02/03/2026
LITININ, 2 GA MARIS
NASSI: MAHUKUNTA 1:11–19
KAN MAGANA: ALLAH YANA MAYARWA MUGU DA MUGUNTA
MAHUKUNTA 1:11–19
11:Daga can s**a tafi su yaƙi Debir wadda a dā ake kira Kiriyat-Sefer.
12:Kalibu ya ce, “Duk wanda ya fāɗa wa Kiriyat-Sefer da yaƙi har ya ci ta, zan ba shi 'yata Aksa aure.”
13:Sai Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kalibu ya ci birnin da yaƙi, Kalibu kuwa ya ba shi 'yarsa Aksa aure.
14:Da ta zo wurinsa, ta iza shi ya roƙi mahaifinta saura. Da ta sauka daga kan jakinta, sai Kalibu ya ce mata, “Me k**e so?”
15:Sai ta amsa masa, “Ka yi mini alheri, da yake ka tura ni a ƙasar Negeb, ka ba ni maɓuɓɓugan ruwa.” Kalibu kuwa ya ba ta maɓuɓɓugan tuddai da na kwari.
16:Zuriyar Bakene, surukin Musa kuwa s**a fita tare da mutanen Yahuza daga birnin dabino, wato Yariko, s**a tafi jejin Yahuda da take a Negeb kudu da Arad. A can s**a zauna tare da Amalekawa.
17:Yahuza kuwa da ɗan'uwansa, Saminu, s**a tafi s**a bugi Kan'aniyawan da suke zaune a Zefat. S**a la'anta birnin, s**a hallaka shi, s**a sāke wa birnin suna Horma, wato hallakarwa.
18:Yahuza kuma ya ci Gaza da karkararta, da Ashkelon da karkararta, da Ekron da karkararta.
19:Ubangiji kuwa yana tare da Yahuza, ya mallaki ƙasar tuddai, amma bai iya korar waɗanda suke zaune a fili ba, domin suna da karusan ƙarfe.
ALLAH YANA MAYARWA MUGU DA MUGUNTA
Babu wani abu mai girma kamar samun yardar Allah tare da da kai.
Yahuda sun kai hari a yankunan da ke makwabtaka da su don samun damar zama. S**a kuma fadawa Kan’aniyawan da suke zaune a Negeb, da kasar tudu ta yamma, da Hebron.
A yau s**a cigaba da yakar Kan’aniyawan da suke Debir. Kalibu ya yi alkawari cewa Isra’ilawa za su ci birnin. Kan’aniyawan da suke zaune a Zafat su ma an ci su, aka hallaka su. Gaza, Ashkelon da Ekron ma an karbe su.
Ka lura cewa duk wadannan nasarorin an same su ne domin Ubangiji yana tare da su. Duk da haka, ba a cika aikin gabadaya ba domin Yahuda ta dauke hankali ga Allah Jehovah don ta ga karusan karfe da mazaunan suke da su, wadanda daga baya sun zama barazana ga Isra’ilawa.
TAMBAYA:
Wacce dama ce Allah ya ba ka da ba ka da cikakkiyar bangaskiya mallaka?
ADDU’A:
Uba, ka motsa ni in san cewa kasancewarka a cikina ya ba ni duk nasarorin da nake bukata a yau. Amin.
ABINCIN YINI - 2026