Samarin faira Jama'are Tv

Samarin faira Jama'are Tv Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Samarin faira Jama'are Tv, Religious Center, unguwar horare jama'are, Jama'are.

MUN ZAMA KAMAR YAN IZALA******Kafin bayyanar izala, malamai suna da tsarin ilimantar da ɗalibai, komi kaifin basirar ɗal...
01/06/2026

MUN ZAMA KAMAR YAN IZALA
*
**
***
Kafin bayyanar izala, malamai suna da tsarin ilimantar da ɗalibai, komi kaifin basirar ɗalibi dole daga ƙawa'idi zai fara karatun fiqihu, fannin hadisi kuma daga Arba'una, haka-haka dai, amma bayyanar izala sai suke tsallake matakan farko, suna zuwa sama kai tsaye, sai ya zamanto suna karatu amma babu fahimta ƙwaƙƙwara.

To haka matasan mu na faidha s**a zama a yau, a da can in muridi ya karɓi Tijjaniyya, to za a ilimantar dashi hukunce-hukunce da ladubban Ɗariƙa kafin ya shiga babin tarbiyya, duk da dai akwai muƙaddamai masu ƙarfin sirri wayanda suke iya shigar da muridi babin tarbiyya ba tareda ya jima da karbar Tijjaniyya ba, kuma zaka same shi lafiya lau, saboda suna kula da shi a zahiri da baɗini.

A yau sai ka ga muridi iri na kai tsaye ya kinkimo Jawãhirul Ma'aniy ko Rasa'il ko Riyadut Tafsir da wanin haka yana kokuwa da ita, a haka kuma zai ce shi masani ne a Tijjaniyya har ma zai iya bada fatawa ko jayayya da jagororin cikin ta ba tareda ya karanta littattafan sharar fage ba, yana gani kamar ai yafi ƙarfin ƙananan litattafai, bai san a cikin su sirrin fahimtar manyan litattafan suke ba, shiyasa za kaga wanda ya karanta Ruhul Adab da kyau ya fishi kyautata mu'amala da ladabi.

Lokaci yayi da za mu daina yaudarar kan mu, tabbas neman ilimi a kan mu dole ne a Tijjaniyya, amma neman ilimin yana da tsari da mataki, mu nemi sanin matakan neman ilimi don mu riski haske da albarkan dake ciki.

Mu guji rungomu tsarin wancan zawiyyar muddin shehin mu baya yi, misali TARIƘIYYA, yadda zawiyyar ku suke yi ba lallai bane ya zama daidai da wancan zawiyyar, ka bar su da nasu, ka riƙe naka, idan Allah yaso fahimtar da kai sirrin Faidha, kallon ƙuda kawai za kayi ka samu dukkan taraƙi, haka nan fannin karanta littattafan sufanci, ka bi tsarin da shehin ka yake kai, kar kace ai wancan zawiyyar kaza suke karantawa bayan sun yi kaza, in ma kuma dole kana son yin abinda suke yi na taraƙi ko karatu, ka nemi iznin shehin ka tukunna.

KA GA DA

27/05/2026

Maulana sheikh TIJJANI MURABBI AZARE RTA yake gaisawa da masoya bayan sallar idin sallar lahiya a babban masallacin idin garin azare katagum jihar Bauchi.
27/05/2026
Allah ƙarawa shehi lafiya.
Allah maimaita mana

Sheikhu Ibrahim Niasse RTA yana faɗa a Ranar Arafah a Hajjinsa ta biyu a shekarar 1370Hijriyyahوَقَفْتُ يَوْمَ الثُّلَاث...
26/05/2026

Sheikhu Ibrahim Niasse RTA yana faɗa a Ranar Arafah a Hajjinsa ta biyu a shekarar 1370Hijriyyah

وَقَفْتُ يَوْمَ الثُّلَاثَاءِ بِعَرَفهْ :: أَذْكُرُ رَبِّي ذِكْرَ عَبْدٍ عَرَفَهْ

“Na tsaya ranar Talata a filin Arafah, ina ambaton Ubangijina irin ambaton bawan da ya san Ubangijinsa.”

دَعَوْتُ لِلنَّفْسِ وَلِلْإِخْوَانِ :: وَلِلزَّمَانِ بَلْ وَلِلْمَكَانِ

“Na yi addu’a ga kaina da kuma ‘yan’uwa; har ma ga zamani da wurare baki ɗaya.”

