26/09/2026
Widows Week of prayer 20/09/2026 ECWA Church Raku-belleng II
KOYARWA A KAN MAGANA:
GWAMRUWAR GASKE BISA GA KOYASWAR LITTAFI MAI TSARKI
NASSI: - I TIMOTAWUS 5:5-6, LUKA 2:36-38.
MAI GABATAR DA TAKARDA:
By
Dr. Mrs. Miriam Philip. BNSC, RN, RM, PHN/CHO, PAED/N, MELI, JP
GWAMRUWAR GASKE BISA GA KOYASWAR LITTAFI MAI TSARKI.
MANUFA
Domin a karfafa gwamraye su zama amintattun shaidun Kristi cikin gwamranci.
GABATARWA
Abubuwan da ke faruwa a kasarmu yau, da irin rayuwar zamanin da mu ke ciki da kuma irin abincin da mu ke ci ya sa akwai gwamraye masu yawan gaske a cikin kasa da kuma ikilisiya. A cikinsu akwai gwamrayen da suke cikin kuruciyarsu, ba su kai shekara talatin ba. Kuruciyar wasu gwamraye da kuma rashin ginuwa cikin Maganar Ubangiji ta sa wasu gwamraye Krista suna rayuwar rashin tsarki da adalci.
Ga alama akwai irin wadannan gwamruye a lokacin Manzo Bulus shi ya sa ya yi maganar a Timoti game da gwauruwar gaske da gwaururwa mai annashuwa. 1 Tim. 5:5-6: "Ita fa da take gwamruwar gaske mai zaman kadaici, begenta yana kafe ga Ubangiji tana nacewa da addu'a dare da rana. Amma ita wadda take maida hankali ga annashuwa matacciya ce tun tana da rai."
Manzo Bulus ya yi amfani da wasu kalmomi domin ya siffata gwamruwar gaske da mai annashuwa. Bari mu duba ma'anar kalmomin nan domin mu gane abin da ake nufi.
Gaske: Na gaskiya, na ainihi.
Gwamruwa: Matar da mijinta ya rasu kuma ba ta yi aure ba.
Kadai: Ba ta da kowa.
Dogara: Sa zuciya ga wani (a wannan hali Allah); mutum ya yadda cewa wani (wato Allah) yana da kyau, mai gaskiya, amintacce etc. A yarda da wani abu (a wannan yanayi, abin da Ubangiji ke fada game da dangantakarsa da gwamraye).
Gaskiya: Ce kuma daidai ne ko kuma zaka iya sa rai da shi.
Cigaba: A rika yin abu ba fasawa.
Roko: Hanyar neman abu cikin tawali'u ko addu'a.
Addu'a: Magana da Allah ta wurin yi masa yabo, godiya da roko.
Rayuwa: Kasancewa a raye, wato mutum ya bi da rayuwarsa ta wata tsarin da yake so.
Annashuwa: Rayuwar jin dadin jiki.
WADANSU GWAMRAYE A CIKIN LITTAFI MAI TSARKI
1. Tamar (Farawa 38:1-30)
2. Naomi da Ruth (Ruth 1)
3. Tekoah (II Samaila 14:1-24)
4. Mamar Hiram (I Sarakuna 7:14)
5. Zeruah (I Sarakuna 11:26)
6. Gwamruwar Zarephath (I Sarakuna 17:1-24)
7. Matar wani Annabi (2 Sarakuna 4:1-7)
8. Hannatu (Luka 2:36-37)
9. Gwamruwa matalauciya (Markus 12:42; Luka 21:2)
10. Gwamruwa ta Nayin (Luka 7:11-15)
11. Gwamruwar Mai roko (Luka 18:1-8)
12. Tabitha ko Dorcas (Ayyukan Manzanni 9:39-24)
Nazarin Rayuwar Anna
Luka 2:36-38 ya bamu labarin wata gwamruwa wadda take da halayen da Manzo Bulus ya yi magana. Bisa ga al'adun Yahudawa na da, an kyasta cewa Anna tana da shekara sha uku zuwa sha biyar lokacin da ta yi aure. Kuma bayan shekara bakwai da aure mijinta ya rasu.
