Jibwis Ingawa

Jibwis Ingawa For the propagating sunnah of the holy prophet

Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta Jihar Katsina ta bada umarnin gabatar da Al-Qunut a faɗin jihar ...
29/06/2026

Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta Jihar Katsina ta bada umarnin gabatar da Al-Qunut a faɗin jihar Katsina

A yau, Lahadi 13 Muharram 1448H, wanda ya yi daidai da 28 ga Yuni, 2026, Majalisar zartaswa ta Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta Jihar Katsina ta gudanar da muhimmin taro domin nazarin halin da ake ciki a jiha Katsina tare da ɗaukar matakan da s**a dace wajen samar da mafita mai ɗorewa ga ƙalubalen da al'umma ke fuskanta.

Da yake gabatar da jawabin buɗe taron, Shugaban Kungiyar na Jihar Katsina, Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan Katsina (Sautus-Sunnah), ya fara da godiya ga Allah (S.W.T) bisa ni'ima da amincewar shi ya haɗa fuskokin mu a daidai wannan lokaci domin tattaunawa akan abinda ya shafi da'awa. Ina roƙon Allah ya sanya albarka da nasara a cikin wannan zama da za mu gudanar.

Ya kara da bayyana cewa manufar kiran wannan taron ita ce tattauna manyan matsalolin da s**a addabi al'umma, musamman matsalar rashin tsaro da taɓarɓarewar tarbiyya, tare da tsara hanyoyin da za su taimaka wajen samun mafita bisa koyarwar Al-Qur'ani da Sunnah.

Shugaban ya kuma yi ishara da taron da Gwamnatin Jihar Katsina ta kira shugabannin ƙungiyoyin addini da malamai domin neman shawarwari kan hanyoyin magance matsalar rashin tsaro da tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Bayan dogon nazari, Majalisar ta bayyana cewa Allah (S.W.T) ya h**e wa al'umma matasa masu ƙwazo waɗanda za su iya taka muhimmiyar rawa wajen shiryar da jama'a, dawo da kyawawan ɗabi'u, yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, da kuma magance matsalar badala.

Majalisar ta kuma jaddada cewa gyaran al'umma ba zai cika ba sai an samar da shugabanci nagari. Saboda haka, ta ƙarfafa mambobinta da sauran al'umma su shiga cikin harkokin siyasa domin samar da shugabanni na gari tun daga matakin farko, domin a samu jagoranci nagari a jihar da ƙasa baki ɗaya.

Da wannan ne ne aka amince da aiwatar da wani shiri na dogon zango da zai mayar da hankali kan wayar da kan al'umma, gina tarbiyya, da ƙarfafa shugabanci nagari.

Shirin zai mayar da hankali kan:
1. Gina ilimi a matsayin jigon addini da zaman lafiya.

2. Fahimtar al'amuran zamani bisa koyarwar Musulunci (Fiqhul Waqi').

3. Hada karfi da karfe domin magance matsalolin da su ke fuskantar wannan al-umma

4. Gina tarbiyya da ƙarfafa imani ga matasa.

5. Kira zuwa ga tuba da komawa ga Allah.

6. Wayar da kai kan haƙƙoƙin makwabtaka da zamantakewa a tsakanin al'umma.

Sakamakon da ake sa ran cimmawa ya haɗa da:
1. Ƙara fahimtar koyarwar musulunci kan shugabanci, zamantakewa da amana.

2. Gina al'umma mai haɗin kai da kyawawan ɗabi'u.

3. Samar da hanyoyin magance matsalolin matasa, iyalai da zamantakewa.

4. Ƙarfafa zaman lafiya da sake haɗa kan al'umma.

Maudu'an farko da za a gabatar sun haɗa da:

1. Muhimmancin kishin ƙasa da rawar da ake takawa wajen gina al'umma.

2. Gudummawar mutanen kirki a harkokin siyasa da wajabcin shiga domin gyaran al'umma.

3. Matsalolin taɓarɓarewar tarbiyyar matasa da hanyoyin magance su.

4. Muhimmancin haɗin kai, haƙuri da juriya wajen bunƙasa al'umma.

Bayan gabatar da waɗannan shawarwari, an buɗe ƙofa ga mahalarta taron domin gabatar da ra'ayoyi da shawarwari, tare da bayyana cewa ƙofar Majalisar a buɗe take ga duk wanda yake da wata shawara mai amfani, ba sai lokacin taro kaɗai ba.

A ƙarshe, Majalisar Zartaswa ta Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah ta Jihar Katsina ta amince da bada umarnin gabatar da Al-Qunut a dukkan masallatan kungiyar da ke faɗin jihar Katsina.

An umarci cewa za a riƙa gabatar da Al-Qunut a dukkan sallolin farilla guda biyar, tare da yin addu'o'i na musamman kan halin rashin tsaro da sauran ƙalubalen da al'umma ke fuskanta. Haka kuma, za a ci gaba da yin irin waɗannan addu'o'i a ƙarshen huɗubobin Juma'a kamar yadda aka saba.

Taron ya gudana ƙarƙashin jagorancin Shugaban Kungiyar na Jihar Katsina, Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan Katsina (Sautus-Sunnah), tare da halartar dukkan masu riƙe da muƙaman kungiyar a matakin ƙasa da na jiha, shugabannin ƙananan hukumomi da sakatarorinsu, shugabannin Majalisar Malamai na ƙananan hukumomi da sakatarorinsu, shugabannin Majalisar Agaji na ƙananan hukumomi da sakatarorinsu, da kuma shugabannin Kwamitin Limamai na ƙananan hukumomi.