نَزَلَ رَبِّي لِيُبَاهِي الْمَلَا :: بِمَلَإِ الْحَجِّ وَحِينَ نَزَلَا

“Ubangijina Ya sauko domin Ya yi alfahari da mahajjata a gaban mala’iku a lokacin saukar rahama.”

قَالَ أَفِيضُوا فَالذُّنُوبُ غُفِرَتْ :: لِكُلُّكُمْ كَذَا الْعُيُوبُ سُتِرَتْ

“Ya ce: Ku gangaro (daga Arafah), domin an gafarta zunubanku gaba ɗaya, kuma an lullube aibobinku.”

شُعْثًا وَغُبْرًا جِئْتُمُونِي الْيَوْمَا :: أَعْتَقْتُكُمْ، لَا ذَنْبَ بَلْ لَا لَوْمَا

“Kun zo gare Ni cikin ƙura da wahala; Na ‘yanta ku yau, babu zunubi a kanku, babu ma abin zargi.”

وَعِنْدَ ذَا تَنَفَّسَ الْكَبِيرُ :: وَرَفَعَ الْبَلَا الْعَلِيُّ الْقَدِيرُ

“A wannan lokaci ne Allah Sarki Babba ya saukar da wata irin Rahama, kuma Maɗaukakin Mai iko Ya ɗauke bala’i.”

قَدْ فَازَ أَحْبَابِي مَدَى الْأَزْمَانِ :: تَفَضُّلًا وَعْدًا مِنَ الرَّحْمَانِ

“Masoyana sun rabauta har abada, wannan kuwa baiwa ce da alƙawari daga Mai Rahama.”

كَأَنَّنِي فِي حَضْرَةِ الدَّيَّانِ :: أَنُوبُ عَنْ وَقْتِي وَعَنْ مَكَانِي

“Kamar ina tsaye ne a gaban Allah Mai sakamako, ina wakiltar mutanen zamanina da garina.”

فَافْتَقَرَ الْكُلُّ إِلَى الْكُلِّ فَحَقَّ :: إِجَابَتِي إِذْ كَانَ سَحْقٌ وَمَحَقْ

“Dukkan halittu s**a bayyana talaucinsu ga Allah Maɗaukaki; saboda haka amsar addu’ata ta tabbata yayin da komai ya shuɗe a gaban girmanSa.”

وَدُكَّتِ الْجِبَالُ إِذْ أَتَيْتُ :: وَجِئْتُهُ وَإِنَّنِي مَا جِئْتُ

“Duwatsu s**a ratsantsane lokacin da na zo gare Shi; na zo gare Shi, alhali a haƙiƙa ni ba ni ne na zo da ƙarfina ba.”

(Wato: komai da taimakon Allah ne, ba da ikon kai ba.)

فَقَالَ لِي مُبَاسِطًا: خُذْ مَا تَرَى :: فَقُلْتُ: يَا كَعْبَةَ قَلْبِي، مَا أَرَى

“Sai Ya ce mini cikin kusanci da tausasawa: ‘Karɓi abin da kake gani.’ Sai na ce: ‘Ya Ka’abar zuciyata! Ni dai ban ga wani abu ba.’”

وَاللَّهِ لَا أَرَى، وَلَا أَرَى، وَلَا :: أُرِيدُ شَيْئًا إِذْ أَطَلْتَ الْمَقُولَا

“Wallahi ban ga komai ba, ban ga komai ba; kuma ba na son wani abu, tun da Kai Ka bayyana mini da zancenKa.”

(Wato ya nutse cikin shuhudi da soyayyar Allah har bai ga wani abu ba face Shi.)

فَقَدْتُ نَفْسِي، وَفَقَدْتُ الْكِلَا :: فَصَارَ مِنِّي وَارِدِي لَا حَوْلَا

“Na rasa kaina, na rasa komai nawa; abin da yake gangarowa cikin zuciyata ya zama daga Allah ne kawai, babu wani ƙarfi nawa na kai na.”