Anna ta fara gwamrancinta tun ba ta kai shekara talatin ba. Ta yi zaman kadaici shekara tamanin da hudu, domin ba mu karanta tana da 'ya'ya ba. Duk da kuruciyarta, Anna ba ta yi zaman bakin ciki da jin tausayin kanta ba. Amma ta mika kanta ga Ubangiji, Shi wanda ya yi alkawari cewa shine maigidan gwamraye.
Cikin shekarun gwamrancinta ta maida haikalin Ubangiji wurin zamanta. Maganar Ubangiji ta nuna mana cewa ba ta taba barin haikali ba. Watau, dare da rana tana zaune cikin haikali tana hidimar Ubangiji. Anna ba ta da lokacin domin komitin abokai, zuwa jana'iza, daurin aure ko suna. Ta hada zamanta a haikali da azumi da addu'a da hidima.
Rayuwar Anna ya nuna mana cewa, rayuwar ibada da kamun kai, hade da azumi da addu'a wajibi ne ga duk mutumin da Ubangiji ya mora. Abin sha'awa ne mu lura cewa, azumi da addu'a da Anna ta dinga yi ba domin bukatun kanta ba ne, amma domin zuwan Almasihu ne.
Ta yi addu'a da bangaskiya da dogara ga Ubangiji cewa Maiceto zai zo. Kuma lokacin da aka haife shi ita kadai da Saminu ne s**a sami gatanci ganewa shine Almasihu da aka yi annabci a kai a cikin Maganar Ubangiji. A cikin rayuwar Anna mun ga gwauruwar gaske da ta fara gwamrancinta cikin kuruciyarta. Har ta tsufa bata fasa dogara ga Ubangiji ba, amma ta yi hidimarsa a haikali da azumi da addu'a dare da rana domin marmarin haihuwar Yesu.
Ba ta tsaya a addu'a da yabon Ubangiji da godiya domin haihuwar Yesu Almasihu kadai ba, amma mun karanta cewa ta tafi ta yi maganar haihuwarsa ga dukan masu sauraro a Urshalima. Sai mu ce ta yi aikin bishara.
Karbar Gwamrancinta
Me gwamraye za su koya daga rayuwar Anna gwamruwar gaske? Abin da gwamruwa za ta fara yi shine ta karbi Yesu ya zama Maicetonta da Ubangijinta. Wannan ne mataki na fari, ba zuwa ikilisiya ko zama yar zumunta mata ba.
Bayan tuba sai ta karbi gwamrancinta. Gwauruwar da ba ta karbi gwamrancinta ba tana zaman jin tausayin kanta da gunaguni, da dacin rai da dakorofi kowane lokaci. Kuma tana fushi da Ubangiji don ya yarda mijinta ya mutu.
Naomi, misalin irin wannan gwamruwa ce. Ta yi zaman kadaici sosai, musamman bayan mutuwar 'ya'yanta guda biyu. Mun ga fushinta da dacin ranta lokacin da ita da Ruth s**a kai Bethelehem.
Ga abin da ta ce ma masu tambayarta, "Kada ku ce da ni Na'omi, mara za ku ce da ni, gama Mai iko dukkaya yi mani aiki mai zafi kwarai, cike na rabu da wurin nan, hannu wofi kuma Ubangiji ya dawo da ni; domin me kuke kirana Na'omi, da shi ke Ubangiji ya nuna mani rashin yarda, Mai iko duka kuma ya kuntata ni?" (Ma'anar Naomi shine mai dadi, Mara kuma daci.)
A cikin dacin ranta Na'omi ba ta ankara cewa Ruth da ta bar garinta da al'adunta ta rungumi ita Na'omin da Ubangijinta albarkace ba. Bayan wannan ma ita da mijinta rashin biyayya s**a yi da s**a bar Baitalami s**a je Moab lokacin yunwa.
