Masjidu Khulafa'ir Rashideen

Masjidu Khulafa'ir Rashideen ADAM BN ABUBAKAR FOUNDATION

_๐Ÿ’•NEMAN ILIMI.๐Ÿ’•_-"A rayuwa kada muyi wasa da neman ilmi musamman ma dai ilmin addinin musulunci"-"Duk wanda ya mayar da ...
14/02/2024

_๐Ÿ’•NEMAN ILIMI.๐Ÿ’•_
-
"A rayuwa kada muyi wasa da neman ilmi musamman ma dai ilmin addinin musulunci"
-
"Duk wanda ya mayar da hankali wajen neman ilmin addini, to haฦ™iฦ™a kusancinsa da Allah yana ฦ™ara ฦ™aimi ne, kuma zai taฦ™aita saษ“awa Allah cikin jahilci"
-
Manzon Allah ๏ทบ, ya ce: "Duk wanda yabi wata hanya yana me neman ilmi a cikinta, dominsa Allah zai sauฦ™aฦ™a masa hanyar shiga aljannah" Sahih Muslim (2699)
-

Duk Cikin Halittar AllahBabu Mutum Mai Kima Da DarajarโœจManzon Allah๏ทบ๐Ÿค๐Ÿฆ‹
25/01/2024

Duk Cikin Halittar Allah

Babu Mutum Mai Kima Da DarajarโœจManzon Allah๏ทบ๐Ÿค๐Ÿฆ‹

12/01/2024

Mafi girman ฦ™alubale da ke gabanka, shi ne rashin sanin Addini.
~Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum

21/12/2023

YADDA MUSULMI ZAI YI TA'AMULI DA BUKIN KIRSIMETI:

โœ… Rubutawar:
Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
Maimaici

Da yake a Nigeria ana zaman cakuda ne tsakanin al'ummar Kirista da al'ummar Musulmi. Sannan da yake shi Musulunci addini ne da ya bayyanar da hukuncin dukkan wani lamari da ya shafi rayuwar dan Adam, ko dai ta hanyar nassi, ko ta hanyar zahiri, ko ta hanyar ishaarah da iimaai. Sannan da yake akwai karkatattu da dama da suke halatta abin da Shari'ah ba ta halatta ba, ko haramta abin da Shari'ah ba ta haramta ba, lalle ya dace a yi wa al'ummar Musulmi bayanin hukuncin abin da ya shafi wannan Idi na Kirsimeti ta bangarorinsa da ke iya shafar wasu al'ummar Musulmi.

To amma kafin mu shiga bayanin wadannan hukunce-hukunce ya kamata Musulmi su san abubuwa kamar haka:-
1. Shi dai bukin kirsimeti wata bidi'ah ce da bata da Kiristoci s**a kirkira sannan s**a maida ita wata ibada da ake samun lada ta hanyar yin ta kamar dai yadda wasu Musulmi s**a kirkiri bidi'ar idin Maulidi, Kiristoci sun kirkiri wannan bidi'ar ce kuwa a shekarar Miladiyyah ta 360, watau a cikin karni na hudu bayan haifuwar Annabi Isa alaihis salam.