كُوْنِي خَدِيمَ الْمُصْطَفَى الْعَدْنَانِي :: لَيْسَ بِمُحْتَاجٍ إِلَى بُرْهَانِ

“Kasancewata Khadimin Abin zaɓi ﷺ (Manzon Allah ﷺ ) ɗan zuriyar Adnani ba ya buƙatar wata hujja.”

Wannan baiti na ƙarshe yana nuna cewa mafi girman daraja a wurinsa ita ce hidima ga Annabi ﷺ, kuma wannan ita ce hujjar samun irin kusancinsa da Allah.

©️Aliyu Uthman Bashir

KUƊUBUL MAKHTUM,KATIMUL MUHAMMADIY.cikamakin waliyyan Allah kwa'ta,kakaf ɗin su shine Shehu Ahmadu TIJJANI rta.kamar All...
26/05/2026

KUƊUBUL MAKHTUM,KATIMUL MUHAMMADIY.
cikamakin waliyyan Allah kwa'ta,kakaf ɗin su shine Shehu Ahmadu TIJJANI rta.kamar Allah bazai ƙara aiko da wani Manzo ba,kuma ya riga ya zartar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama shi ne cikamakin Annabawa A.S. haka Allah ta'ala ya riga ya zartar Shehu TIJJANI shi ne kuɗubul MAKHTUM KATIMUL MUHAMMADIY, shi ne cikamakin waliyyan Allah baki ɗayan su.Duk waliyin da Zai bayyana awannan zamanin babu Wanda zai sake zuwa da Wata Ɗariqa wacce zata sadar da bayi zuwa ga Allah Sai dai yazo yabi SHEHU TIJJANI rta,Yadda sahihul faida,Gausuz zamani,shehul Islam Alhaji Ibrahim nyass yazo yabi SHEHU TIJJANI,ya ishe karatu har zuwa ranar busa kaho.
shifa muƙamin SHEHU TIJJANI RTA ba maganar nasaba bace kace jinin gidan annabta bane, a'a tun ba'a halicci Adamu da Hauwa ba, ba'a ma tsara za'a yi annabta da manzanci ba.tun Babu al'arshi,babu kursiyyu.shehu TIJJANI RTA yake shugaban waliyyan Allah Shehu TIJJANI RTA Neman Allah yabaka kujerar sa haramun ne, yana jawowa hallaka ga Mutum Ko aljani Kai kowacce Irin alam ma.wannan maganar ka yarda ko karka yarda.shehu Ahmadu TIJJANI RTA shine kuɗubul MAKHTUM, KATIMUL MUHAMMADIY.Allah Sanya SHEHU TIJJANI namu,muma muzama nasa. 🖊️ ALIYU TAMASINI JAMA'ARE. https://www.facebook.com/share/1MapF7qXzC/

24/05/2026

Allah ka iyar Mana lamuran alfarmar SHEHU TIJJANI RTA

Yan Shi'a sun jima suna ta kokarin yin karya da yaudarar mutane cewa Shehu Tijjani na Tawasali da Imamai 12, kamar yanda...
23/05/2026

Yan Shi'a sun jima suna ta kokarin yin karya da yaudarar mutane cewa Shehu Tijjani na Tawasali da Imamai 12, kamar yanda nasha fada maku Tawasali da imaman ba wani laifi bane ga wanda bai san komai acikin hakin hadaran Allah ba, amma wannan karyan da sukewa Shehu Tijjani ya kamata su yi akuri su waye kuma su fahimci gari ya waye an fahimci damuwar su.

Basuda wata mafaka sai littain : أحزاب وأوراد

Inda Shehu Muhammad Al-Hazif Al- Misri ya kawo : النر جسة العنبرية
Ta سيدي إبراهيم الرياحي التونسي da aykin العربي بن السائح

Bayan ya kawo salatin سيد إبراهيم الر ياحي التونسي
Sai ya karasa da ta العربي بن السائح

Amma a kasa sai yace maka : وقد بلغنا عن مشايخنا الثقات أنه ألفها قبل أن يأخذ الطريقة التجانية

Wato sunyi tane tun kafin su zama Tijjanawa, domin ya nuna maka cewa komai tana da hakin sa da doka da ka'ida, sai ya takaita akan السيدة زينب Damon tsayawa kan sahaban Annabi wanda yace itama tana cikin su.

Zai kyautu idan yaudaran ka akayi ka chaza tunanin ka kafin ka fada cikin assarar duniya da kiyama.

