19/08/2026
Yau ƴar takarar sanatan Filato ta arewa Mrs Ruth Bitrus ta kawo mun ziyara a garin Gana Ropp domin jajanta mana akan abubuwan da s**a faru acikin garin Gana da kewaye.
Acikin jawaban Madam Ruth Bitrus Mwantai ta yaba da ƙoƙarin Khalifan Tijjaniyya na jihar Filato Sheikh Ladan Gana akan aiyukan haɗin kai da wanzar da zaman lafiya a garin Gana Ropp da Barikin Ladi da jihar Filato bakiɗaya, Harma ta yaba da yadda Sheikh Ladan yake tafiyar da salon jagorancinsa wajen hulɗa da jama'a cikin salon dattaku ba tareda nuna banbancin yare, ƙabila ko addini ba, Mrs Ruth ta yaba wa al'ummar Gana Ropp kan yadda suke da haɗin kai musamman adaidai wannan lokacin da ake cikin halin ƙuncin rayuwa da tsadar rayuwa, Sannan ta roki Sheikh Ladan da ya ɗora akan aiyukansa na wanzar da zaman lafiya a jihar Filato.
Sheikh Ladan Gana ya yaba da yadda tazo ƙafa da ƙafa har garin Gana Ropp, Wannan yana nuni da yadda take ƙoƙarin haɗa kan al'ummar Filato cikin salon rarrashi da jinƙai. Allah yasaka mata da alheri, Allah ya biya mata buƙatun ta na alheri 🙏
✍️ Sheikh Ladan Gana
👳 Chief Imam Gana Ropp
📿 Khalifan Tijjaniyya Plateau State
🫂 Peace Ambassador