2. Ya kamata kowa ya san cewa ba ya halatta Musulmi ya yi tarayya da wadanda ba musulmi ba cikin bukukuwansu na idi, watau ta hanyar halartan wasu tarurruka da za su kira, ko ta hanyar ba su wani taimako domin karfafa idodin nasu, wannan dai shi ne hanyar Salafus Salih: Sahabbai, da Taabi'ai, da Taabi'uttaabi'in; dalili kuwa shi ne:-
Imamul Baihaqiy ya ruwaito cikin As-Sunanul Kubraa hadithi na 19,334 cewa Sayyidina Umar Dan Khattab Allah Ya kara masa yarda ya ce: ((ุงุฌุชู†ุจูˆุง ุงุนุฏุงุก ุงู„ู„ู‡ ููŠ ุนูŠุฏู‡ู…)). Ma'ana: ((Ku nisanci makiya Allah cikin idinsu)).
Sannan Shaikhul Islam Ibnu Tamiyyah ya ce -kamar yadda ya zo cikin Al-Mustadrak Alaa Fataawaa Ibnu Tamiyyah 1/108, da Mukhtasarul Fataawaa Misriyyah1/517 :-
((ูˆู„ูŠุณ ู„ู„ู…ุณู„ู…ูŠู† ุงู† ูŠุนูŠู†ูˆู‡ู… ุนู„ู‰ ุฃุนูŠุงุฏู‡ู… ู„ุง ุจุจูŠุน ู…ุง ูŠุณุชุนูŠู†ูˆู† ุจู‡ ุนู„ู‰ ุนูŠุฏู‡ู… ูˆู„ุง ุจุงุฌุงุฑุฉ ุฏูˆุงุจู‡ู… ู„ูŠุฑูƒุจูˆู‡ุง ููŠ ุนูŠุฏู‡ู… ู„ุงู† ุฃุนูŠุงุฏู‡ู… ู…ู…ุง ุญุฑู…ู‡ ุงู„ู„ู‡ ุชุนุงู„ู‰ ูˆุฑุณูˆู„ู‡ ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู… ู„ู…ุง ููŠู‡ุง ู…ู† ุงู„ูƒูุฑ ูˆุงู„ูุณูˆู‚ ูˆุงู„ุนุตูŠุงู†)). ุงู†ุชู‡ู‰.
Ma'ana: ((Musulmi ba su da damar su taimaka musu cikin idodinsu, ko dai ta hanyar sayar musu da abin da za su karfafu da shi, ko ta hanyar ba da hayar dabbobinsu domin su hau su cikin idinsu, saboda idodinsu na daga cikin abin da Allah Madaukakin Sarki da kuma manzonSa mai tsira da amincin Allah s**a haramta, saboda abin da yake cikinsu na kafirci da fasikanci da kuma sabo)).

3. Babu wani wanda ya isa ya bugi kirji a duniyan nan ya ce: ga tabbatacciyar wata da rana da aka haifi Annabi Isa alaihis salam a cikinta, sai dai kowa ya fadi abin da yake zato kawai, wannan shi ya sa ma Kiristoci masu yin bukin ranar Kirsimeti watau ranar haifuwar Annabi Isa alaihis salam s**a yi sabani dangane da ranar da za a yi wannan bukin zuwa mazhabobi biyu:-

Mazhabar farko: Za a yi bukin Kirsimeti ne a ran 25 ga watan December, wannan ita ce mazhabar da Catholic, da Protestant, da kuma mafi yawan bangarorin Kiristoci ke bi.

Mazhaba ta biyu: Za a yi bukin Kirsimeti ne a ran 7 ga watan January, wannan ita ce mazhabar da bangarorin Orthodox ke bi.

4. Kiristoci kafurai ne kamar yadda Yahudawa da Majusawa da sauran masu bautar gumaka suke kafurai, babu sabani cikin wannan mas'ala cikin shari'ar Musulunci.

5. Ya kamata a san cewa akwai wasu kafuran da Musulunci ya kebanta su da wasu hukunce-hukunce saboda tabbatar wa Musulmi wata maslaha, wadannan kuwa su ne: Yahudawa da Kiristoci, su wannan nau'i na kafurai Musulunci ya halatta wa Musulmi cin yankansu, da auren matansu, sabanin mabiya addinin majusu, ko mabiya addinin Hindu, ko mabiya addinin Budha, ko mabiya sauran addinai na bautan gumaka.
Idan masu karatu sun fahimci wannan to sai mu shiga bayanin mas'alarmu da muke son yi wa jama'a bayaninta.

HUKUNCIN KARBAN KYAUTUTTUKAN KAFURAI A RANAR IDINSU:

Su kyaututtukan da kafurai -Ahlul kitabi ko wasun Ahlul kitabi- ke ba wa Musulmi a ranakun idinsu na kafurci da bidi'ah sun kasu kashi biyu ne:-

1. Kyaututtukan da suke ba nama ba ne da ake bukatar yankawa, watau kamar irinsu: halawa, da tufafi, da kayan marmari da sauransu.

