Jibwis lagos

Call Website Contact the place of worship

Jibwis lagos The Islamic Organization For Eradicating Innovations and Establishing Sunnah.

Taya MurnaMu taya Baban mu Sheikh Buhari Yaqubu murnan zama daga cikin national patron na Sunnah Media Professionals Of ...
28/09/2026

Taya Murna
Mu taya Baban mu Sheikh Buhari Yaqubu murnan zama daga cikin national patron na Sunnah Media Professionals Of Nigeria (SMPN) daga bagaran kudu maso yamman Nigeria. Lalle an daura kwarya a gurbin ta. Muna addu'a Allah ya taimaki malam ya daura shi a kan dede.

Jibwis Lagos.

📸 LABARIN HOTUNA:  Wa'azin Jiha da ya gudana yau Lahadi, 27 ga Satumba 2026, a Unguwar Amukoko, Ifelodun Local Governmen...
27/09/2026

📸 LABARIN HOTUNA:

Wa'azin Jiha da ya gudana yau Lahadi, 27 ga Satumba 2026, a Unguwar Amukoko, Ifelodun Local Government, Lagos State, ƙarƙashin jagorancin JIBWIS Lagos State.

Allah Ya saka wa dukkan mahalarta da alheri, Ya kuma karɓi ibadunmu. 🤲

✍️JIBWIS LAGOS

25/09/2026

Hudubar jumma'ah daga Babban Masallacin Juma’a na JIBWIS IJORA BADIA LAGOS STATE

WA’AZIN JIHA! WA'AZIN JIHA!! WA'AZIN JIHA!!! Wa'azin Jiha A Unguwar Amukoko Ifelodun Street Lagos State.Sheikh Sulaiman ...
24/09/2026

WA’AZIN JIHA! WA'AZIN JIHA!! WA'AZIN JIHA!!!

Wa'azin Jiha A Unguwar Amukoko Ifelodun Street Lagos State.

Sheikh Sulaiman Ibrahim Imam 1004, v/i
Shugaban Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah na (JIBWIS LAGOS)

Sheikh Muhammad Abubakar Argungu,
Shugaban Majalisar Malamai (JIBWIS LAGOS)

Alh Bala Muhammad,
Daraktan Yan Agaji (JIBWIS LAGOS)

A MADADIN KUNGIYAR JAMA’ATU IZALATIL BID’AH WA IKAMATIS SUNNAH NA JIHAR LAGOS,

Na gayyatar Alummar muslimai
Zuwa wa’azin Jiha

WANDA ZA'AYI KAMAR HAKA;

Ranar Lahadi /Date: 26 September 2026

Wuri/Venue: Odofin Street Amukoko Ifelodun local government Lagos state

Lokaci/Time: 10:00 na Safe zuwa 02:00 na Rana.

MALAMAI MASU WA'AZI;
Sheikh Imam sulaiman Ibrahim 1004.
Sheikh Abubakar Muhammad Argungu.
Sheikh Buhari Yakubu Agege.
Sheikh Ishaq Ayendiran.
Sheikh Siraj Sharafuddeen Adam Ijora Badia.
Sheikh Abdul Nasir mile12.
Sheikh Sadiq Abubakar Hausa line.
Sheikh Malam Ahmad Musa Agege.
Sheikh Imam Salis idi'araba.
Sheikh Abubakar Usman Taraba.
Malam Muddassir Abdulmumin.
Sheikh Malam Aliyu Mai Dubu Dubu.
Malam Kabiru Muazu Danbatta.
Malam Mala Muhammd.
M mustafha bello Gandi
ALARAMMOMI;
Alarammah Nura Safyan Agege
Alarammah Auwal Al Hassan Apapa
Alarammah Abubakar Ibrahim iddo Otto
Alarammah Amiru Muhammad Apapa
Alarammah Muhammad Ibrahim Sageer Ijora Badia
Alarammah Hafeez Aswad.

