Halliru Maraya Forum

Halliru Maraya Forum Shafin Makarantar Halliru Maraya zai rika kawo muku karatuttukan da Malam ke gabatarwa a ko'ina.
(1)

KU CI GABA DA KASANCEWA SHEIKH DR. HALLIRU MARAYA KAI-TSAYE YAU 9:PM daga Ziwiyya Sheikh Musa Malami T/Wada Kaduna.
19/02/2026

KU CI GABA DA KASANCEWA SHEIKH DR. HALLIRU MARAYA KAI-TSAYE YAU 9:PM daga Ziwiyya Sheikh Musa Malami T/Wada Kaduna.

Assalamu Alaikum.Yau ɗin nan Laraba 1st Ramadan 1447AH/ 18th February 2026  Sheikh (Dr) Halliru Abdullahi Maraya zai buɗ...
18/02/2026

Assalamu Alaikum.

Yau ɗin nan Laraba 1st Ramadan 1447AH/ 18th February 2026 Sheikh (Dr) Halliru Abdullahi Maraya zai buɗe Tafseer kamar yadda aka saba.

A Zawiyyar Marigayi Sheikh Salihu Musa Malami da ke Tudun Nupawa Kaduna.

Ƙarfe Tara Na Dare 9:0 0pm in sha Allah.

IYAYEN ANNABI MUHAMMADU(SAW) 'YAN ALJANNA NEWasu mutane sun dauki kayan talla domin sayarwa a madadin IBLIS (L.A.) . Kay...
28/04/2024

IYAYEN ANNABI MUHAMMADU
(SAW) 'YAN ALJANNA NE

Wasu mutane sun dauki kayan talla domin sayarwa a madadin IBLIS (L.A.) . Kayan da Shaydan din kuwa ya dora masu a kansu domin su sayar masa shi ne CIN MUTUNCIN MANZON ALLAH (SAW) , wato halittar nan mai albarka , wadda Shaydan ya fi kin ta a cikin halittun Allah (SWT) .

Kowane mai talla da abin da yake fada a lokacin talla domin ya jawo hankalin mutane zuwa ga kayan
da yake so a saya . Su masu wannan talla, a madadin Shaydan , abinda suke cewa shi ne " IYAYEN ANNABI
'YAN WUTA NE . " Allah (SWT) Ya tsare mu . Innaa lil-Laahi , wa innaa ilayhi raaji'uun !

SAKAMAKON DA WANNAN TALLA ZAI HAIFAR Duk wanda ya yarda da cewa
iyayen Manzon Allah (SAW) 'yanwuta ne , wato kafirai ne , to zai samu kansa cikin :

i . karyata Allah (SWT) ;
ii. karyata Manzon Allah (SAW) ;
iii. cutar da Allah (SWT), da kuma ManzonSa (SAW) .
SAKAMAKON DA MASU TALLA DA SAYEN WANNAN KAYA ZASU SAMU
Mafi kankantar sakamakon da masu cewa iyayen Manzon Allah (SAW) , Abdul-Laahi da Aaminatu (A.S.), 'yan wuta ne , da wadanda s**a yarda da haka , zasu samu shi ne
zama a katafaren gidan Shaydan, wato WUTA . Allah (SWT) Ya tsare mu .

Zasu samu wannan sakamako ne sanadiyyar karyata Allah (SWT) , karyata Manzon Allah (SAW) , da
kuma cutar da Allah (SWT) da
ManzonSa (SAW) . Insha'Allah , zamu ji yadda fadin haka yake karyata Allah (SWT) da ManzonSa (SAW) , da kuma cutar da su .

DALILAN DAKE NUNA CEWA
IYAYEN MANZON ALLAH (SAW) BA 'YAN WUTA BA NE
Akwai dalilai masu nuna cewa
iyayen Manzon Allah (SAW) ba 'yan wuta ba ne . Dalilan kuwa su ne :
i. dalilai daga Al-Qur'ani ,
ii. dalilai daga Hadisi , da kuma
iii. dalilai na hankali .