2. Kyaututtukan da suke nama ne da ke bukatar a yi masa yanka irin ta Shari'ah.

To shi na farkon, watau kyaututtukan da suke ba nama ba ne da ke bukatar yanka irin ta Shari'ah, babu sabani tsakanin Salafus Salih -a dai iya saninmu- cikin halaccin karbarsu, saboda dalilai kamar haka:-

1- Imamul Baihaqii ya ruwaito athari na 18,644 daga Muhammad Dan Siiriin cewa:-
((ุฃุชูŠ ุนู„ูŠ ุฑุถูŠ ุงู„ู„ู‡ ุจู‡ุฏูŠุฉ ุงู„ู†ูŠุฑูˆุฒุŒ ูู‚ุงู„: ู…ุง ู‡ุฐู‡ุŸ ู‚ุงู„ูˆุง: ูŠุง ุงู…ูŠุฑ ุงู„ู…ุคู…ู†ูŠู† ู‡ุฐุง ูŠูˆู… ุงู„ู†ูŠุฑูˆุฒ. ู‚ุงู„: ูุงุตู†ุนูˆุง ูƒู„ ูŠูˆู… ููŠุฑูˆุฒ)) .
Ma'ana: ((An zo wa Sayyidina Aliyyu Dan Abii Taa'lib Allah Ya kara masa yarda da kyautar (idin) Nairuuz, sai ya ce: mene ne wannan? Sai s**a ce: Ya Amirar Muu'miniin! Wannan ranar Nairuuz ce. Sai ya ce: (in haka abin yake) ku rika yin Fairuuz a ko wace rana)).

2- Imam Ibnu Abii Shaibah ya ruwaito cikin Musannaf athari na 24,371, da Imam Ishaq Ibnu Raa'huyyah cikin Musnad athari na 1,606 daga Qaa'bus Dan Zibyaan daga shi mahaifin nasa cewa wata mace ta tambayi Nana A'isha Allah Ya kara mata yarda ta ce:-
((ุงู† ู„ู†ุง ุงูƒุงุฑุง ู…ู† ุงู„ู…ุฌูˆุณ ูˆุงู†ู‡ ูŠูƒูˆู† ู„ู‡ู… ุงู„ุนูŠุฏ ููŠู‡ุฏูˆู† ู„ู†ุงุŒ ูู‚ุงู„ุช: ุงู…ุง ู…ุง ุฐุจุญ ู„ุฐู„ูƒ ุงู„ูŠูˆู… ูู„ุง ุชุฃูƒู„ูˆุง ูˆู„ูƒู† ูƒู„ูˆุง ู…ู† ุฃุดุฌุงุฑู‡ู…))
Ma'ana: ((Muna da 'yan kodago daga cikin Majusawa, sannan kuma suna da ranar idin da suke aika mana da kyaututtuka. Sai ta ce: Amma abin da aka yanka saboda wannan ranar to kada ku ci, to amma ku ci daga 'ya'yan itatuwansu)).

3- Imam Ibnu Abii Shaibah ya ruwaito a cikin Musannaf athari na 24,372 daga Abuu Barzah cewa:-
((ูƒุงู† ู„ู‡ ุณูƒุงู† ู…ุฌูˆุณ ููƒุงู†ูˆุง ูŠู‡ุฏูˆู† ู„ู‡ ููŠ ุงู„ู†ูŠุฑูˆุฒ ูˆุงู„ู…ู‡ุฑุฌุงู† ููƒุงู† ูŠู‚ูˆู„ ู„ุฃู‡ู„ู‡: ู…ุง ูƒุงู† ู…ู† ูุงูƒู‡ุฉ ููƒู„ูˆุง ูˆู…ุง ูƒุงู† ู…ู† ุบูŠุฑ ุฐู„ูƒ ูุฑุฏูˆู‡)).
Ma'ana: ((Yana da wasu mazauna Majusawa, kuma sun kasance suna aika masa da kyautuka a lokacin Nairuuz da Mihrajan, sannan ya kasance yana gaya wa iyalansa cewa: Kyautar da ta kasance ta kayan marmari ne to ku ci, wacce kuma ta kasance ba hakan ba, to ku mayar da ita)).