Da Sauran Malamai da Alarammomi

Allah Ya Bada Ikon Zuwa, Ameen.

✍️ JIBWIS LAGOS

Majalisar Agaji ta Jihar Lagos ta gudanar da wani muhimmin taro a ƙarƙashin jagorancin Daraktan Agaji na Jihar Lagos, Us...
20/09/2026

Majalisar Agaji ta Jihar Lagos ta gudanar da wani muhimmin taro a ƙarƙashin jagorancin Daraktan Agaji na Jihar Lagos, Ustaz Balah Muhammad.

An gudanar da taron ne a Babban Masallacin Juma’a na Sheikh Abubakar Gumi, da ke Okoko Maiko, Alaba Rago, Lagos State.

Taron ya samu halartar mambobin majalisar na jiha (State Members), shugabannin Divisional Leaders, da sauran masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar Lagos.

Haka kuma, taron ya samu halartar shugabannin farin kaya na unguwar, waɗanda s**a kasance cikin mahalarta taron.

Taron ya kasance wata muhimmiyar dama ta tattauna batutuwan da s**a shafi ayyukan Agaji, ƙarfafa haɗin kai tsakanin shugabanni da mambobi, tare da duba hanyoyin da za a inganta ayyukan majalisar a faɗin jihar Lagos.

Allah Ya sanya taron ya zama sanadin alheri da ci gaba ga al’umma. Amin.

✍️State Pub. Sec. And media team

🕌 GAGARUMIN MUHADARAA UNGUWAR GATAN KOWA, ALIMOSHO, LAGOS STATESHEIKH SIRAJ SHARAFUDINI ADAMSakataren Majalisar Malamai ...
18/09/2026

🕌 GAGARUMIN MUHADARA

A UNGUWAR GATAN KOWA, ALIMOSHO, LAGOS STATE

SHEIKH SIRAJ SHARAFUDINI ADAM
Sakataren Majalisar Malamai ta JIBWIS Lagos

MALAM KABIRU MUAZU DANBATTA

ZA SU GABATAR DA GAGARUMIN MUHADARA

A BABBAN MASALLACIN GATAN KOWA,
ALIMOSHO, LAGOS STATE

📅 RANA: LAHADI, 20 GA SATUMBA, 2026

🕰️ LOKACI: BAYAN SALLAR MAGRIBA,

Allah Ya bada ikon zuwa

Jibwis Lagos

🕌 RAHOTON TATTARA FATUN LAYYA NA JIBWIS NIGERIA – SHEKARAR 2026💰 JIBWIS Ta Tattara Kusan Naira Miliyan 190 Daga Fatun La...
17/09/2026

🕌 RAHOTON TATTARA FATUN LAYYA NA JIBWIS NIGERIA – SHEKARAR 2026

💰 JIBWIS Ta Tattara Kusan Naira Miliyan 190 Daga Fatun Layya

Shugaban Ƙungiyar JIBWIS ta Ƙasa, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, ya karɓi rahoton tattara kuɗaɗen fatun layya na shekarar 2026 daga Kwamitin Tattara Fatun Layya na Ƙasa.

Shugaban kwamitin, Malam Lamara Azare, tare da sauran mambobin kwamitin ne s**a miƙa rahoton a wani taro da aka gudanar a Kaduna.

Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau ya yaba wa kwamitin bisa jajircewa, gaskiya da riƙon amana da s**a nuna wajen gudanar da wannan aiki. Haka kuma ya yaba wa jihohin JIBWIS a faɗin ƙasar nan bisa gudummawar da s**a bayar, tare da addu’ar Allah Ya saka musu da mafificin alheri.