Gwamrayen Krista da yawa suna k**a da Na'omi, suna cike da dacin rai, suna zama cikin bakin ciki, ba su jin dadin kansu, ba su ganin 'ya'yansu da ikilisiyoyinsu albarka ne. Ba su yaba ma kowa ko wani abu. Suna rayuwar bakin ciki. Ba su da lafazi mai kyau. Duk lokacin da s**a yi magana mai ji zai san suna da damuwa. Su dai abin da suke so shine duniya ta tsaya tsit, ta saurare su.
Rayuwar Addu'a
Rayuwar addu'a da azumi irin na Anna abin da kowace gwamruwar Krista za ta koya ne. Ko da yake ba za ta zauna a cikin majami'a k**ar Anna ba, za ta iya mai da gidanta gidan addu'a maimakon zama da abokanta tana bada labarin wahalar da surukanta s**a ba ta, ko gulman membobin ikilisiya ke matan zumunta.
Mun karanta a Ayyukan Manzanni 12 cewa lokacin da malaikan Ubangiji ya fitar da Bitrus daga kurkuku ya tafi gidan wata gwauruwa, uwar John Mark, domin masu bin Yesu sun taru gidanta suna addu'a domin shi Bitrus.
Mu lura cewa, a wannan lokacin ana tsananta wa Krista sosai, amma ta yi kasada ta bude gidanta domin addu'a. Hakika, idan akwai wani lokaci da ya k**ata gwamraye su bude gidajensu domin addu'a yanzu ne.
Domin? Domin Ikkilisiyar Almasihu yau, ta biye ma zamanin nan, ta yi ridda, ga kuma tsanani da take fuskanta. Kasarmu kuma tana fuskantar matsaloli da yawa. Matasanmu fa? Sun zama kayan aikin da shaidan yake mora yana mugunta. Su ne masu fashi da makami, sune masu satan mutane, su ake haya su kashe mutane ko su tada zaune tsaye ma 'yan siyasa. Sune 'yan kwaya, 'yan kungiyar asiri, masu yaudara ta hanyoyi dabam dabam, suna zaman lalata ta dukkan fanni.
Babban abin bakin ciki game da 'ya'yanmu matasa shine sun fara kisan kai da kuma kashe junansu. Gwamruwar gaske k**ar Anna, za ta tara mutane su yi addu'a da kuka ga Ubangiji domin yanayin da kasarmu take ciki da kuma ikkilisiya da 'ya'yanmu matasa.
Gwamruwa mai koyi da Anna za ta zama mai addu'a da azumi kullayomi domin matsalolin gidanta, da na ikkilisiyarta, wurin aikinta da kuma musamman domin 'ya'yanta. Za ta yi addu'a domin dukkan fannin rayuwarsu: girmansu na ruhaniya, makarantarsu, wadanda zasu aura, gidajen wadanda s**a yi aure, wurin aikinsu da sauransu.
Idan tana da bukatar kudi domin biyan bukatun makarantarsu, za ta zo gaban Ubangiji fa gaba gadi ta fada masa bukatunta daya, daya. Zata mori Maganar Ubangiji ta yi addu'a k**ar haka, 'Ya Ubangiji maganarka ta ce kai ne Uban marayu da mai kare gwamruwa. 'Ya'yanka za su koma makaranta kuma suna da bukatar kudi domin litattafai, da kudin makaranta da uniform. Na zo gareka, kai ne ubansu. Ina rokonka ka taimake ni ka biya masu bukatunsu. Nagode, domin ka amsa addu'ata!'
Ba shakka Ubangiji zai amsa addu'ar nan, domin ba ta je roko wajen pastor da dattawa ko kuma wani ba, kafin ta je wurinsa.