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya yi taliki a kan wadannan hujjojin a cikin littafinsa mai suna Iqtidhaa'us Siraa'til Mustaqiim 2/554-555 ya ce:-
((ูู‡ุฐุง ูŠุฏู„ ุนู„ู‰ ุงู†ู‡ ู„ุง ุชุฃุซูŠุฑ ู„ู„ุนูŠุฏ ููŠ ุงู„ู…ู†ุน ู…ู† ู‚ุจูˆู„ ู‡ุฏูŠุชู‡ู…ุŒ ุจู„ ุญูƒู…ู‡ุง ููŠ ุงู„ุนูŠุฏ ูˆุบูŠุฑู‡ ุณูˆุงุกุ› ู„ุงู†ู‡ ู„ูŠุณ ููŠ ุฐู„ูƒ ุฅุนุงู†ุฉ ู„ู‡ู… ุนู„ู‰ ุดุนุงุฆุฑ ูƒูุฑู‡ู…)).
Ma'ana: ((Wannan duka yana nuni ne a kan cewa: Idi ba yi da wani tasiri a kan hana karban kyautarsu, a'a hukuncin karban kyautarsu ba yi da wani bambanci tsakanin lokacin Idi da kuma lokacin da ba na Idi ba, saboda babu wani abu na taimakon addininsu a cikin karban kyautarsu)).

TALIKI:
Da wannan ne za mu fahimci cewa: Maluman Musulunci sun hana cin yankan da Majusawa s**a yi domin bukukuwan idinsu, to amma fa ba wai sun hana cin yankan ba ne saboda kasancewarsa yankan da aka yi domin bukin idin kafurai ba, a'a an hana cin yankan ne saboda kasancewarsa yankan Majusawan da ba sa cikin mutanen nan ne da ake kira Yahudawa ko ake kira Kiristoci, dukkan kuma kafurin da ba ya cikin abin da ake kira Yahudawa ko ake kira Kiristoci to ba a cin yankansa.

HUKUNCIN CIN NAMAN DABBAR DA YAHUDAWA KO KIRISTOCI S**A YANKA DA HANNAYENSU SABODA YIN BUKUKUWAN IDINSU:

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya yi bayani game da cin abin da Yahudawa ko Kiristoci s**a yanka saboda bukukuwan idinsu, a cikin littafinsa mai suna Iqtidhaa'us Siraa'til Mustaqim 2/555,558 ya ce:-
((ูˆุงู†ู…ุง ูŠุฌูˆุฒ ุงู† ูŠุคูƒู„ ู…ู† ุทุนุงู… ุงู‡ู„ ุงู„ูƒุชุงุจ ููŠ ุนูŠุฏู‡ู… ุจุงุจุชูŠุงุน ุงูˆ ู‡ุฏูŠุฉ ุงูˆ ุบูŠุฑ ุฐู„ูƒ ู…ู…ุง ู„ู… ูŠุฐุจุญูˆู‡ ู„ู„ุนูŠุฏ. ูุฃู…ุง ุฐุจุญ ุงู„ู…ุฌูˆุณ ูุงู„ุญูƒู… ููŠู‡ุง ู…ุนู„ูˆู… ูุฅู†ู‡ุง ุญุฑุงู… ุนู†ุฏ ุงู„ุนุงู…ุฉ. ูˆุฃู…ุง ู…ุง ุฐุจุญู‡ ุงู‡ู„ ุงู„ูƒุชุงุจ ู„ุงุนูŠุงุฏู‡ู… ูˆู…ุง ูŠุชู‚ุฑุจูˆู† ุจุฐุจุญู‡ ุงู„ู‰ ุบูŠุฑ ุงู„ู„ู‡ ู†ุธูŠุฑ ู…ุง ูŠุฐุจุญ ุงู„ู…ุณู„ู…ูˆู† ู…ู† ู‡ุฏุงูŠุงู‡ู… ูˆุถุญุงูŠุงู‡ู… ู…ุชู‚ุฑุจูŠู† ุจู‡ุง ุงู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุชุนุงู„ู‰ุŒ ูˆุฐู„ูƒ ู…ุซู„ ู…ุง ูŠุฐุจุญูˆู† ู„ู„ู…ุณูŠุญ ูˆุงู„ุฒู‡ุฑุฉุŒ ูุนู† ุงุญู…ุฏ ุฑูˆุงูŠุชุงู†: ุงุดู‡ุฑู‡ู…ุง ููŠ ู†ุตูˆุตู‡: ุงู†ู‡ ู„ุง ูŠุจุงุญ ุงูƒู„ู‡ ูˆุงู† ู„ู… ูŠุณู… ุบูŠุฑ ุงู„ู„ู‡ ุชุนุงู„ู‰. ูˆู†ู‚ู„ ุงู„ู†ู‡ูŠ ุนู† ุฐู„ูƒ ุนู† ุนุงุฆุดุฉ ูˆุนุจุฏ ุงู„ู„ู‡ ุจู† ุนู…ุฑ.....ูˆุงู„ุฑูˆุงูŠุฉ ุงู„ุซุงู†ูŠุฉ ุงู† ุฐู„ูƒ ู…ูƒุฑูˆู‡ ุบูŠุฑ ู…ุญุฑู…))ุงู†ุชู‡ู‰
Ma'ana: (Cin abincin Ahlul Kitabi a lokacin idinsu ga abin da dama ba su yanka shi saboda Idi ba, yana halatta ne ta hanyar saye da kudi, ko kuwa kyauta, ko wanin haka. Amma abin da Majusawa s**a yanka hukuncinsa sananne ne, watau haramun ne a wurin dukkan malamai, to amma abin da Ahlul Kitabi s**a yanka saboda idinsu, da kuma abin da suke yin ibada ta hanyar yanka shi ga wanin Allah' kamar abin da suke yankawa saboda Almasihu, da Zahrah, irin dai abin da Musulmi suke yankawa na Hadaya, da Layya, domin neman kusantar Allah da shi, to, Imam Ahmad yana da fatawowi biyu game da hakan, fatawar farko wacce ita ce ta fi shahara: Wannan ba ya halatta a ci shi koda kuwa ba a ambaci sunan wanin Allah a kansa ba. An nakalto hana cin wannan yankan ma daga Nana A'isha, da Abdullahi Dan Umar.. Fatawa ta biyu ita ce: Cin wannan yankan makruuhi ne ba haramun ba. Wannan ita ce mazhabar Malikiyyah, Imam Malik ya kyamaci cin abin da Ahlul Kitabi s**a yanka saboda Coci-Cocinsu, ko saboda idinsu amma ba tare da ya haramta hakan ba)).