Abin mamaki ne a ce musulmi- mai-hankali ya yarda , kuma har ya rika fadin cewa iyayen Shugaban manzanni (A.S.) , kuma
halittar da Allah(SWT) Ya fi so a cikin dukkan halittarSa , "'yan wuta ne ." A'uudhu bil-Laah ! A dalilin wannan gawurtaccen rashin hankali da masu fadi , da kuma
yarda da wannan mummunar
magana , ke nunawa zan fara
amfani da dalilai na hankali domin kifar da wannan kaya na talla da Shaydan (L.A.) ya dora wa masu tallan kayansa domin su sayar masa .

DALILAI NA HANKALI MASU NUNA CEWA IYAYEN MANZON ALLAH (SAW) BA 'YAN WUTA BA NE
Akwai dalilai , masu yawa ,na
hankali masu nuna cewa iyayen Manzon Allah (SAW) , Abdul-Laahi (AS) , da Aminatu (AS) , ba 'yan wuta ba ne . Daga ciki akwai :
i. sunayensu (AS) : sunan mahaifin Manzon Allah (SAW) Abdul-Laahi , wato BAWAN ALLAH . Sunan mahaifiyarsa Aaminatu , wato WADDA TA YI IMANI. Idan mutum yana da lafiyayyen hankali , zai gane cewa lallai Allah (SWT) Ya kimsawa iyayensu ne su sa masu wannan suna saboda ya san zasu kasance
mutane ne muminai wadanda zasu haifi shugaban manzanni (SAW) .
A wancan lokaci , babu mutane masu suna Abdul-Laahi , da Aaminatu , a cikin mushirikai .
ii. iyayen dukkan Annabawa (AS) muminai ne : dukkan Annabawa , har da Annabi Ibraahiim (AS) , iyayensu ba kafirai ba ne . Saboda haka , mai lafiyayyen hankali zai
fahimci cewa iyayen Manzon da ya fi dukkan Manzanni komai , a wurin Allah (SWT) , baza su zama
a ce su kadai ne kafirai ba, 'yan wuta . A'uudhu bil- Laah !
Misali : Babu yadda za a yi a ce kwamishinoni nada motar ofis , amma gwamna baida ita .
iii. duk iyayen Annabawa(AS) 'yan Aljanna ne : Mai hankali zai fahimci cewa babu yadda za a yi a ce kowane manzo zai zauna tare da iyayensa a Aljanna , amma Shugabansu nasa iyayen na wuta .
iv. duk wanda ya shiga Aljanna. ya shiga ne saboda sakamakon bin sakon da Manzon Allah(SAW) ya kawo :
mai hankali zai fahimci cewa babu yadda za a yi a ce duk alherin nan da Manzon Allah (SAW) ya zo da shi , amma kuma a ce iyayensa (AS) ba zasu amfana ba, saidai su zauna a wuta tare da Shaydan, Abuu Jahlin , Abuu Lahbin , Fir'aun, da sauran kafirai.

Misali : Attajiri , kuma mutumin kirki , mai ba talakawa abinci , an ya zai hana iyayensa abinci , har su mutu saboda yunwa ?
v. Makkah da Madinah sun fi
kowane gari ne saboda an haifi Manzon Allah (SAW) ne a Makkah, kuma ya tafi gidan rahama a Madinah : mai hankali zai fahimci
cewa yadda garin da aka haifi
Manzon Allah (AS) ya fi kowane gari , haka tsatso , da kuma cikin da Manzon(SAW) ya zauna ya fi kowane tsatso da ciki. Saboda haka , mai tsatson , da kuma mahaifar da Manzon Allah (SAW) ya zauna , wato Abdul-Laahi (AS) , da Aaminatu (AS) , sun fi iyayen kowa, dalilin haka su ba 'yan wuta ba ne .
vi. mushirikai kazanta ne : Saboda haka , babu yadda za a yi a ce Allah (SWT) Ya sanya Manzon Allah (SAW) , halittar da Ya fi so , a cikin kazanta , wato tsatso da mahaifa
ta mutane kafirai . Wannan yana nuna wa mai hankali cewa mai tsatso da mahaifar da Annabi (SAW) ya zauna , wato iyayensa (AS) , ba
kafirai ba ne , domin su ba najasa ba ne .
Zan tsaya a nan yau . Insha' Allah gobe ko jibi , zan kawo wasu daga cikin dalilai na Hadisi masu nuna cewa iyayen Manzon Allah (AS) ba 'yan wuta ba ne kamar
yadda Shaydan ya bayar da talla ga wasu , kuma suke yi.
Allah (SWT) Ya kara wa Manzon Allah (SAW) alayensa(AS) , da sahabbansa (RA) , tsira da aminci .