In kuma tana da yaron da yana da kinji sosai, cikin azumi da addu'a za ta tuna ma Ubangiji maganarsa a Irmiya 49:11: 'Ubangiji kace ka bar marayunka, ni zan rayar da su, matan da mazansu sun mutu, sai su dogara gare ni.' Ina barin yaron nan (suna) a hannunka. Ina rokonka ka bashi sabuwar zuciya, ka kuma sa Ruhunka a cikinsa domin ya sake, ya zama abin da kake so ya zama.
GAFARTAWA
Mun gani cewa Anna gwauruwa ce da ta hori kanta, mai tsabtacciyar zuciya, ba ta da fushi, da dacin rai da hushi. Saboda haka, gwamruwar da take so ta zama gwauruwar gaske ta kuma mika kanta ga addu'a, dole ta zama tana da zuciyar gafara.
Dole ne ta gafarta wa dukan wadanda s**a yi mata laifi, musamman surukanta, domin addu'arta ta samu karbuwa wurin Ubangiji.
Gwamruwa mai gafartawa tana ce ma Ubangiji, ka yi yaki domina. Ubangiji kuwa zai mata yakin. Amma wadda ba ta gafara, tana ce ma Ubangiji, bana bukatarka, zan iya yin yakina da kai na. Shi kuwa zai nade hannusa ya barta ta yi ta wahala cikin bakin ciki.
Gwamraye idan kuna son salama da farin ciki, kuma Ubangiji ya yi yaki dominku, ina rokonku, ku zama masu gafartawa, masu barin kome ya wuce.
Ku tuna, Yesu ya ce a Matta 6:14-15, "Gama idan kuna gafarta ma mutane laifofinsu, Ubanku na sama kuma, zai gafarta muku, amma idan ba ku gafarta ma mutane laifofinsu, Ubanku kuma ba zai gafarta muku laifofi ba."
Kullum kuna addu'ar Ubangiji kuna cewa, "Ka gafarta laifofinmu k**ar yadda mu ke gafarta ma wadanda s**a yi mana laifi." To ku da ba ku gafara, da bakinku ku ke cewa, tun da ba mu gafarta ba, mu ma Ubangiji kada ka gafarta mana.
Masu bin Yesu da yawa da s**a mutu basu shiga mulkin sama ba domin rashin gafara. Gwamraye ina rokonku, kada ku kai kanku wutar jahannama don rashin gafara.
Ban da wannan yayin da ku ke a raye a duniya, addu'oinku hayaniya ne da surutu kawai a kunnen Ubangiji. Bugu da kari, rashin gafara yakan haifi fushi, dacin rai da haushi. Wadannan kuma su kan kawo cututtuka k**ar hawan jini, ciwon kai kowane lokaci, kullum cikin tashin hankali da rudewa, ciwon jiki har ma da ciwori cancer kansa da ciwon jiki.
SANIN MAGANAR UBANGIJI
Wajibi ne kowane mai bin Yesu ya san Maganar Ubangiji, domin Maganar Ubangiji tana cikin mak**an yaki da Ubangiji ya ba mu. Ubangijinmu Yesu Almasihu da kansa, da ita Ya yi yaki ya ci nasara da shaidan, lokacin da ya jarabce Shi.
Anna gwamruwa ce da ta san Maganar Ubangiji, shi ya sa ta san annabcin haihuwar Yesu, ta kuma mika kanta tana ibada da azumi da addu'a domin haihuwarsa.
Gwamruwar da ta san Maganar Ubangiji za ta san rayuwar da ya k**ata ita da 'ya'yanta su yi. Ba za su yi rayuwar annashuwa da shashanci ba. Tsoron Ubangiji zai sa ta yi nesa da zina da abubuwan sa maye. Za ta guji duk abin da ta sani zai bar ma 'ya'yanta mugun ambato.
Sanin Maganar Ubangiji zai taimake ta ta fahimta da abubuwan da ke faruwa a duniya yau, alamun karshen zamani ne: kisan kai, satar mutane, sabbin cututtukan da ake fama da su, ribar banza ta mugunta, rashin kiyaye doka, fadan kabilanci, tayarwar yara da kuma yadda mutum ya fi son kansa da Ubangiji da sauransu.