Sannan har yanzu Sahikhul Islam Ibnu Taimiyyah ya ce a cikin Iqtidhaa'us Siraa'til Mustaqim 2/559 :-
((ูˆู†ู‚ู„ุช ุงู„ุฑุฎุตุฉ ููŠ ุฐุจุงุฆุญ ุงู„ุฃุนูŠุงุฏ ูˆู†ุญูˆู‡ุง ุนู† ุทุงุฆูุฉ ู…ู† ุงู„ุตุญุงุจุฉ ุฑุถูŠ ุงู„ู„ู‡ ุนู†ู‡ู…ุŒ ูˆู‡ุฐุง ููŠู…ุง ุงุฐุง ู„ู… ูŠุณู…ูˆุง ุบูŠุฑ ุงู„ู„ู‡ุŒ ูุงู† ุณู…ูˆุง ุบูŠุฑ ุงู„ู„ู‡ ููŠ ุนูŠุฏู‡ู… ุงูˆ ุบูŠุฑ ุนูŠุฏู‡ู… ุญุฑู… ููŠ ุงุดู‡ุฑ ุงู„ุฑูˆุงูŠุชูŠู†ุŒ ูˆู‡ูˆ ู…ุฐู‡ุจ ุงู„ุฌู…ู‡ูˆุฑุŒ ูˆู‡ูˆ ู…ุฐู‡ุจ ุงู„ูู‚ู‡ุงุก ุงู„ุซู„ุงุซุฉ ููŠู…ุง ู†ู‚ู„ู‡ ุบูŠุฑ ูˆุงุญุฏุŒ ูˆู‡ูˆ ู‚ูˆู„ ุนู„ูŠ ุจู† ุงุจูŠ ุทุงู„ุจ ูˆุบูŠุฑู‡ ู…ู† ุงู„ุตุญุงุจุฉุŒ ูˆู‡ูˆ ู‚ูˆู„ ุงูƒุซุฑ ูู‚ู‡ุงุก ุงู„ุดุงู… ูˆุบูŠุฑู‡ู…. ูˆุงู„ุซุงู†ูŠุฉ: ู„ุง ูŠุญุฑู… ูˆุงู† ุณู…ูˆุง ุบูŠุฑ ุงู„ู„ู‡ุŒ ูˆู‡ุฐุง ู‚ูˆู„ ุนุทุงุก ูˆู…ุฌุงู‡ุฏ ูˆู…ูƒุญูˆู„ ูˆุงู„ุงูˆุฒุงุนูŠ ูˆุงู„ู„ูŠุซ)).
Ma'ana: ((An ciro yin sauki a kan cin yanke-yanken idodin (Yahudawa da Kiristoci) da makamantansu (su yanke-yanken) daga wani sashi na Sahabbai Allah Ya kara musu yarda amma fa wannan sai idan ba su ambaci wanin Allah a lokacin yankan ba, in kuma har sun ambaci wanin Allah a lokacin yankan to cin sa ya haramta a cikin fatawa mafi shahara daga cikin fatawowi biyu da Imam Ahmada yake da su a cikin mas'alar, wannan kuwa shi ne mazhabar jumhur, kuma shi ne mazhabar Fuqaha'un nan guda uku, kamar yadda mutane da yawa s**a ruwaito, kuma shi ne maganar Aliyyu Dan zabii Taa'lib da waninsa a cikin Sahabbai, daga cikinsu ma akwai Abud Dardaa, da Abu Umamah, da Irbadh Dan Saa'riyah, da Ubaa'dah Dan Saa'mit, kuma shi ne maganar maluman Sham da wasunsu. Fatawar Imam Ahmad ta biyu ita ce: Cin wannan yankan ba haramun ba ne koda kuwa sun ambaci sunan wanin Allah a lokacin yankan, wannan kuwa shi ne maganar Ataa'u, da Mujaa'hid, da Makhuul, da Auzaa'ii, da kuma Laith)).