JIBWIS Katsina
13 Muharram, 1448
28 June, 2026

18/05/2026

Kwanaki Goma Na Farkon Dhul-Hajj

- Sheik Dr Gadon kaya

18/05/2026

Kwanaki Goma Na Farkon Dhul-Hajj

- Prof. Isa Ali Ibrahim Pantami, CON.

18/05/2026

Manzon Allah SAW yace:

Babu wasu kwanaki wadanda ayyukan alheri s**afi soyuwa a wajen Allah kamar wadannan ranaku goman.
Sahabbai s**a ce: Ya manzon Allah koda jihadi fisabilillah?

Yace: ko jihadi bai kaishi ba, sai dai mutumin da ya fita jihadin da kansa da dukiyarsa amma bai dawo da komai ba.

JIBWIS INGAWASAKAMAKON KADDAMAR DA LIMAMAI DA CHANJIN DA AKA SAMU1. Masallacin GRAMalam Sulaiman Yusuf Malam Adamu Danla...
06/04/2026

JIBWIS INGAWA
SAKAMAKON KADDAMAR DA LIMAMAI DA CHANJIN DA AKA SAMU

1. Masallacin GRA
Malam Sulaiman Yusuf
Malam Adamu Danladi

2. Masallacin Aliyu bin Abi Dalib
Malam Rabiu Ado Crc
Malam Kabir Nakano

3. Masallacin bakin Asibiti
Malam Adamu Gambo
Malam Yusuf Yahaya

4. Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na II
Malam Mansur Jibril

KUNGIYAR IZALA RESHEN KARAMAR HUKUMAR INGAWA NAMA AL'UMMA GAISUWAR LIMAN MALAM IBRAHIM U ABDULLAHI YAYAInnalillahi wainn...
04/04/2026

KUNGIYAR IZALA RESHEN KARAMAR HUKUMAR INGAWA NAMA AL'UMMA GAISUWAR LIMAN MALAM IBRAHIM U ABDULLAHI YAYA

Innalillahi wainnailaihi rajiun, cikin alhini Kungiya ke isar da Sakon gaisuwa ga alumma na rashin Babban malami Mai tawaliu da akayi jiya da yamma.

Kafin rasuwarsa shine
1. Limamin Masallacin GRA
2. Mataimakin Shugaban Majalisar na II
3. Mataimakin Shugaban kwamitin marayu

Malam ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya, ya rasu Yana furta kalmar shahada a bakinsa Kuma ranar Juma'a da yammaci

Malam ya kasance mai ilimi ga kyawawan dabiu, duk Wanda zai muamulance shi sai dai ya sanya Masa albarka, ko ranar rasuwar shi da asuba bayan ya gama jan Sallah yayi nasiha Kan zuwa Sallar Juma'a akan lokaci don sauraren hudubar

Allah yajikan Malam, yayi Masa sakamako da Jannatul Firdaus, ya albarkaci abinda ya Bari 🤲

29/03/2026

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

Assalamu Alaykum,
Ƙungiyar Jibwis Ingawa tana gayyatar dukkan al'umma zuwa wajen wa'azin goron Sallah wanda zai gudana kamar haka:
Rana: Yau Lahadi
Lokaci: Bayan Sallar Isha'i
Wuri: Masallacin Uthman bin Affan ( Sabon Masallacin Jumu'a)

Allah Ya bada ikon halarta, Amin 🤲🙏🙏


Jibwis Ingawa
Masallacin Abubakar Siddiq Ingawa
Buhari Isah Aisha Usama Bashir Idris Muhammad Sani Isah Abba S Jarmae Jamilu Ado Asmeey Beauty Abdurrahman Mustapha Usman Rabiu Ibrahim Sanusi Abba Garba

SITTU SHAWWALAzumin kwanaki 6 bayan RamadanAnnabi ﷺ ya ce:“Duk wanda ya azumci watan Ramadan, sannan ya bi shi da azumin...
24/03/2026

SITTU SHAWWAL
Azumin kwanaki 6 bayan Ramadan

Annabi ﷺ ya ce:
“Duk wanda ya azumci watan Ramadan, sannan ya bi shi da azumin kwanaki shida na Shawwal, kamar ya azumci shekara gaba ɗaya ne.”

Yadda ake yi:
👉Za ka iya yin su a jere
👉Za ka iya yin su a rarrabe
👉Za ka iya yin su farkon wata ko ƙarshen wata

Muhimmi: Kada ka bari watan Shawwal ya wuce ba tare da ka yi su ba.

Tunatarwa:
Abubakar Yahaya Ladan

23/03/2026

AN GAMA SALLAH SAI SITTU SHAWWAL
Annabi SAW yace duk Wanda ya azumci Ramadan Kuma ya biyo bayanshi da sitti shawwal kamar ya azumci shekarar ne

Allah yasa mu dace

21/03/2026

Big shout out to my new rising fans! Aminatu Usama, Sabitu Sanusi Ingawa, Abba Garba

Address

Round About Ingawa
Ingawa

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jibwis Ingawa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share