Note: Tawasali dasu ba komai bane, amma yiwa Shehu Tijjani shari ba sai ta nan zaku biyo ba.

Tijjanawa sune iyalan gidan Annabi, kuma bawata firka da ta kaisu wayan " Sidi" mun godewa Manzan Allah { s a w}.

Shehu Tijjani ya wadaci komai, shi yasa Shehu ke cewa : هذا الذى منه أرجو كل اونة... نيل ٱلفتوح وتسهيل ٱلمرامات

Kaga wannan Shehu Tijjani, agurin sa nike niman duk wani abun nima, na daga fatahi da bukace bukace na.

Malan Ridwan

21/05/2026

MUHAMMADU RASULULLAH SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA

19/05/2026

Lokacin da Maulana shehin azare yake karɓar gaisuwa daga Alhaji Rabi'u taka lafiya Sarkin yaƙin Faira.

NA'ANA'A :DR.ALIYU DALHATU07034925929SAKATAREN MASU BADA MAGUNGUNAN GARGAJIYA(NANTMP)JAMA'ARE BAUCHI STATE.Na'ana'a Wato...
25/10/2025

NA'ANA'A :

DR.ALIYU DALHATU
07034925929
SAKATAREN MASU BADA MAGUNGUNAN GARGAJIYA(NANTMP)
JAMA'ARE BAUCHI STATE.

Na'ana'a Wato (Mint life a Turance)
Wani Ganyen Mai Albarka Dake dauke da Manyan Sana daran Inganta lafiyar Dan Adam

Ana Samun Na'ana'a Mafitan Qasashen Duniya Ci Har da Qasar mu

GA KADAN DAGA CIKIN AFANIN NA'ANA'A:

1-ASMA:
Shan Shayin Ganyen Na'ana'a Lokaci-lokaci Yana Maganin Ciwon Asma

2+ MURA:
Ayi Shayin Ganyen Na'ana'a da danyar Citta zaa Sami Lafiya

3-(SLIMING RAGE QIBA) RAGE KITSE MARA KYAU A JIKI:

Ariqa Yin Shayin Ganyen Na'ana'a ana sa Lemun Tsami Zaa Rage Giba Mara Amfani

4-KUMBURIN CIKI:

Shan Shayin Ganyen Na'ana'a na Magance Matsalolin Ciki Musamman Kumburin Ciki

5-KWAKWALWA:

Shan Shayin Ganyen Na'ana'a Yana Wanke Kwakwalwa daga Chushewa

6-DANDANO:

Wanda Ya Rasa Dandano Sakamakon Wani Ciwo da yayi Ko Hakanan Kawai
Yasha Shayin Ganyen Na'ana'a Dandano sa Zai dawo

7-HAQORA:

Shan Shayin Ganyen Na'ana'a Yana Qara Lafiyar Haqora da Qarfin su

8-SHAWARA ( FEVER):

Shayin Na'ana'a na Maganin Shawara

9-IDANU:

Shan Shayin Ganyen Na'ana'a Na Qara Lafiyar Ido da Qarfin Gani da Hasken Ido

10-MAI JUNA 2:

I Dan Macce Na Laulayi Shan Shayin Ganyen Na'ana'a Zai Taimaka mata Sosai
Wajen Qarfafa jikin ta Wajen Qara mata Kuzari da Saita mata Dandanun Bakin ta

11-MAI SHAYARWA:

Shan Shayin Ganyen Na'ana'a Yana Qara Ruwan Nono

12-FATA:

Shan Shayin Ganyen Na'ana'a Yana Kawar da Cututtukan Fata Ya SATA Sheqi da Hasken

13-NUFASHI:

Shan Shayin Ganyen Na'ana'a Na Inganta Lafiyar Huhun Dan Adam Wajen Kawar Mishi Da Cututtukan Dake Huhun shi da Qara Mishi dadin Numfashi

14-MAQOGWARO:

Shan Shayin Ganyen Na'ana'a da Kanumfari na Magance Matsalolin Maqogoro
Zaku iya garzayawa shagunan Islamic domin samun Ganyen da man Na'a Na'a

Allah yayi mana Jagora
07034925929

Address

Unguwar Horare Jama'are
Jama'are

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Samarin faira Jama'are Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share