Ba za ta zauna da tsoro ko fargaba ba, amma za ta kara lizama cikin addu'a domin iyalinta, ta tabbatar sun karbi Yesu Maicetonsu, kuma sun shirya zuciyarsu suna zaman tsarki da adalci domin in an busa kaho su zama cikin wadanda za a fyauce. Wannan gwamruwa kuma za ta lura da dangantakarta da mutane.
WASU ALKAWARAN UBANGIJI GA GWAMRAYE DA MARAYU
1. Ba zaka kuntata ma kowace gwaruwa ba, ko maraya. Idan ka kuntata masu ko kadan, sun kwa yi mani kuka da ko kaka, hakika zan ji kukansu; fushi na kuma za ya kuna da zafi, zan kashe ku da takobi; matayenku fa za su zama gwamraye 'yayanku kuma marayu. (Fitowa 22:22-24)
2. Ita fa da take gwamruwar gaske mai jin kewa kuwa, begenta yana kafe bisa ga Allah, tana lizima cikin godo da addu'a dare da rana. (I Timothawus 5:5)
3. Kada ki ji tsoro gama ba za ki sha kunya ba, kada ki yi fargaba kuma; gama ba za a kunyata ki ba, gama za ki manta kunyar kuruciyarki, zargi na zaman gwamrancinki kuma, ba za ki kara tuna da shi ba. Gama mahalicinki shine mijinki, Ubangiji mai runduna shine sunansa: Mai-Tsarki na Isra'ila kuma shine mai fansar ki, za a ce da shi Allah na dukan duniya. Gama Ubangiji ya yi kiranki k**ar mata wadda an yashe ta, mai jin ciwo a ranta, mata mai kuruciya da aka kita kenan, in ji Allahnki. Dan lokaci kankani na yashe ki amma da jinkai mai-girma zan dawo da ke. A cikin hasala mai-zafi na boye maki fuskata dan lokaci kadan: amma da madawamin alheri zan yi maki jin kai, in ji Ubangiji mai fansar ki. (Ishaya 54:4-8)
4. Zan damra alkawalin aure dake har abada; cikin adalci da sharia da rahama, da jinkai, zan yi alkawali dake. (Hosea 2:19)
5. Ka yi sauraro ga Ubangiji: ka karfafa, ka bar zuciyata ta dauki karfin rai. (Zabura 27:14)
6. Ubangiji zai yi yaki dominku, ku yi shuru kawai. (Fitowa 14:14)
7. Na iya kaskanta, na kuma iya yalwata: a cikin kowace matsala, a cikin abu kuma, an bayyana mani in saba da koshi in saba da yunwa kuma, in yalwata in yi fatara kuma. Na iya yin abu duka a cikin wannan da yake karfafata. (Filibiyawa 4:12-13)
8. Wannene fa a cikin ku bisa ga alhininsa yana da iko ya kara ko kamu daya ga tsawonsa? Idan fa ba ku da iko ku yi ko abin da ya fi kankanta, don mi ku ke alhini a kan saura? Ku lura da fure fa girman da suke yi; basu kan yi wahala, basu kan yi kadi ba; amma duk da haka, ina ce muku ko Solomon cikin darajarsa duka baya yafa kaya k**ar guda dayansu ba. Amma idan Allah yakan yi wa ganyaye cikin saura sutura haka, abin da ke rayuwa yau, gobe ana jefawa cikin tanduru; b***e ku, ku masu kankantar bangaskiya? Kuma kada ku nemi abin da za ku ci da abin da za ku sha, kada ku yi zuciya biyu. Gama dukan wadannan abu al'umman duniya suna ta bida: amma Ubanku ya sani kuna bukatar wadannan abu. (Luka 12:22-30)
9. Sai ka bar mani marayunka ni ma in kiyaye ransu; bari kuma gwamrayenka su dogara gareni. (Irmiya 49:11).
10. Gama na san irin tunanin da ni ke tunaninku da su in ji Ubangiji, tunani na lafiya bana masifa ba domin in baku bege mai-kyau a karshe. Sa'an nan zaku kira gareni, ku tafi ku yi mani addu'a ni ma in jiku. Za ku neme ni, ku same ni kuma, lokacin da ku ke nemana da zuciya daya. (Irmiya 29:11-13).