Taliki na farko:-
Za mu fahimta daga maganganun malaman da s**a gabata cewa: Abin da Yahudawa da Kiristoci suke yankawa saboda bukukuwan idinsu yana kasuwa ne zuwa kashi biyu:-

Na farko: Abin da s**a ambaci sunan Allah yayin yanka shi.
Na biyu: Abin da s**a ambaci sunan wanin Allah yayin yanka shi.

To ita dabbar da aka ambaci sunan Allah lokacin yanka ta, Malamai sun kasu kashi biyu game da hukuncin cin ta.

Mazhabar farko: Sahabbai da yawa sun ba da damar cin wannan nama. Maluman Malikiyyah, da Imam Ahmad cikin ruwayah sun halattar da cinsa amma tare da nuna kyama.

Mazhaba ta biyu: Nana A'isha, da Abdullahi Dan Umar, da kuma Maluman Hanaa'bilah sun ce cin wannan nama haramun ne.

Sannan ita kuma dabbar da aka ambaci sunan wanin Allah lokacin yanka ta, watau kamar wacce aka ambaci sunan Yesu Almasihu lokacin yanka ta, wannan ma Malamai sun kasu kashi biyu game da hukuncin cin wannan dabbar:-

Mazhabar farko: Cin wannan dabba bai halatta ba, wannan shi ne abin da Aliyyu Dan Abii Taa'lib, da Abud Dardaa'i, da Abuu Umamah, da Irbadh Da Saa'riyah, da Ubaa'dah Dan Saa'mit, da Hanafiyyah, da Malikiyyah, da Shafi'iyyah, da Hanaa'bilah, da mafi yawan maluman kasar Sham, suk fada.

mazhaba ta biyu: Cin wannan dabba halal ne, wannan shi ne abin da Ataa'u, da Mhjaa'hid, da Makhul, da Auzaa'ii, da Laithu Dan Sa'ad, da kuma Imam Ahmad cikin ruwaya s**a fada.

Taliki na biyu:-
Za mu iya fahimta daga maganganun da s**a gabata cewa: Naman kasuwa da Musulmi ke yankawa da hannayensu idan Kiristoci s**a saya s**a dafa a matsayin abincin Kirsimeti, to wannan abincin halal yake ga dukkan wanda s**a ba da shi gare shi. Wallahu A'alam.