"𝙎𝙪 𝙆𝙪ɗ𝙞 𝘼𝙗𝙪𝙣 𝘿𝙖 𝙔𝙖 𝙎𝙖 𝙎𝙪𝙠𝙚 𝘽𝙞𝙮𝙖𝙣 𝘽𝙪ƙ𝙖𝙩𝙖 𝙎𝙖𝙗𝙤𝙙𝙖 𝙔𝙖ƙ𝙞𝙣𝙞𝙣 𝘿𝙖 𝙆𝙖𝙠𝙚 𝘿𝙖 𝙎𝙝𝙞𝙣𝙚 𝘼𝙠𝙖𝙣𝙨𝙪, 𝙄𝙙𝙖𝙣 𝙆𝙖𝙣𝙖 𝘿𝙖 𝙎𝙪 𝙖 𝘼𝙡𝙟𝙞𝙝𝙪 𝘽𝙖𝙠𝙖 𝙏𝙪𝙣𝙖𝙣𝙞𝙣 𝙠...
30/11/2023

"𝙎𝙪 𝙆𝙪ɗ𝙞 𝘼𝙗𝙪𝙣 𝘿𝙖 𝙔𝙖 𝙎𝙖 𝙎𝙪𝙠𝙚 𝘽𝙞𝙮𝙖𝙣 𝘽𝙪ƙ𝙖𝙩𝙖 𝙎𝙖𝙗𝙤𝙙𝙖 𝙔𝙖ƙ𝙞𝙣𝙞𝙣 𝘿𝙖 𝙆𝙖𝙠𝙚 𝘿𝙖 𝙎𝙝𝙞𝙣𝙚 𝘼𝙠𝙖𝙣𝙨𝙪, 𝙄𝙙𝙖𝙣 𝙆𝙖𝙣𝙖 𝘿𝙖 𝙎𝙪 𝙖 𝘼𝙡𝙟𝙞𝙝𝙪 𝘽𝙖𝙠𝙖 𝙏𝙪𝙣𝙖𝙣𝙞𝙣 𝙠𝙖𝙣𝙖 𝙙𝙖 𝙒𝙖𝙩𝙖 𝙈𝙖𝙩𝙨𝙖𝙡𝙖, 𝙒𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙔𝙖ƙ𝙞𝙣𝙞𝙣 𝙎𝙝𝙞 𝙉𝙚 𝙎𝙞𝙧𝙧𝙞𝙣 𝘽𝙞𝙮𝙖𝙣 𝘽𝙪ƙ𝙖𝙩𝙖𝙧 𝙆𝙪ɗ𝙞.

𝘿𝙖 𝙖𝙘𝙚 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃 𝙕𝙖𝙞 𝙔𝙞 𝙬𝙖 𝘽𝙖𝙬𝙖 𝙁𝙖𝙩𝙖𝙝𝙞 𝙔𝙖 𝙎𝙖𝙢𝙪 𝙔𝙖ƙ𝙞𝙣𝙞 𝘿𝙖 𝙎𝙝𝙞, 𝙄𝙧𝙞𝙣 𝙃𝙖𝙠𝙖 𝙔𝙖 𝙧𝙞𝙠𝙖 𝙅𝙞 𝙖 𝙍𝙖𝙣𝙨𝙝𝙞 𝙘𝙚𝙬𝙖 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃 𝙣𝙚 𝙕𝙖𝙞 𝙈𝙖𝙜𝙖𝙣𝙘𝙚 𝙈𝙖𝙨𝙖 𝙈𝙖𝙩𝙨𝙖𝙡𝙖𝙧𝙨𝙖, 𝙩𝙤 𝙙𝙖 𝙔𝙖 𝙂𝙖𝙢𝙖 𝘼𝙧𝙯𝙞ƙ𝙞 𝘿𝙪𝙣𝙞𝙮𝙖 𝘿𝙖 𝙇𝙖𝙝𝙞𝙧𝙖.''

