04/09/2026
HARAMCIN MAGANA BA TARE DA ILIMI BA
KA BINCIKA KAFIN KA FAƊA — KA TABBATAR KAFIN KA YAƊA
Daya daga cikin manyan matsalolin wannan zamani shi ne mutum ya ji wata magana, sai ya gaggauta yaɗa ta ba tare da ya bincika gaskiyarta ba. Wasu kuma su yi magana a kan Al-Ƙur’ani, Hadisi, Halal da Haram, alhali ba su da cikakken ilimi a kan abin da suke magana a kai.
Musulunci ya yi tsananin gargadi a kan wannan hali bisa dalilai k**ar haka.
1️⃣ ALLAH YA HARAMTA BIYAR ABIN DA BA A DA ILIMI A KANSA
Allah سبحانه وتعالى Ya ce:
﴿وَلَا تَقْفُ مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ ۚ إِنَّ السَّمْعَ وَالْبَصَرَ وَالْفُؤَادَ كُلُّ أُولَٰئِكَ كَانَ عَنْهُ مَسْئُولًا﴾
“Kada kuma ka dinga bibiyar abin da ba ka da ilimi a kansa. Lalle ji da gani da zuciya, duk waɗannan sun za abin tambaya ne game da su.” (Suratul-Isrā’: 36)
Wannan aya tana koyar da musulmi cewa ba a yarda mutum ya yi magana bisa zato, jita-jita ko zato-zaton kansa ba.
Imam Ibn Kathir رحمه الله ya kawo daga Qatādah رحمه الله:
«لَا تَقُلْ رَأَيْتُ وَلَمْ تَرَ، وَسَمِعْتُ وَلَمْ تَسْمَعْ، وَعَلِمْتُ وَلَمْ تَعْلَمْ، فَإِنَّ اللَّهَ سَائِلُكَ عَنْ ذَلِكَ كُلِّهِ»
Ma’ana:
“Kada ka ce: Na gani alhali ba ka gani ba; na ji alhali ba ka ji ba; na sani alhali ba ka sani ba. Domin Allah zai tambaye ka game da dukkan wannan.”
2️⃣ ALLAH YA UMARCI MU DA TABBATAR DA LABARI
Allah سبحانه وتعالى Ya ce:
﴿يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنْ جَاءَكُمْ فَاسِقٌ بِنَبَإٍ فَتَبَيَّنُوا أَنْ تُصِيبُوا قَوْمًا بِجَهَالَةٍ فَتُصْبِحُوا عَلَىٰ مَا فَعَلْتُمْ نَادِمِينَ﴾
“Ya ku waɗanda s**a yi imani! Idan wani fasiƙi ya zo muku da wani labari, ku tabbatar da shi, kada ku cutar da wasu mutane saboda jahilci, sannan ku wayi gari kuna nadamar abin da kuka aikata.” (Suratul-Ḥujurāt: 6)
Saboda haka, idan aka kawo maka wani labari, musamman wanda zai iya jawo fitina, ƙiyayya, zargi ko ɓata mutuncin mutum, kada ka gaggauta yaɗa shi sai ka samu gaskiyar magana akan abun
3️⃣ IDAN BA KA SANI BA, KA TAMBAYI MASU ILIMI
Allah سبحانه وتعالى Ya ce:
﴿فَاسْأَلُوا أَهْلَ الذِّكْرِ إِنْ كُنْتُمْ لَا تَعْلَمُونَ﴾
“Ku tambayi ma’abota ilimi idan ba ku sani ba.”
(Suratun-Naḥl: 43)
Don haka, “Ban sani ba” ba abin kunya ba ne. Abin kunya shi ne mutum ya yi magana a kan abin da bai sani ba.
4️⃣ ANNABI ﷺ YA GARGADE MU DA YAƊA DUK ABIN DA MUKA JI
Annabi ﷺ ya ce:
«كَفَى بِالْمَرْءِ كَذِبًا أَنْ يُحَدِّثَ بِكُلِّ مَا سَمِعَ»
“Ya isa mutum ya kasance maƙaryaci idan yana ba da labarin duk abin da ya ji.”
(Sahih Muslim, Muqaddimah)
Mu lura: Annabi ﷺ bai ce dole mutum ya ƙirƙiri ƙarya ba kafin ya zama maƙaryaci. Ya gargade mu cewa yaɗa duk abin da mutum ya ji ba tare da tantancewa ba na iya kai shi cikin ƙarya.
Domin abin da ka ji zai iya zama ƙarya, kuskure, ƙari, ragewa ko kuma an fahimce shi ba daidai ba.
MENENE MUKE BUKATAR MU YI KAFIN MU YI MAGANA?
Kafin mu faɗi wani abu, musamman a kan addini ko wani :
① Mu tambayi kanmu: Shin mun san wannan?
② Idan hadisi ne: Shin hadisin sahihi ne?
③ Idan magana ce ta wani malami: Shin da gaske ya faɗe ta?
④ Idan fatawa ce: Shin akwai hujja daga Qur’ani da Sunnah?
⑤ Idan labari ne: Shin na tabbatar da shi?
⑥ Idan ban sani ba: Shin na shirya cewa “Ban sani ba”?
⑦ Idan akwai sabani tsakanin malamai: Kada ka gabatar da ra’ayinka k**ar shi ne ijma’i.
MI TUNA
Ba duk abin da ka ji ake faɗa ba.
Ba duk abin da aka rubuta ake yaɗawa ba.
Ba duk wanda ya yi magana yake da hujja ba.
Ba duk abin da ya yi k**a da hadisi ne hadisi ba.
Ba duk abin da aka danganta wa malami ne malamin ya faɗa ba.
SAƘO GA MASU YAƊA BAYANI BA TARE DA TABBACI BA
Masu yaɗa bayanai game da ɗan Sheikh Nuru Muhammad Khalid, wanda ake cewa ya koma addinin Kirista, ku ji tsoron Allah. Kada ku yaɗa abin da ba ku da cikakken ilimi ko tabbaci a kansa.
Abin da ya k**ata a fahimta shi ne: yaron ɗan Sheikh Nuru Muhammad Khalid ne, amma ba jikan Sheikh Ibrahim Bawa Mai Shinkafa رحمه الله ba ta fuskar uwa, domin ba ’yar Sheikh Ibrahim Bawa Mai Shinkafa ce ta haife shi ba, k**ar yadda wasu bayanai marasa tushe suke yaɗawa.
Saboda haka, muna kira ga kowa da kowa: a daina yaɗa jita-jita, a tabbatar da gaskiya kafin a wallafa ko a tura wani bayani.
Mu zamanto masu bincike kafin magana da tabbatarwa kafin yaɗawa, masu hujja akan abu kafin hukunci.
Saboda haka, idan ba ka da tabbaci akan abu , mafi aminci shi ne ka ce: “Ban sani ba, zan bincika.” Wannan ya fi ka faɗi abin da zai zama ƙarya, zalunci ko ɓatar da mutane.
Allah Ya shiryar da mu zuwa gaskiya, Ya kiyaye mu daga faɗin abin da ba mu sani ba, Ya kuma sa mu zama masu bincike da tabbatarwa kafin magana da yaɗawa. آمين.
Rubutawa: Sheik Ibrahim Bawa Mai Shinkafa Da'awah And Charity Foundation