’azin Jiha shi ne:

*مناقب الصحابة*
*MATSAYIN SAHABBAI*

Wannan taro zai tattaro fitattun Malamai daga sassa daban-daban, ciki har da:

Dr. Yusuf Ibrahim Kubau

Dr. Haruna Adam Danmagaji

Sheikh Nasir Yusuf Khidr

Dr. Muhammad Aliyu Low-cost

Dr. Nura Zubairu Dambo

Sheikh Aminu Ibrahim Sautussunnah

Dr. Ahmad Libiya

Sheikh Jamilu Abubakar Albani

Sheikh Umar Shehu Zaria

Barr. Ishaq Adam Almadany

Imam Khidr Manufa

Sheikh Dalhatu Bello Amaru

Dr. Abubakar Jumare Gidado

Dr. Jamilu Abdulkadir Assudany

Sheikh Adam Jibril Azzahidy

Dr. Shuaibu Rabiu Imamud Da’awah

Dr. Yahya Lawal Asgar

Da sauran manyan Malamai da alarammomi.

Wannan dama ce ta musamman ga al’umma su halarta, su amfana da ilimi, su kuma sabunta alakar su da tarihin Sahabbai, wadanda s**a dauki nauyin yada addinin Musulunci da sadaukarwa.

Allah Ya sanya albarka, Ya kuma karɓi wannan ƙoƙari.

Sanarwa:

Daga Sakataren Yada Labarai:
Imam Nuruddeen Muhammad Mujaheed.

Ta Hannun:

JIBWIS Social Media, Kaduna State.

05/04/2026
Alhamdulillah Yau Makarantan,Da’awa(IMWON) Darun Tahfizul Qur’an Godo Godo, Ta sauke Mahaddata AlQuran Mutum 21 Agarin g...
05/04/2026

Alhamdulillah
Yau Makarantan,Da’awa(IMWON) Darun Tahfizul Qur’an Godo Godo, Ta sauke Mahaddata AlQuran Mutum 21 Agarin godogodo
Muna addu’a Allah yasa musu albarka
Allah yasa muwanye Lafiya

Address

Godogodo Jama’a Local Government
Kafanchan

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jibwis Godogodo branch posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share