SHEHU ALIYU HARAZIMI .

𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃 𝙔𝙖 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃 𝙆𝙖 𝘼𝙯𝙪𝙧𝙩𝙖 𝙈𝙪 𝙙𝙖 '𝙔𝙖ƙ𝙞𝙣𝙞 𝘼𝙠𝙖𝙣 𝙈𝙖𝙝𝙖𝙡𝙞𝙘𝙘𝙞𝙣𝙢𝙪.

ᴢᴜᴡᴀɴ sʜᴇɪᴋʜ ɪʙʀᴀʜɪᴍ ɪɴʏᴀss ғᴀʟᴀsƊɪɴᴜ.....sʜᴇɪᴋʜ ɪʙʀᴀʜɪᴍ ɪɴʏᴀss (ʀᴀ) ᴀ ᴄɪᴋɪɴ ᴢɪʏᴀʀsᴀ ᴀ ᴍᴀsᴀʟʟᴀᴄɪɴ ᴋᴜᴅᴜs ɴᴀ ғᴀʟᴀsᴅɪɴ ᴀ sʜ...
19/10/2023

ᴢᴜᴡᴀɴ sʜᴇɪᴋʜ ɪʙʀᴀʜɪᴍ ɪɴʏᴀss ғᴀʟᴀsƊɪɴᴜ.....

sʜᴇɪᴋʜ ɪʙʀᴀʜɪᴍ ɪɴʏᴀss (ʀᴀ) ᴀ ᴄɪᴋɪɴ ᴢɪʏᴀʀsᴀ ᴀ ᴍᴀsᴀʟʟᴀᴄɪɴ ᴋᴜᴅᴜs ɴᴀ ғᴀʟᴀsᴅɪɴ ᴀ sʜᴇᴋᴀʀᴀʀ 1966. ɢᴀ ᴋᴀɗᴀɴ ᴅᴀɢᴀ ᴄɪᴋɪɴ ᴀʙɪɴᴅᴀ ʏᴀ ғᴀɗᴀ ᴀ ʟᴏᴋᴀᴄɪɴ ᴢɪʏᴀʀᴀʀ:

ɴᴀ sᴀᴍɪ ᴀʟғᴀʀᴍᴀʀ ʏɪɴ sᴀʟʟᴀʀ ᴊᴜᴍᴀ'ᴀ ᴀ ᴄɪᴋɪɴ ᴍᴀsᴀʟʟᴀᴄɪɴ ᴀǫsᴀ (ᴋᴜᴅᴜs) ᴅᴀ ᴡᴀᴢɪғᴀʜ ᴍᴀɪ ᴛsᴀʀᴋɪ ᴀ ᴋᴀʀᴋᴀsʜɪɴ ᴅᴜᴛsᴇɴ sᴀᴋʜʀᴀʜ ᴍᴀɪ ᴀʟʙᴀʀᴋᴀ, ᴅᴀɢᴀ ɪɴᴅᴀ ᴍᴀɴᴢᴏɴᴍᴜ (sᴀᴡ) ʏᴀ ᴛᴀғɪ ᴍɪ'ɪʀᴀᴊɪ.

ɴɪ ᴅᴀ ᴋᴀɪɴᴀ ɪɴᴀ ᴋᴀʟʟᴏɴ ʙᴀʟᴀ'ɪɴ ғᴀʟᴀsᴛɪɴ (ᴘᴀʟᴇsᴛɪɴᴇ 🇵🇸) ᴀ ᴄɪᴋɪɴ ᴢᴜʀғɪɴ ʀᴀɪ ɴᴀ. ᴋᴜᴅᴜs ᴛᴀɴᴀ ᴡᴀᴋɪʟᴛᴀʀ ᴢᴜᴄɪʏᴀʀ ᴀʟ'ᴜᴍᴍᴀʀ ᴍᴜsᴜʟᴍɪ, ᴀ ɢᴀʀᴇɴɪ.