HUKUNCIN CIN YANKAN KIRISTOCI DA YAHUDAWA A MAZHABAR MALIKIYYAH:
A karshen wannan makala tamu za mu yi bayanin mene ne mash'hurin mazhabar Malikiyyah game cin yankan Kiristoci da Yahudawa, saboda Musulmin wannan kasa tamu Nigeria su kara fahimtar irin banbancin da yake tsakanin abin da ke rubuce cikin littattafan Mazhabar Malkiyyah, da kuma abin da wasu jahilan 'yan bidi'ah da suke ikirarin cewa su masu bin Mazhabar Malikiyyah ne, alhali kuwa hayaniyarsu kawai suke yi, son zuciyarsu ne kawai suke bi, duk abin da jahilan shaihunansu s**a ce to shi ne addini a wurinsu. Allah ya tsare mu da sharrin Shaidan.
Babban malamin Malikyyah Imamul Qurtubii ya ce cikin littafinsa Aljaami'u Li Ahkaamil Qur'an 6/53:-
((ูˆู‚ุงู„ ุฌู…ู‡ูˆุฑ ุงู„ุงู…ุฉ ุงู† ุฐุจูŠุญุฉ ูƒู„ ู†ุตุฑุงู†ูŠ ุญู„ุงู„ ุณูˆุงุก ู…ู† ุจู†ูŠ ุชุบู„ุจ ุงูˆ ุบูŠุฑู‡ู…ุŒ ูˆูƒุฐู„ูƒ ุงู„ูŠู‡ูˆุฏ)).
Ma'ana: ((Jumhuurin Al'ummah sun ce: Lalle yankan ko wane kirista halal ne, babu banbanci daga kabilar Taglib ne ko daga wasunsu, haka nan su ma Yahudawa)). Intaha.
Khalil Dan Ishaq ya ce cikin Mukhtasar Khalil shafi na 90
((ูˆุงู† ุณุงู…ุฑูŠุง ุงูˆ ู…ุฌูˆุณูŠุง ุชู†ุตุฑ ูˆุฐุจุญ ู„ู†ูุณู‡ ู…ุณุชุญู„ู‡ุŒ ูˆุงู† ุงูƒู„ ุงู„ู…ูŠุชุฉ ุงู† ู„ู… ูŠุบุจ))
Ma'an: ((koda ya kasance wani basaamire ne, ko bamajuse ne da yazama kirista ya yanka abin da yake halal a gare shi saboda kuma kan shi, koda kuwa yana halatta cin mushe ne, matukar dai musulmi na sane da cewa shi din ne ya yi yankan)).
Sannan ya zo cikin littafin As'halul Madaarik 2/92:-
((ูŠุฌูˆุฒ ู„ู„ู…ุณู„ู… ู†ูƒุงุญ ุญุฑุงุฆุฑ ุงู‡ู„ ุงู„ูƒุชุงุจ .. ูˆูƒุงู† ุงู„ุตุญุงุจุฉ ุจุชุฒูˆุฌูˆู† ู…ู† ุงู„ูŠู‡ูˆุฏ ูˆุงู„ู†ุตุงุฑู‰ ูƒุซูŠุฑุง ุฒู…ู† ุงู„ูุชุญ .. ูˆู†ูƒุญ ุนุซู…ุงู† ู†ุตุฑุงู†ูŠุฉุŒ ูˆู†ูƒุญ ุทู„ุญุฉ ูŠู‡ูˆุฏูŠุฉ)).
Ma'ana: ((yana halatta ga musulmi auren 'yantattun matan Ahlul Kitaabi.. Sahabbai sun kasance da yawa suna auren matan Yahudawa da Kiristoci a lokacin da ake cin kasashe da yaki.. Sayyidina Uthman ya auri wata kirista, Sayyidina Talhah ya auri wata bayahudiya)). Allah muke roko da Ya taimake mu. Ameen.

