Sunnah Media Taraba

Sunnah Media Taraba Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Sunnah Media Taraba, Religious Center, Jalingo.

SIYAN LITTAFAI...Yanzu littafai sun yi tsada matuƙa, ga shi kuma yawancin ɗalibai ba su da kuɗi, kuma lallai buƙatar ɗal...
23/09/2024

SIYAN LITTAFAI...

Yanzu littafai sun yi tsada matuƙa, ga shi kuma yawancin ɗalibai ba su da kuɗi, kuma lallai buƙatar ɗalibai ga littafai tana cikin buƙatu masu girma in ma ba su kai ga larura ba, kamar abinci da tufafi da wurin zama ba. To yanzu meye abin yi a irin wannan yanayi ? Abin da ya kamata ko wane ɗalibi yanzu ya maida hankali a kansa shine kamar haka :

1- Ka fara da siyan littafan ɗaukar karatu a gaban malami tukun, a kowanne fanni na ilmi ka yi ƙoƙari ka ga ka siya littafan da ake koyon ilimin da su a gaban malamai, ko da ba ka zo fannin ba, ka ga da ka zo ba ka da matsala.

2- Ka siya sharhohin waɗancan littafan, amma ka tabbatar ka shawarci malaminka ko wani masanin fannin kafin ka siya, kar kawai ka ga bango ko bugu ya burge ka ka siyo.

3- Ka fi mayar da hankali wurin siyan littafan magabata, musamman dukkan wani malami da ka ji ana faɗar sa da ya rayu kafin shekara ta dubu ɗaya bayan hijira a kowanne fanni waɗannan littafansu galibi masu amfani ne.

4- Kar ka siya littafin malamin zamani sai wanda ka tabbatar da ƙwarewarsa a fannin da yayi rubutu, da kuma tahƙiƙinsa ga mas'aloli na ilimi kuma wanda ya shahara cikin malamai da nagartar ilimi da tsoron Allah da zurfin ilimi. Za ka san haka ne ta hanyar shawartar malamanka da na gaba da kai a karatu kafin ka sayi littafi.

5- Bincikar mafi kyawun bugun littafi da ake samu kafin ka siya, don kar ka siyo littafi mara kyan bugu da kuma yawan kusakuran tahƙiƙi da na ɗab'i, hakan zai iya jefa ka cikin matsaloli masu yawa a farkon lamari.

6- Ka guji littafan raddi a farkon lamarin neman iliminka, ka fi mayar da hankali wurin littafan ilimi da s**a tara fa'idoji masu amfanarwa ga ɗalibai.

7- Ka fi bada ƙarfi wurin siyan littafan da suke damuwa da ta'asili na ilimi sama da mayar da hankali da yawa wurin ambato saɓanin malamai da yawan kawo ta'alilat ɗin da ba lallai su amfani ɗalibi ba, musamman a littafan Luga, da Fiƙhu, da Musɗalah, da Usul da Ƙira'at.

8- Kar ka damu da sai ka siya littafai masu yawan mujalladai don a ga kai ma ɗin ba dama. Ka fi mayar da hankali da damuwa da kyawun bugu kawai, wasu littafai za ka samu bugun su mai mujalladi ɗaya ya fi mai mujalladai biyunsu, ko ukunsu, ko huɗu ko biyar kyau, kawai an yi wancan bugun ne don a nemi kuɗi ba don amfanar da ɗalibai ba. Don haka kar yawan mujalladai ya ruɗe ka, ba a nan take ba.

9- Akwai malaman da kana iya cewa duk littafansu suna da fa'ida sosai a kowanne babi s**a yi rubutu, ka yi ƙoƙarin sanin su daga malamanka domin ka mallaki littafansu, kamar kusan dukkan malaman da s**a yi rubutu a ƙarni na biyu, da na uku, da kuma irin su Ibn Al-jauziy, da Nawawi, da Ibn Taimiyya, da Ibn Al-ƙayyim, da Ibn Hajar, da Suyuɗi( a fannonin ulumul ala) da Ibn Malik, da Ibn Hisham, da Ibn Abdilbarri, da malamai da yawa ire-irensu masu gogaye a fannoni ko a fannin da s**a shahara.

10- A ƙarshe kuma a dage da rage zafi da Pdf's in littafan sun ƙi samuwa, kuma a riƙa haƙurin karantawa ko ba daɗi a daure. Kuma ko ba yawa a riƙa budget na Littafai ko da duk wata ne, kuma abu mai muhimmanci a riƙa shawartar malamai da magabata a harkar ilimi don sanin mafiya kyawan littafan da ya kamata ɗalibi ya siya.

20/09/2024

Address

Jalingo

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sunnah Media Taraba posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share