ᴋᴜᴅᴜs ᴛᴀɴᴀ ʙᴜᴋᴀᴛᴀʀ ᴍᴀᴢᴀᴊᴇ ᴍᴀsᴜ ᴛsᴀʀᴋɪɴ ᴢᴜᴄɪʏᴀ ᴋᴡᴀᴛᴀɴᴋᴡᴀᴄɪɴ ɪʀɪɴᴛᴀ sᴀʏʏɪᴅɴᴀ ᴜᴍᴀʀ (ʀᴀ) ʙᴀ ’ʏᴀɴ sɪʏᴀsᴀ ᴍᴀsᴜ sᴏɴ ᴅᴜɴɪʏᴀ ʙᴀ.

ᴢᴀ ᴀ ᴄɪ ɢᴀʙᴀ ᴅᴀ ᴊɪʜᴀᴅɪ ᴀ ᴋᴇᴡᴀʏᴇɴ ʙᴀʏᴛᴜʟ ᴍᴀǫᴅɪs ʜᴀʀ ᴢᴜᴡᴀ ʀᴀɴᴀʀ sᴀᴋᴀᴍᴀᴋᴏ, ᴋᴀᴍᴀʀ ʏᴀᴅᴅᴀ ʏᴀ ᴛᴀʙʙᴀᴛᴀ ᴀ ʜᴀᴅɪsɪ.

"Duk wanda kaga yasan kai Musulmi ne tare da hakan  ya iya furta kalmar bid'a, ko shirka akanka. To babu abun daya rage ...
17/10/2023

"Duk wanda kaga yasan kai Musulmi ne tare da hakan ya iya furta kalmar bid'a, ko shirka akanka. To babu abun daya rage masa gare ka illa ya jiraci Alkiyama domin ya dannaka cikin wuta. Idan ma dawani amfani daza kayi masa bai wuce yai amfani dakai lokutan zabe ba".

SHEIKH DR.HALLIRU MARAYA.

14/09/2023

KU KASANCE DA WANNAN KAFAR DOMIN KAWO MUKU TARON MAULIDIN SHEIKH AHMAD TIJJANI RTA KAI-TSAYE.

Daga Tudun Wada Kaduna da Karfe 8:30pm .

𝗠𝗨𝗠𝗕𝗔𝗥𝗜𝗡 𝗝𝗨𝗠𝗔'𝗔 🕋"Ka yi hankali da mutumin da ya ke Da'awar Malanta sannan kuma ya tsunduma cikin harkar Siyasa tare da ...
21/07/2023

𝗠𝗨𝗠𝗕𝗔𝗥𝗜𝗡 𝗝𝗨𝗠𝗔'𝗔 🕋

"Ka yi hankali da mutumin da ya ke Da'awar Malanta sannan kuma ya tsunduma cikin harkar Siyasa tare da mika wuya ga dukkan bukatun Mahukunta ko kare Muradansu.

"Alamun hakan shine kawar da kai daga ko wani irin kuskure su ka aikata da yunkurin Yakar dukkan wanda ya furta gaskiya akan kurakuran da su ka bayyana a zahiri".

"Ku sani, Malamai na hakika sune wadanda aikinsu ke tabbatar da gaskiyar da Bakinsu ya furta, ba sa Kalamai da manufar Dadadawa wani ko 'Kuntatawa wani, sai domin isar da sakon Allah SW".
"Da haka su ke bambanta kansu da wadanda su ka dauki Duniya da abin cikinta abin alfaharinsu, kuma su ka mayar da Addinin Allah matakala dan kaiwa ga Muradansu ba dan maslahar al'umma ba".

Address

No17 Nata'Ala Road H/banki
Kaduna

Telephone

+2348033709851

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Halliru Maraya Forum posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Halliru Maraya Forum:

Share