Sallar Walaha (Salatud Dhuhaa) Manzon Allah (S.A.W) yace "Sallar mutanen kirki".   ~ Idan kana so ka gwada kanka shin ka...
14/12/2023

Sallar Walaha (Salatud Dhuhaa) Manzon Allah (S.A.W) yace "Sallar mutanen kirki".
~ Idan kana so ka gwada kanka shin ka bin Sahun mutanen kirki musamman wajen neman Lada ta hanyar Nafilfili toh ka gwada kanka wajen yin Sallar Walaha ko rashin yin ta. Bari kaji wani abu, ita Sallar Walaha takan budewa mutum 'kofar Rahama, Arziki (Kudi) da warkewar rashin lafiya ne.

Idan kana so ka gane ta a harshen zamani toh sai ince ko ka san Morning ๐ŸŒ… Exercise? (Morning jogging)? da safe zaka ga wasu mutane musamman masu Kudi ko masu Kiba s**an fita da sassafe suje suyi gudu, su jijjige jikin su, su dawo suyi wanka.
~ Dadin da suke ji tun daga safe har dare daban ne da ranar da ba suyi wannan jogging din ba. Kwakwalwar takan bude, Basira da fikira a wannan ranar daban ce.

Toh Sallar Walaha ta zarce wannan morning jogging din, (spiritually), amma fa duk da haka ba ina s**an Morning jogging bane, domin yana da amfani ga lafiyar mutum, kada a fahimci bayanin a juye.
~ Sallar Walaha kamar muce itace (spiritual morning jogging) alkhairin da zata jawo maka a wannan ranar ba kadan bane, wadanda s**a saba yi zaka basa dainawa, saboda sun san me suke samu sun san me suke ji a jikin su duk rana. Zaka ga ko ana sanyi sai sunyi, ko ana zafi ko Damina sai sun fita morning jogging, toh haka Sallar Walaha a wajen mutanen kirki.

Lamarin zai fi burgewa zai fi bayar da kala ace kana Morning jogging kuma kana yin Sallar Walaha, haske bisa haske kenan.
~ A Arewacin Nigeria anyi kuskuren bayanin Sallar Walaha ada, cewa wai Sallar Tsofi ne, kuma idan an fara ba'a dainawa, wannan ba daga karatun Annabi Muhammadu bane, gaskiya.

~ Hukuncin ta, Sunnah ce me karfi:

Idan ka samu dama kayi, idan baka samu ba babu laifi, maganar da ake cewa wai idan ka fara yin Sallar Walaha ba'a dainawa wannan ba gaskiya bane, ba Hadisin Annabi bane.

~ Saboda muhimmancin ta har a ranar Fatahu Makkah sai da Manzon Allah ya shiga wani Gida da sauri da gaggawa yaje yayi Sallar ya fito, wata Baiwar Allah ta shinfida masa Sallaya yayi Walaha.

Nana Aisha (R.A) tace:
Manzon Allah yakan yi Sallar Walaha Raka'a hudu, kuma yakan 'kara fiye da haka ma.
Karanta Sahihu Muslim, Hadisi na 1,176.

Ya halatta kayi ta raka'oi 2, ko 4, ko 6, amma ba'a wuce Raka'oi 8.

A yanzu (December 2023) musamman a nan yankin North Eastern Nigeria, muna fara yin ta daga karfe 7:30 na safe (a yadda nake fahimta) har zuwa karfe 11:30 na safe ko ma sama da haka kafin 12:00 Noon.

Yanayin lokutan s**an sha banban daga waje zuwa waje, sai ka lura da yankin da kake, ko wajen da k**e, Allah yasa mu dace....
Babu wadanda s**a fi ganin tasirin wannan Sallar kamar matasa, yam mata, da masu karancin shekaru idan suna yi, daga 'yan shekaru 55 zuwa kasa.

~ Kada ka gafala 'dan uwa, sabgogin rayuwar nan suna da yawa, kuma ana cikin su tsamo tsamo ake wuce zuwa cikin Qabari.

Karanta Sahihul Bukhariy, Hadisi na 1,178.

Karanta Sahihu Muslim, Hadisi na 748.

Sunanut Tirmiziy, Hadisi na 437, Sheikh Muhammad Nasir Al-baniy yace Hadisin Sahihi ne.

Allah ya karba mana yasa mudace....

Address

Kumbiya Kumbiya Quarter's, Shehun Burema Street Gombe
Gombe

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Masjidu Khulafa'ir Rashideen posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share