22/05/2026
ABUBUWAN DA AKE SO MUSULMI YA YI A WADANANN KWANAKI GOMA NA ZUL-HIJJA
1. Duk wanda zai yi yankan layya, kada ya aske gashin kansa, kada kuma ya yanke farce har sai an yi babbar Sallah
2. Ana son musulmi su yawaita yin azumi a kwanaki na farkon watan Zul-Hijjah, saboda Annabi yakan azumci kwanaki tara na farkon watan Zul-Hijjah.
3. Ana son musulmi ya yawaita yin tasbihi, ma'ana yawaita fadin 'Allahu Akbar, wa Subhanallah, wal Hamdu liLlah'
4. Ana son wanda yake da hali ya yi yankan layya ranar goma ga watan.
5. Ana son a yawaita ba da sadaka 6. Ana son a yawaita karanta al-Kur'ani
7. Ana son a yawaita gaida marasa lafiya
8. Yin sulhu tsakanin musulmai
9. Da sauran ayyukan lada