11. Ka kira ni, ni ma sai in amsa maka, in nuna maka manya al'amura masu wuya wadanda ba ka sani ba. (Irmiya 33:3).
12. Gama shi da kansa ya ce, Dadai ba ni tauye maka ba, dadai kwa bani yashe kaba. Domin wannan fa gabagadi muna cewa Ubangiji mai-taimako na ne; ba zan ji tsoro ba; ina abin da mutum zai yi mani. (Ibraniyawa 13:5-6).
13. Uban marayu ne Allah cikin mazauninsa mai tsarki, mai yin shari'a ne kuma domin gwamraye. (Zabura 68:5)
Karshen Magana
Gwamruwa ta gaske ta yi amirci ga mijinta, ana girmamata saboda dangantakarta da sauran mutane. Ana kuwa shaidatta da kyau domin kyawawan ayyukanta. Ta horas da 'ya'yanta a hanya mai kyau, ta yi wa baki alheri, ta yi wa wasu Krista hidima cikin tawali'u, ta yi gudumawa ga wadanda ke cikin bukata, kuma a shirye take ta yi kyakkyawan aiki.
An shawarci kananan gwamraye su sake aure saboda kuruciya na iya kaisu ga lalata da tayi gaba da Kristi, kuma saboda hana ragwanci da yawon bin gidaje da tsegumi da shishigi suna fadin abin da bai k**ata ba. (I Timotawus 5:5-10). Saboda haka, an umurce kananan gwamraye da su sake yin aure su haifi yara, su kuma lura da gidansu, yin haka zai hana magabci ya sami hujjar magana akansu.
Na gode sosai da zarafin da kuka bani, da kauna mai yawa.
KORUS
1. Solo - Ya Yesu na
- Ya Maicetona
All Part (Answer) - Gyara bakina in zama mai fadin gaskiya...
Don zamanin nan mugun zamani ne, gyara baki na in zama mai fadin gaskiya.
2. Solo - Ya Yesu na
- Ya Maicetona
All Part (Answer) - Gyara ni, in zama gwamruwa ta gaskiya
Don zamanin nan mugun zamani ne, gyara ni in zama gwamruwa ta gaskiya.
A karshe, annabiya Anna ta iya rayuwar da tayi a haikali da kamun kai, da dogara ga Ubangiji da maganarsa domin ita gwamruwa mai albarka ce, "wadda ba ta karbi shawarar miyagu ba, ba ta tsaya a cikin tafarkin masu zunubi ba, ba ta zamna cikin mazamnin masu ba'a ba." (Zab. 1:1)
Amma jin dadinta shine cikin hidimar da take yi a haikali da azumi da addu'a dare da rana.
Idan kina so ki zama gwaruwar gaske, sai ki auna kanki da tambayoyin nan. Su wanene abokanki? Shawarar wa ki ke amfani da shi? Idan kina da bukata da matsaloli wurin wa ki ke zuwa? Kina da lokaci domin 'ya'yanki kuma su abokanki ne? Awa nawa cikin awowi ashirin da hudu na kowace rana ki ke amfani da shi domin addu'a da bincike Maganar Ubangiji? Yaya dangantakarki da surukanki yake? Kina fushi da su? Yaya dangantakar ki da 'yan ikkilisiyarki da makwabtan ki da wurin aikin ki ya ke? Akwai wani da ki ke gani ko wurin da ki ke zuwa a boye ko a asirce? Ubangiji ya san amsoshin dukan tambayoyin nan. Ba a yi masa ba'a, abin da kika shuka, shi za ki girbe.