Ibrahim lawal

Ibrahim lawal Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Ibrahim lawal, Religious organisation, 17 Kwarbai Road, Kaduna.

09/03/2026

Alhamdulillah 💙💚💜💝

Naseeha daga makarantar *AL-KITABU WAS-SUNNA MEDIA TV* da *DA’AWATUS-SUNNAH FOUNDATION* akan amfani da social media:---*...
20/11/2025

Naseeha daga makarantar *AL-KITABU WAS-SUNNA MEDIA TV* da *DA’AWATUS-SUNNAH FOUNDATION* akan amfani da social media:

---

*📍Tattaunawa Ta Musamman Akan Amfani da Social Media*
*Tsakanin AL-KITABU WAS-SUNNA MEDIA TV da DA'AWATUS-SUNNAH FOUNDATION*

*AL-KITABU WAS-SUNNA MEDIA TV:*
Assalamu Alaikum warahmatullah. A yau muna tare da abokan aikinmu daga DA’AWATUS-SUNNAH FOUNDATION domin yin duba kan yadda musulmi ke amfani da social media a wannan zamani.

*DA’AWATUS-SUNNAH FOUNDATION:*
Wa Alaikumus Salam wa rahmatullah. Alhamdulillah, muna godiya da wannan damar. Social media tamkar takobi ce mai kaifi biyu. Ana iya amfani da ita wajen yada da’awah, ilimi, wa’azi, da haɗa al’ummah. Amma idan ba a kiyaye ba, tana iya janyo zunubi mai yawa.

*AL-KITABU WAS-SUNNA MEDIA TV:*
Hakika gaskiya ne. Mun lura da yadda matasa da yawa ke amfani da dandamali kamar WhatsApp, Facebook, da TikTok wajen aikata abubuwan da ba su dace ba. Saurin yadawa, tsiraici, ƙarya, da ɓata lokaci sun zama ruwan dare.

*DA’AWATUS-SUNNAH FOUNDATION:*
Eh, wannan lamari yana da matuƙar haɗari. Abin lura ne cewa duk abin da mutum ke posting, ana rubuta shi a littafin ayyukansa. Duk wanda ya ga posting ɗinka ya shiga ɓarna, kana da hannun jari a hakan.
*AL-KITABU WAS-SUNNA MEDIA TV:*
To mecece mafita?

*DA’AWATUS-SUNNAH FOUNDATION:*
Mafita ita ce a koyar da jama’a mahimmancin *niyyah* da *tsoron Allah* a yayin amfani da social media. A san cewa ana kallonmu kuma ana rubuta komai. Ya kamata mu rinƙa amfani da social media wajen:

- Yada hadisai da ayoyi
- Wa’azantarwa
- Nasiha
- Koyar da tarbiyya
- Ƙarfafa zumunci bisa gaskiya

*AL-KITABU WAS-SUNNA MEDIA TV:*
Na’am. Kuma yana da kyau mu kafa ƙungiyoyi masu amfani da social media wajen koyar da sahihiyar Sunnah da karantar da al’ummah gaskiya.

*DA’AWATUS-SUNNAH FOUNDATION:*
Hakika. Kuma muna ƙarfafa kowanne musulmi da ya mayar da social media nasa mimbarin da’awah. Domin wata kalma kaɗai da ka rubuta za ta iya canza rayuwar wani har abada.

*AL-KITABU WAS-SUNNA MEDIA TV:*
Muna yi wa kowa fatan alheri. Kuma muna roƙon Allah Ya sa mu yi amfani da dukkan hanyoyin zamani wajen bauta masa da yaɗa addininsa cikin hikima.

*DA’AWATUS-SUNNAH FOUNDATION:*
Amin. Kuma muna ƙarfafa dukkan masu bibiyar mu da su yada wannan saƙo ga wasu. Domin ɗa'a da yaɗa alheri ibada ne.

---

*📌Ku ci gaba da bibiyar shafukan AL-KITABU WAS-SUNNA MEDIA TV da DA’AWATUS-SUNNAH FOUNDATION don ƙarin nasihohi da shirye-shirye masu fa’ida.*

*_AL-KITABU WAS-SUNNA MEDIA TV WHATSAPP CHANNEL LINK_*

https://whatsapp.com/channel/0029VbBFgFp545uzEbyhkN3O

*_DA'AWATUS-SUNNAH FOUNDATION WHATSAPP CHANNEL LINK_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb6iSMD3wtb7FYCaMQ0A

Fiqihun Sallah!Komai a duniya kanã nisantanshi yana kara kankanta amma banda ka'aba, ita kana nisantanta tana kara girma...
28/10/2025

Fiqihun Sallah!

Komai a duniya kanã nisantanshi yana kara kankanta amma banda ka'aba, ita kana nisantanta tana kara girma, kana kusantanta tana kara kankanta.

Shiyasa wanda zaiyi sallah a gaban ka'aba yã fi shan wahalar fuskantar ka'aba domin ko kãfadansa ya kaucewa ginin ka'aba, sallarsa tã 6aci, domin shi wãjibine ya fuskanci شطر المسجد الحرام

Amma wanda yake garin makka idan zaiyi sallah sai ya fuskanci الجهة da yã tabbata yã fuskanci جهة shikenan sai ya kabbara sallarsa basai ya daidaita jikinsa ga شطر المسجد الحرام ba tunda bãya ganinta.

Wanda kuma yake wajen makka kaman mu sai mu kalli القبلة wato bangaren da tanan ne جهة da شطر المسجد الحرام take.

Shiyasa masallaci zai iya fin ginin ka'aba girma kuma haka zamuyi sahu a tsaye batare da kallon cewa sahummu yã wuce girman ka'aba ba.

Amma duk yadda ka'aba ta kai ga kankanta, baza'a iya yin sahu a wuceta ba saidai a zãgayeta saboda ita ko ina a jikinta شطر ce.

Muyi kokari mu rungumi littattafan fiqihun magabatammu mu nisanci littattafan fiqihun malaman zamani bazãka samu irin wa'yannan فوائد a cikinsu ba.

Allah ya bamu ikon dawwama da tabbata kan fikihun magabata.

Wassalamu Alaikum

Shams Musa Abban Sanam

Address

17 Kwarbai Road
Kaduna

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ibrahim lawal posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share