TFS Islamic Channel

TFS Islamic Channel wannan Channel mai suna TFS wato Tadbiƙu Ilmus Salaf an ƙirƙire shi ne don wayar da kan al'umma game

31/08/2026

LALLE MUNAFUKAI FITINA NE GA ADDINI

Abdullahi bin Ubayyi bin Salul Shugaban munafikai, wanda ya yi wa Matar Annabi ƙazafin zina, har ma a ka samu wasu daga cikin Musulmai s**a fitinu da shi, s**a ringa yaɗa wannan magana a cikin garin Madina. Wannan waƙi'ar ta ƙage ta haifar da fitina, kuma ta janyo cece-ku-ce da jayayya tsakanin Muminai musamman ƙabilun garin Madina wato Aus da Khazraj.
Allah Maɗaukaki cikin tausasawarSa Ya sauƙar da Ayoyi da suke wanke Matar Annabi daga, wannan kagen da la'anannu, tsinannu kuma munafikai s**a yi mata. Allah Maɗaukakin Sarki cikin Suratun Nur, Ya ce:
إِنَّ ٱلَّذِينَ جَآءُو بِٱلۡإِفۡكِ عُصۡبَةٞ مِّنكُمۡۚ لَا تَحۡسَبُوهُ شَرّٗا لَّكُمۖ بَلۡ هُوَ خَيۡرٞ لَّكُمۡۚ لِكُلِّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُم مَّا ٱكۡتَسَبَ مِنَ ٱلۡإِثۡمِۚ وَٱلَّذِي تَوَلَّىٰ كِبۡرَهُۥ مِنۡهُمۡ لَهُۥ عَذَابٌ عَظِيمٞ (11) لَّوۡلَآ إِذۡ سَمِعۡتُمُوهُ ظَنَّ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتُ بِأَنفُسِهِمۡ خَيۡرٗا وَقَالُواْ هَٰذَآ إِفۡكٞ مُّبِينٞ (12) لَّوۡلَا جَآءُو عَلَيۡهِ بِأَرۡبَعَةِ شُهَدَآءَۚ فَإِذۡ لَمۡ يَأۡتُواْ بِٱلشُّهَدَآءِ فَأُوْلَٰٓئِكَ عِندَ ٱللَّهِ هُمُ ٱلۡكَٰذِبُونَ (13) وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِ لَمَسَّكُمۡ فِي مَآ أَفَضۡتُمۡ فِيهِ عَذَابٌ عَظِيمٌ (14) إِذۡ تَلَقَّوۡنَهُۥ بِأَلۡسِنَتِكُمۡ وَتَقُولُونَ بِأَفۡوَاهِكُم مَّا لَيۡسَ لَكُم بِهِۦ عِلۡمٞ وَتَحۡسَبُونَهُۥ هَيِّنٗا وَهُوَ عِندَ ٱللَّهِ عَظِيمٞ (15) وَلَوۡلَآ إِذۡ سَمِعۡتُمُوهُ قُلۡتُم مَّا يَكُونُ لَنَآ أَن نَّتَكَلَّمَ بِهَٰذَا سُبۡحَٰنَكَ هَٰذَا بُهۡتَٰنٌ عَظِيمٞ (16) يَعِظُكُمُ ٱللَّهُ أَن تَعُودُواْ لِمِثۡلِهِۦٓ أَبَدًا إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ (17) وَيُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمُ ٱلۡأٓيَٰتِۚ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ (18) إِنَّ ٱلَّذِينَ يُحِبُّونَ أَن تَشِيعَ ٱلۡفَٰحِشَةُ فِي ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَهُمۡ عَذَابٌ أَلِيمٞ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ (19) وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ وَأَنَّ ٱللَّهَ رَءُوفٞ رَّحِيمٞ (20)

Dukkanin Musulmi, ya yarda da wannan Ayoyi kuma ya yi Allah wadai da irin abin da munafukai s**a aikata na yi wa Iyalin Annabi ƙage, amma jikokin Abdullahi bin Ubayyi bin Salul wato shi'a suna kan bakansu na yaɗa wannan ƙarairayin da ƙage, wadda Allah Ya riga Ya kuɓutar da ita daga wannan maganar.

Binyamin Aliyu Assalafi

20/08/2026
20/08/2026
27/07/2026

BA A YI UMURNIN A YABI ANNABI A CIKIN WAƘA BA TOH AMMA KUMA BA A HANA BA:

1. Babu inda Shari'ar Musulunci ta yi umurnin a yabi Annabi mai tsira da amincin Allah a cikin waƙa, babu irin wannan nassin a cikin Wahyin Alƙur'ani ko cikin Wahyin Hadithi ingantacce; wannan shi ne ma ya sa babu wata ƙasida da Abubakar ya yi, ko Umar ya yi, ko Uthman ya yi, ko Aliyyu ya yi domin kawai yabon Annabi mai tsira da amincin Allah.

2. Toh amman Allah Maɗaukakin Sarki Ya yi umurnin a yi wa Annabi mai tsira da amincin Allah salati, kuma Annabi shi ma ya yi umurnin a yi masa salatin, ya kuma koya wa al’ummar Duniya yadda za a yi masa salatin, kuma babu sigar salatil Fatihi a cikin sigogin salatan da ya koya wa al’ummarsa.

3. Toh amma Annabi bai haramta a yabe shi ko a yabi waninsa a cikin waƙa ba matuƙar dai babu saba wa Shari’ar Musulunci a cikin lafuzan waƙar. Wannan shi ne ya sa Sahabi Hassan Bin Thaabit ya yabe shi ya kuma yabi Sahabbansa a cikin ƙasidu da yawa, kuma shi ne ya sa Sahabi Ka'ab Bin Zuhair Bin Abi Sulmaa ya yabi Annabi har ma Annabin ya ba shi kyautar wani mayafi na lullunɓa, ya yabe shi a cikin mashhuuriyar ƙasidarsa:
بانت سعاد فقلبي اليوم متبول && متيم اثرها لم يفد مكبول
وما سعاد غداة البين اذ ظعنوا && الا اغن غضيض الطرف مكحول

4. Amma Annabi mai tsira da amincin Allah ya ba wa Hassan umurnin ya mayar da martani mai zafin gaske a cikin waƙoƙinsa a kan mushurukai masu yi wa Annabi da Musulunci da Sahabbai sharri da yarfe.

Address

Jalingo
660213

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when TFS Islamic Channel posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share