🏆 Jihohi 10 na farko a tattara fatun layya:

1️⃣ Kaduna — ₦25,866,300.00
2️⃣ Kebbi — ₦25,830,950.00
3️⃣ Sokoto — ₦19,412,490.00
4️⃣ Bauchi — ₦17,595,583.00
5️⃣ Niger — ₦12,110,500.00
6️⃣ Katsina — ₦10,957,850.00
7️⃣ Zamfara — ₦10,901,250.00
8️⃣ Adamawa — ₦9,186,400.00
9️⃣ Taraba — ₦8,431,400.00
🔟 Jigawa — ₦6,547,500.00

📊 Sauran Jihohi:

11. Kano — ₦6,385,850.00
12. Gombe — ₦5,838,700.00
13. Abuja (FCT) — ₦5,370,400.00
14. Nasarawa — ₦4,239,300.00
15. Lagos — ₦3,728,555.00
16. Kogi — ₦3,162,150.00
17. Borno — ₦2,890,900.00
18. Benue — ₦1,986,500.00
19. Yobe — ₦1,854,550.00
20. Kwara — ₦1,656,150.00
21. Plateau — ₦1,634,850.00
22. Oyo — ₦1,194,672.00
23. Ogun — ₦624,903.58
24. Osun — ₦486,272.00
25. Rivers — ₦385,500.00
26. Enugu — ₦380,000.00
27. Delta — ₦335,600.00
28. Ondo — ₦202,202.42
29. Edo — ₦145,500.00
30. Bayelsa — ₦135,000.00
31. Imo — ₦110,000.00
32. Akwa Ibom — ₦87,000.00
33. Anambra — ₦76,650.00
34. Ekiti — ₦69,495.00
35. Ebonyi — ₦67,200.00
36. Cross River — ₦50,300.00
37. Abia — ₦24,000.00

💰 JIMLAR KUƊAƊEN DA AKA TATTARA

📖 Kuɗin Fatun Layya: ₦179,771,140.00

🧾 Kuɗin Rasit: ₦10,191,283.00

✅ Jimla Gaba Ɗaya: ₦189,962,423.00

Allah Ta’ala Ya ce:

﴿ يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنْ تَنْصُرُوا اللَّهَ يَنْصُرْكُمْ وَيُثَبِّتْ أَقْدَامَكُمْ ﴾

"Ya ku waɗanda kuka yi imani! Idan kuka taimaki addinin Allah, Allah zai taimake ku kuma Ya tabbatar da dugaduganku." (Suratul Muhammad: 7)

Annabi ﷺ ya ce:

"Allah yana taimakon bawa matuƙar bawan yana taimakon ɗan’uwansa." (Sahih Muslim)

A ƙarshe, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau ya yi addu’ar Allah Ya saka wa dukkan masu bayar da gudummawa da mafificin alheri, Ya karɓi ibadun layya, Ya ƙara wa JIBWIS albarka da ci gaba.

🤲 Allah Ya saka da alheri.

🕌 Jibwis Nigeria

Innalillahi wa inna ilaihi raji,unAllah yayiwa mahaifin oga rabiu rasuwa jagora ne a social media na jahar lagos Muna ad...
13/09/2026

Innalillahi wa inna ilaihi raji,un

Allah yayiwa mahaifin oga rabiu rasuwa jagora ne a social media na jahar lagos

Muna adu'ar allah ya jikansa da rahama yasa aljannah ce makomarsa

✍️jibwis lagos

Labari cikin hotuna:HOTUNA: Wa'azin jiha kenan da ya gabata a Yau lahadi 13 Sep 2026 a unguwar Sabo Alabigba Ajegunle Ap...
13/09/2026

Labari cikin hotuna:

HOTUNA: Wa'azin jiha kenan da ya gabata a Yau lahadi 13 Sep 2026 a unguwar Sabo Alabigba Ajegunle Apapa Lagos State

Muna adu’ar Allah yayi jagora

✍️Jibwis Lagos

13/09/2026

Address

Ikeja
LAGOS

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jibwis lagos posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Place Of Worship

Send a message to Jibwis lagos:

Shortcuts

Share